TAMBAYOYI AKAN MANZANNI
SU WAYE ANNABAWA DA MANZANNI?
SU MUTANE NE DAGA CIKIN’YAN ADAM, ALLAH YA SAUKAR MUSU DA ANNABCI KUMA YA UMURCE SU DA ISAR DA SAKO GA MUTANENSU, KUMA YA KIRA SU ZUWA GA BAUTAR ALLAH SHI KADAI, NA FARKONSU SHI NE ANNABI ADAM – AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI – KUMA NA KARSHEN SU SHI NE ANNABI MUHAMMAD ((S.A.W)) – KUMA SUNA DA YAWA. DOMIN ALLAH YA AIKE SU ZUWA GA DUKKAN AL’UMMAR DUNIYA DA SUKE RAYE A KANTA, KAMAR YADDA A KOWANE MATAKI NA TARIHI AKWAI WANI ANNABI DAKE KIRAN MUTANENSA YANA SHIRYAR DA SU HANYAR SHIRIYA.
ME YASA ALLAH YA AIKO MANZANNI?
ALLAH YA AIKO MANZANNI; RAHAMA GA MUTANE DA SHIRIYA A GARE SU DA ISAR DA SAKON UBANGIJINSU ZUWA GARE SU, DOMIN MANZO MUTUM NE WANDA MUTANENSA SUKA SAN SHI KWARAI DA GASKE SUKA KUMA YI MASA SHAIDA NA ALHERI KAFIN A SAUKAR DA WAHAYI ZUWA GARE SHI, KUMA ALLAH YA SANYA MANZANNI SU ZAMA ABIN MISALI GA MUTANE, YANA KARANTAR DA SU HALAYE DA DABI`U, SUNA BAYYANA MUSU ABIN DA ZAI AMFANE SU KUMA NISANTAR DA SU DAGA ABIN DA ZAI CUTAR DA SU, DON HAKA AIKO MANZANNIN DON SU KAFA HUJJA GA HALITTU SUNA HADA MUTANE AKAN ADDINI DAYA, WANDA SHI NE BAUTAR ALLAH SHI KADAI, DON HAKA MUTANE SUNA BUKATAR MASU SHIRYARWA DA ZA SU SHIRYAR DA SU ZUWA GA HANYA MADAIDAICIYA DA KUMA YARENSU, SABODA HAKA; ALLAH YA SAUKAR DA LITTATTAFAI GA WADANNAN MANZANNI DA YAREN MUTANENSU, DON A ISAR DA SAKON A FILI.
SHIN ANNABAWA MA’ASUMAI NE?
ANNABAWA BANGARE NE NA MUTANE, KUMA SUNA DA DUKKAN WASU MA’ANONI NA MUTANE. ALLAH NE YA KARE SU GAME DA ABINDA YAKE DA ALAKA DA SAKON DA YA BASU, KUMA YA KARE SU DAGA ABINDA ZAI YI BATANCI CIKIN HALAYENSU KO KYAWAWAN DABI’UNSU, DON SU ZAMA KYAKKYAWAN MISALI GA MUTANE SU KUMA GAMSU DA MAGANGANUNSU DA AYYUKANSU, KUMA DON KADA A SAMI HANYAR SHIGAR ƁATANCI CIKIN ISAR SAƘONSU, AMMA – DUK DA WANNAN – SUMA MUTANE NE WAƊANDA SUKAN IYA FAƊAWA CIKIN KUSKURE NA AL’ADA HAKAN BA ZAI CUTAR DA SAKONSU BA, KAMAR SU: KUSKUREN KIMANTA WURI MAFI DACEWA GA AIKIN GONA KO YAKE-YAKE, KO KIMANTA GURIN DA YA KE KWADAYIN DA`AWA.
WANENE ANNABI MUHAMMAD, AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI?
