TARBIYYAR IMANI GA YARO DAGA
DAGA CIKIN MAUDU`AI MASU MUHIMMANCI A FANNIN TARBIYYA SHI NE TARBIYYAR DASA IMANI A ZUCIYAR YARO DOMIN TANA SANYA DABI`U NAGARI TA KUMA TABBATAR DA SU, TA KUMA DASA INGANTACCIYAR AKIDA A CIKIN TUNANI DA ZUCIYAR YARO. YA KUMA NUSASSHE DA YARO ZUWA DA HALAYYA TAGARI DA AIKATA WANNAN HALAYYAR A DUKKAN AYYUKAN SHI. ACIKIN WANNAN MATAKIN SHEKARUN, YARO ZAI GINA HANGEN SHI GA YANAYIN YADDA DUNIYA KE TAFIYA, DAGA FAHIMTAR HAKA NE ZAI SAN YADDA ZAI GINA DABI`UN SHI DA MU`AMALAR SHI DA MUTANE, DAGA CIMMA WANNAN MANUFAR NE ZAI SAMU JIN DADIN DUNIYA YA KUMA TSIRA A LAHIRAR SHI, WANNAN NAUYIN NA ABUBUWAN DA AKA AMBATA YANA KAN IYAYE NE, TUN TARBIYYAR SHI NA KARKASHINSU NE, SU ZASU DORA SHI KAN HANYA DA ZAI CIMMA WANNAN MANUFAR HAR YA ZAMA MUTUM NAGARI. ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA CE: {ALLAH YANA YI MUKU WASIYYA GAME DA `YA`YANKU} [ANNISA: 11]. MANZON ALLAH ((S.A.W)) YA BAYYANA HAKAN INDA YACE: (( BABU WANI YARO FACE AN HAIFE SHI AKAN TURBA SAI DAI IYAYEN SHI SU YAHUDANTAR DA SHI KO SU NASARANTAR DA SHI KO SU MAJUSANTAR DA SHI.)) [BUKHARY: 1359]. HADISIN YANA NUNI AKAN AL`AMURA MASU YAWA, DAGA CIKIN SU:
- IMANI FIDRA CE TA MUTUM KUMA WANDA YA CANZA MAI SHI YA CANZA MISHI SABODA MATSALA DAGA CIKIN MATSALOLIN `YAN ADAM.
- HADISIN YA BAYYANA NAUYIN DAKE KAN IYAYE DA KUMA MATSAYINSU MAI GIRMA ACIKIN TARBIYYA.
- YA YI NUNI IZUWA TASIRIN INDA MUTUM KE RAYUWA ACIKIN TARBIYYA.
DAGA CIKIN FALALAR ALLAH AKAN MUTUM SHI NE TSARKAKE ZUCIYAR SHI TUN FARKON RAYUWAR SHI GA IMANI BA TARE DA BUKATAR WATA HUJJA DA DALILI BA, MA`ANA TUN KAFIN YA SAN CIWON KAN SHI. DA WANNAN SAI MU CE IYAYE YA KAMATA SU TSAYU AKAN KARIYA TA HANYAR DASA MAI AKIDA INGANTACCIYA DA GASKIYAR TSAYUWA, SU KUMA TSARKAKE TURBAR DA TUN ASALI AKANTA KOWA YAKE, SU TARBIYYANTAR DA `YA`YANSU AKAN INGANTACCEN ADDINI DA ALKUR`ANI DA SUNNAH SUKA ZO DA SHI. KUMA KADA SUYI KASALA WAJEN TARBIYYANTAR DA WAJEN DA SUKE ZAUNE WANDA FAHIMTAR YARO KE DOGARO DA IRIN FAHIMTAR YANAYIN WAJEN.
TSARKAKAKKIYAR ZUCIYAR YARO ITA CE ZINARIYAR DA BABU KOWANE IRIN ZANE DA HOTO A KANTA, KUMA TA DACE DA KOWANE IRIN ZANE, DOMIN SABAWA DA ALHERI DA SANINSA YA GIRMA AKANSHI KUMA YAYI FARIN CIKI DUNIYA DA LAHIRA, IYAYENSA DA MALAMANSA KUMA SU YI TARAYYAR LADAN KOWANE MALAMI DA LADABI TARE DA SHI A CIKIN LADANSA, KUMA SABAWA DA SHARRI DA WATSI DA GAFALA IRIN TA DABBOBI YA HALAKA SU, KUMA NAUYIN YA KASANCE A WUYAN MAI KULA DA LAMARINSA; DOMIN GYARA MAFI KYAU NA KASANCEWA NE TUN MUTUM NA ƘARAMI, AMMA IDAN AKA BAR YARON, AKA SANGARCE, CI GABA A HAKA, GYARA SHI NA DA WUYA.
YARON DA YA GIRMA A CIKIN DANGI MASU IMANI MAI ƘARFI YANA HIMMATUWA DA KOYARWAR MUSULUNCI DAIDAI, YANA KUMA YIN KOYI DA IYAYENSA A CIKIN KOMAI, KUMA YANA SAMAR DA NASA RA’AYOYIN TA MAHANGAR IYAYENSA, DON HAKA MUKE GANIN WAƊANDA SUKE GABATAR DA KA’IDOJIN SHARI’A CIKIN TSANANTAWA DA TSATTSAURAN YANAYI WANDA KE HAIFAR DA MUMMUNAN SAKAMAKO GA YARA, KAMAR YADDA YARO IDAN YA GIRMA YA SAMI IYAYENSA BA SU DA KOYARWAR MUSULUNCI; YANA DA WAHALA A GARE SHI YA SAMI SHA’AWAR ADDINI A NAN GABA. DOMIN LOKACIN DA YAKE KARAMI BAI GA ALAMAR ADDINI BA, DON HAKA BAI DA WATA FAHIMTA GAME DA ADDINI.
BUNKASA
ADDINI GA YARO
ADDINI YANA FARAWA NE AWAJEN YARO DA TUNANI GUDA DAYA, SHI NE TUNANIN SAMUWAR ALLAH, DAGA NAN SAI WASU TUNANUKA TA WANI GEFEN SU FARA BAYYANAR MAI KAMAR TUNANIN HALITTA DA LAHIRA DA MALA’IKA DA SHAIDANU. KUMA ANA BANBANCE TUNANIN BUNKASAR ADDININ YARO A ABUBUWA GUDA HUDU:
- ABINDA KE FARUWA:
- ANAN FAHIMTAR YARO GAME DA ADDINI ZATA KARKATA NE GA ABINDA KE FARUWA YAKE KUMA IYA GANI KO TABAWA, YANA KARA GIRMA TUNANIN SHI NA KARUWA KADAN-KADAN HAR YA KAI GA GANO GASKIYA, YA SANYA TA A INDA YAKE GANIN TA DACE A LOKACIN DA YA KAI SHEKARUN BALAGA.
- SURANTAWA:
- ANAN YARO ZAI RINKA KWAIKWAYON YADDA MANYA KE IBADUNSU DA ADDU’O’INSU BABTARE DA YA SAN MA’ANARSU KO YA SAN GIRMANSU A ZUCIYA BA, SHIYA SA YA KAMATA GA MAI TARBIYYA YA SAN ABINDA YARO YAFI KARKATA AKAN SHI AWANNAN SHEKARUN NA YARINTA DAN YA KOYAR DA SHI RUKUNAN MUSULUNCI DA DABI’UN SHI DA RUKANAN IMANI DA TASIRIN SHI GA MUTUM.
- AMFANI.
- YARO ZAI FAHIMCI FARIN-CIKIN IYAYEN SHI DA MALAMAN SHI DA WADANDA KE KEWAYE DA SHI SABODA ABINDA YAKE AIKATAWA NA WASU IBADU, SAI YA RINGA AIKATA HAKAN DAN SAMUN SOYAYYARSU DA KUMA CIMMA MANUFAR WASU DAGA CIKIN ABUBUWAN AMFANUWAR SHI KO DAN TUNKUDE WATA CUTARWA DA KA IYA SAMUN SHI.
- TSATTSAURAN RA’AYI: HAKAN NA KASANCEWA NE A LOKACIN DA YARO YA ZAMA MAI TSATTSAURAN RA`AYI GAME DA ADDININSA YANA MAI SHA’AWAR HAKAN TA HANYAR JINGINUWA GA ADDININ DA KUMA JINGINUWA ZUWA GA ALLAH – MADAUKAKI.