SHI NE KARSHEN ANNABAWA DA ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA AIKO WA BAYINSA, KUMA SUNANSA SHI NE: MUHAMMAD BIN ABDULLAH BIN ABDUL MUTTALIB AL-HASHEMI AL-QURASHI, AN HAIFE SHI NE A MAKKA RANAR LITININ A CIKIN WATAN RABI ‘AL-AWWAL A SHEKARAR GIWA, MAHAIFINSA YA RASU ALHALIN YANA CIKIN MAHAIFIYARSA, MAHAIFIYARSA KUMA TA RASU YANA DA SHEKARA SHIDA, SAI KAKANSA ABDULMUDDAIB YACI GABA DA RAINONSA SHI MA YA RASU SHEKARUN MANZO – TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI TAKWAS SANNAN BAFFANSA ABU TALIB YA DAUKI NAUYINSA, ANA CE MASA MAI GASKIYA DA AMANA. YA KASANCE MAI KYAWAWAN HALAYE – TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI -, AN AIKO SHI YANA DA SHEKARU ARBA’IN, KUMA YA TASHI YANA KIRAN MUTANENSA A MAKKA TSAWON SHEKARU GOMA SHA UKU ZUWA GA MUSULUNCI, SANNAN LOKACIN DA CUTARWARSU TA TSANANTA SOSAI. YA YI KAURA ZUWA MADINA YA ZAUNA A CAN NA TSAWON SHEKARU GOMA, YA KULLA YAN`UWANTAKA TSAKANIN MASU HIJIRA DA MUTANEN MADINA, KUMA YA KAFA DOKA DA HUKUNCIN ALLAH, KUMA YA RASU A SHEKARA TA GOMA SHA DAYA TA HIJIRA BAYAN YA ISAR DA SAKO KUMA YA SAUKE AMANA.
MENENE HUJJAR TSARKIN GASKIYAR MANZON ALLAH – TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI?
HUJJOJIN ANNABCIN ANNABI MUHAMMADU – SALATIN ALLAH DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI – SUNA DA YAWA, MAFI MAHIMMANCI DAGA CIKINSU SHI NE ALKUR’ANI MAI GIRMA. WANNAN LITTAFIN MAI BAN AL’AJABI YANA CI GABA DA BA MUTANE MAMAKI DAGA TSARA ZUWA TSARA DA TASKARSA DA LU’LU’UNSA WADANDA KE BIRGE HANKALIN MUTANE. DAGA CIKIN HUJJOJIN GASKIYARSA ITA CE: TARIHIN RAYUWARSA DA KYAWAWAN HALAYENSA WADANDA ABOKAN GABANSA SUKA BAYYANA KAFIN MASOYANSA, DON HAKA AKE KIRANSA DA AL-AMIN MAI GASKIYA, KUMA DAGA CIKIN ALAMUN TGASKIYARSA: IT ACE SHARI`AR MUSULUNCI WACCE TAKE CIKE DA KAMALA DA KYAU, KUMA DAGA CIKIN ALAMUN GASKIYARSA: BUSHARAR DA LITATTAFAN DA SUKA GABATA SUKA FITAR, KUMA DAGA CIKIN HUJJOJI – MA -: WANNAN CI GABA DA YADUWAR ADDININ MUSULUNCI A KOWANE LOKACI DA WURI, KUMA DAGA CIKIN ALAMUN GASKIYARSA: BADA LABARI GAME DA AL’UMMOMIN DA SUKA GABATA DA AL’AMURAN DA KE ZUWA.
TA YAYA MANZON ALLAH – TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI – YA HAU ZUWA SAMA A CIKIN DARE GUDA?
AN TAFI DA ANNABI – TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI – CIKIN DARE AKAN BURAKA HAR ZUWA KUDUS, SANNAN YA HAU SAMA TARE DA JIBRILU – AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI -, KUMA ALLAH MADAUKAKIN SARKI YANA DA IKON YIN KOMAI BA ABINDA KE GAGARARSA A DUNIYA KO A CIKIN SAMA, KUMA KAMAR YADDA MUKE GANI A YAU: TA YAYA NE MUTUM MAI RAUNI YA IYA A CIKIN TUNANINSA YA ƘIRƘIRI JIRGIN SAMA WANDA YA ZARCE SAURIN SAUTI, KUMA YA ƘIRƘIRA KAYAN WATSA HOTO MASU ƁANGARORI UKU, WANDA KE SANYA MUTUM YA ZAMA A SAMA DA WURI GUDA A LOKACI GUDA; ALLAH SHI NE MAFI GIRMA, DA DAUKAKA, KUMA MAFI GIRMAN IKO SAMA DA HALITTARSA.