DAGA ABINDA YA GABATA ZAMU FAHIMCI MUHIMMANCIN MAI DA HANKALI AKAN TARBIYYAR DASA IMANI, DA KUMA CEWA WAJIBI NE AKAN IYAYE DA MASU TARBIYYA SU MAI DA HANKALI WAJEN KUSANTO DA IMANI A ZUCIYAR YARO MUSAMMAN MA A WANNAN ZAMANIN DA FITINTINU SUKA YI YAWA DA JUYA ABUBUWA DA SHAGALA DA SAUYE-SAUYE. DAGA CIKIN AL’AMURA DA YA KAMATA ACE SUN AIKATA SU SUNE:
1- TABBATAR DA FIDIRA A ZUCIYAR YARO WANDA SHI NE KOYA MA YARO KALMAR TAUHIDI.
2- TABBATAR DA IMANI TA HANYAR SANAR DA SU RUKUNAN IMANI GUDA SHIDA, WANDA HAKAN ZAI TAIMAKAWA WAJEN SON ALLAH MADAUKAKIN SARKI DA SON MANZON ALLAH ((S.A.W)) DA KOYAR DA ALKUR’ANI.
SAMUWAR FIDIRA TA ADDINI DA TAKE BOYE A ZUKATA NA DAGA CIKIN ABIN DA KE TAIMAKAWA IYAYE WAJEN TSAYUWA AKAN ABINDA YA KAMACE SU A TARBIYYA, FIDIRA TANA NUNI ZUWA GA SHA’AWA TA ADDINI. KUMA ITA WANNAN SHA’AWAR KAMAR IRIN SAURAN SHA’AWOWI NE DA BA ZA’A IYA CANZA SU BA, SAI DAI CI GABA DA FADAKARWA DA SAMUN CI GABA AKAN HAKAN. KUMA ANA IYA AMFANI DA WANNAN FIDIRAR TA FUSKOKI DABAN-DABAN BANDA FUSKAR DA AKA HALICCI MUTUM ASALI DOMIN TA. SHI KO ADDININ MUSULUNCI YANA KIRA NE ZUWA GA DORA MUTUM AKAN FIDIRAR DA AKA HALICCE SHI SABODA ITA.
DAGA CIKIN MUHIMMAN ABUBUWAN DA YA KAMATA A RAINI DAN MUSULMI AKAN SU NE RUKUNAN MUSULUNCI GUDA SHIDA, KUMA MAFI MUHIMMANCI ACIKINSU DA YA KAMATA A KARANTAR DA SHI SHI NE IMANI DA ALLAH, IMANI DA ALLAH DA SON ALLAH SHI NE ZAI SA YAYI SAURIN FAHIMTAR SAURAN RUKUNAN IDAN YA ZO KANSU. ALLAH ((S.W.T)) YA SANYA SOYAYYAR SHI YA ZAMA MAFI GIRMAN SHARUDDAN IMANI DA KUMA KANKAN DA KAI GA ALLAH. MA’ANA SON SHI WAJIBI NE WAJEN YI MAI BIYAYYA DA KUMA ADAWA DA MAKIYAN SHI, WATO SAI KA SO SHI KAFIN KA YI MAI BIYAYYA KUMA KAKI MAKIYAN SHI. KUMA YA WAJABTAR DA WANNAN SON NA SHI YA ZAMA YAFI NA KOWA ACIKIN DUNIYA. ALLAH MADAUKAKIN SARKI YANA CEWA: { KA CE IDAN UBANNIN KU DA ‘YA’YAN KU DA ‘YAN`UWANKU DA MATAN KU DA DANGIN KU DA DUKIYOYI, WADANDA KUKA YI TSIWIRWIRIN SU DA FATAUCI WANDA KUKE TSORON TASGARONSA DA GIDAJE WADANDA KUKE YARDA DA SU , SUN KASANCE MAFIYA SOYUWA AGARE KU DAGA ALLAH DA MANZON SA , DA YIN JIHADI GA HANYAR SA, TO, KUYI JIRA HAR ALLAH YA ZO DA UMURNIN SA. KUMA ALLAH BA YA SHIRYAR DA MUTANE FASIKAI.} [TAUBAH: 24]. KUMA SAI YA SANYA SIFFAN FARKO TA BAYIN DA YA YARDA DA SU TA ZAMA SON SHI. YA CE: {YA KU WADANDA SUKA YI IMANI, WANDA YAYI RIDDA DAGA CIKIN KU DAGA ADDININ SA TO, ALLAH ZAI ZO DA WASU MUTANE, YANA SON SU KUMA SUMA SUNA SON SHI, MASU TAWALU’I AKAN MUMINAI MASU IZZA AKAN KAFIRAI, SUNA YIN JIHADI ACIKIN HANYAR ALLAH KUMA BA SA TSORON ZARGIN WANI MAI ZARGI, WACCAN FALALAR ALLAH CE, YANA BAYAR DA ITA GA WANDA YAKE SO, KUMA ALLAH MAYALWACI NE MAI ILIMI.} [MA’IDAH: 54]. YA KUMA BAYYANA CEWA TSARKAKAKKEN TAUHIDI BAYA KASANCEWA FACE SAI DA KADAITA ALLAH DA TSANTSAR SOYAYYA YA CE: {DAGA CIKIN MUTANE AKWAI WADANDA SUKA RIKE WANIN ALLAH KISHIYA SUNA SON SHI KAMAR YADDA SUKE SON ALLAH, WADANDA SUKA YI IMANI SUNA TSANANIN SON ALLAH} [AL-BAKARAT: 165]. KUMA IBADAR DA ALLAH YA HALICCE MU DOMIN TA ITA CE MAFI GIRMA A MATAKAN SOYAYYA, ASALIN TAUHEEDI SHI NE TSARKAKE SOYAYYA GA ALLAH SHI KADAI, SHI NE ASALIN KADAITAWA, SHI NE MA HAKIKANIN BAUTA, KUMA TAUHIDI BAYA CIKA HAR SAI SON BAWA GA UBANGIJINSA YA CIKA KUMA YAFI DUKKAN WANI ABU DA YAKE SO YA KUMA RINJAYE SHI. SAI YA KASANCE DA SHI ZA A YI HUKUNCI, TA YADDA SAURAN ABUBUWA DA YAKE SO DUK SUNA BAYAN SON DA YAKE MA ALLAH NE WANDA SHI NE JIN DADIN MUTUM DA KUMA TSIRAN SHI A LAHIRA.
KUMA WANNAN SOYAYYAR DA AKA GINA TA AKAN IMANI NA DAGA CIKIN MANYAN HANYOYIN KARFAFA DABI’UN YARA DA TABBATAR DA SU AKAN ADDININ MUSULUNCI DA KUMA BIYAYYA GA ALLAH DA MANZON SHI ((S.A.W)), DUK WANDA AKA DASA SON ALLAH DA MANZON SA ACIKIN ZUCIYAR SHI HAKIKA YAFI KASANCEWA TSAYAYYE A AKIDAR SHI DA IBADAR SHI DA DABI’UN SHI, KUMA DUK YADDA ZA A JUYAR DA WASU MAS’ALALOLI KO WANI YANKI NA ADDINI KO GAFALA TA ZO MISHI KO MANTUWA, SOYAYAYYAR NAN DAKE CIKIN ZUCIYAR SHI TA ALLAH DA MANZON SHI SAI SUN DAWO DA SHI KAN HANYAR DAIDAI DA YARDAR ALLAH TA’ALA, SABODA AKWAI SOYAYYA TA CIKI, BA WAI TA WAJE KADAI BA.
MAHANGAR DA AKIDAR MUSULUNCI TAKE BAYARWA GA RAYUWA TAYI FICE KASANCEWARTA TA DACE DA ASALIN HALITTAR DAN ADAM DA KUMA YADDA DABI’AR SHI TAKE, KUMA TANA TAFIYA KAFADA DA KAFADA DA LAFIYAYYEN HANKALI KUMA BABU CIN KARO A TSAKANINSU, KAMAR YADDA TAYI FICE DA WASU ABUBUWA KYAWAWA WADANDA BA A SAMUN SU A WATA AKIDA DOMIN KUWA TSARI NA TUNANI DA NA AKIDA DA NAGARTA DA SHARI’A SUN CIKA ACIKIN TA, IDAN KA KALLE TA ZAKA GA CEWA TSARI NE NA TUNANI DA AKIDA ZATA BAKA FASSARAR ASALIN SAMUWAR HALITTU DA MAKOMARSU DA HAKIKANIN ABUBUWAN DA KE CIKIN SU DA ABINDA ZA SU ZO BAYA, WATO BAYAN MUTUWA, TO, AKIDAR MUSULUNCI ITA KE BAKA AINIHIN BAYANI CIKAKKE DA HANKALI ZAI DAUKA KUMA TUNANI ZAI DAUKA BA TARE DA AN SAMU CIN KARO BA, SABANIN SAURAN AKIDU, KUMA TANA BAYYANA FARKON RAYUWAR MUTUM DA KARSHEN SHI, SANNAN YANA IYAKANCE FA’IDAR ABINDA YA SA AKA HALICCI MUTUM SABODA SHI, DA KUMA FA’IDA WACCA TASA AKA HALICCI MUTUM DAN A CIMMA MANUFAR TA, SHIYASA AMSA TAMBAYOYIN MUTUM AKAN RAYUWA WACCA BABU MAKAWA DOLE SAI MUTUM YAYI TAMBAYA AKAN SU SABODA YANAYIN DABI’A TA HANKALI WANDA IN MUTUM BE SAMU AMSAR SU GAMSASSU BA BA ZAI SAMU NATSUWA BA, IN KO BA HAKA BA ZAI RAYU NE CIKIN RUDANI DA DAMUWA AKODA YAUSHE SABODA BAI SAN MEYE MA’ANAR RAYUWAR DA YAKE ACIKI BA.