ME YASA ANNABI MUHAMMADU ((S.A.W)) YA ZAMA KARSHEN ANNABAWA?
HAKIKA LAMARIN AIKO MANZANNI YANA DA NASABA DA HIKIMA – WACCE ITA CE SHIRIYA DA NUNI – KUMA TUNDA LITTATTAFAN DA SUKA GABATA SUN FUSKANCI RAGI, KUMA AN JIRKITA SU BAYAN MUTUWAR MANZANNI; HIKIMAR ALLAH TA BUKACI YA AIKO MANZO DA LITTAFI WANDA BA ZAI FUSKANCI WANNAN RAGIN BA. MAIMAKON HAKA, ALLAH YA TABBATAR DA CEWA ZAI KIYAYE SHI HAR ZUWA TASHIN KIYAMA, KUMA TUNDA NA DAGA CIKIN MU’UJIZAR ALKUR’ANI.-CEWA LITTAFI NE BAYYANANNE KUMA HUJJA CE WACCE TA TABBATA TA KUMA TSAYA AKAN DUKKAN HALITTA. YANA DAGA CIKIN HANKALI CEWA MANZO – TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI – SHI NE KARSHEN ANNABAWA DA MANZANNI.
ME YA SA YA WAJABTA MU KAUNACI MANZON – TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI?
SABODA SOYAYYAR ANNABI – ((S.A.W))- TANA DAGA CIKIN SHIKA-SHIKAN IMANI, A MAIMAKON HAKA, IMANI DA ALLAH MADAUKAKIN SARKI BA YA CIKA SAI DA WANNAN KAUNA, KUMA AN HADA KAUNAR ANNABI – ((S.A.W)). TARE DA KAUNAR ALLAH MADAUKAKIN SARKI, KUMA SABODA ALLAH MAI GIRMA DA DAUKAKA YA ZABE SHI DAGA CIKIN MUTANE DON ISAR DA WANNAN SAKON MAI GIRMA, ALLAH YA ZABI MAFI KYAWUN MUTANE TA HANYAR NASABA, DABI’U, MAGANA DA AIKI. DOMIN ALLAH MADAUKAKI YA FI KOWA SANIN WANDA YA BA AMANAR SAKONSA, TO MUDDIN ALLAH YA ZABE SHI CIKIN DUKKAN MUTANE DON WANNAN BABBAN AIKI. HAKKINMU NE MU ZABE SHI A MATSAYIN MASOYI SAMA DA DUKKAN MUTANE. DOMIN SHI NE WANDA YA SANAR DA MUTANE UBANGIJINSU, KUMA SHI NE MAFI ALHERIN MANZO DAGA CIKIN AL’UMMARSA, KUMA MAFI RAHAMAR ANNABI GA AL`UMARSA, DOMIN BABU WANI MAI BAIWA BAYAN ALLAH GA MUTANE SAMA DA SHI – TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI – KUMA SHI ANNABI- AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI – YA JURE CUTARWA DOMIN KIRAN MUTANE ZUWA GA ADDINI DA KYAUTATAWA, HAR KIRJINSA ((S.A.W)) YANA YIN KUNCI, IDAN WANI BAI YI IMANI BA IDAN YA KIRA SHI ZUWA GA ADDININ ALLAH SABODA TAUSAYI A GARE SU NA SHIGA WUTA, ALLAH MADAUKAKI YA CE: (KANA NEMAN KA HALAKA KANKA A BAYANSU IDAN BA SU YI IMANI DA WANNAN ALKUR`ANIN BA SADODA BAKIN CIKI) (AL-KAHF: 6), SABODA WANNAN DALILI. ANNABI – TSIRA DA AMINCI SU TABBATA A GARE SHI – YA KASANCE MUTUMIN DA YA FI CANCANTA DA ƘAUNARMU BAYAN ALLAH.