FA’IDAR
TARBIYYAR IMANI
AKWAI TARIN FA’IDAJI WADANDA MAI TARBIYYA ZAI IYA TATTARA SU AKAN TARBIYYAR IMANI. DAGA CIKINSU AKWAI:
- GAGGAWA WAJEN AIKATA ALKHAIRAI, YA DUBA DUK WATA KAFA TA AIKI DA ZATA KUSANTAR DA SHI ZUWA GA YARDAR ALLAH DA KUMA RAHAMAR SHI.
- KARFAFA DUK WANI ABU DA ZAI HANA SHI AIKATA MUMMUNAN ABU, INGANTACCEN IMANI SHI KE DAIDAITA DABI’UN MUTUM.
- GUDUN DUNIYA, KADA ZUCIYAR SHI TA ZAMA TA DANFARU DA SON DUNIYA HAR YA ZAMA SHI DAI KULLUN BURIN SHI YA ZAI SAMU DUNIYA.
- DACEWA DA ABINDA ALLAH KE SO, ALLAH SUBHANAHU WA TA’ALA ZAI RINKA JIBINTAR LAMARIN BAWAN SHI MUMINI, TA YANDA ZAI JANYO MAI MASLAHA DA KUMA JIN DADIN DUNIYA DA LAHIRA.
- KWADAITARWA ZUWA GA ALLAH, DUK SANDA IMANI YA KARU, TO BAWA ZAI KARA YARDA DA UBANGIJIN SHI DA KWADAITA ZUWA GARE SHI DA JUYA BAYA GA BARIN HALITTAR SHI.
- BOYE ABUBUWA DA SUKE MARASA KYAU DA KUMA RAGE MATSALOLI TSAKANIN MUTANE, ADUK LOKACIN DA IMANI YA KARU A ZUCIYA, TASIRIN SON ZUCIYA ZAI RAGU AKAN TA, TA KAI MUTUM ZUWA GA DABI’U NAGARI MADAUKAKA.
- TASIRI NA KWARAI A ZUKATAN MUTANE; MUMININ KWARAI NA KOKARIN GYARA KANSA NE DA KUMA WADANDA KE KEWAYE DA SHI.
- JIN NUTSUWA DA KWANCIYAR HANKALI; GWARGWADON YADDA WANNAN IMANI YA TABBATA A ZUCIYAR BAWA, GWARGWADON YADDA TSORON DA KE FIRGITA MUTANE ZAI GUSHE DAGA GARE SHI.
BATUTUWAN
TARBIYYAR IMANI
ABINDA YAKE WAJIBI AKAN IYAYE SHI NE SU KOYA MA ‘YA’YAN SU ABINDA ZAI KARFAFA IMANINSU, KUMA YA KYAUTATA DABI’UNSU, KUMA YA KARFAFA MISHI JIN JINGINUWA ZUWA GA AL’UMMAR ANNABI MUHAMMAD ((S.A.W)). DAGA CIKIN ABINDA KE KARKASHIN HAKA SHINE:
- KOYAR DA RUKANAN IMANI GUDA SHIDA, IMANI A DUNKULE WANDA YA DACE DA SHARI’AH DA DABI’AR MUTUM, TARE DA NISANTAR AIKATA ABU A AIKACE AGABAN YARO WANDA ZAI SA YA RASA IMANI, DA KOKARIN AIKATA AIKIN DA ZAI FARKAR DA ZUKATA YA SAITA KWAKWALWA YA KUMA INGANTA DABI’U.
- TARBIYYANTAR DA YARA AKAN SON MANZON ALLAH ((S.A.W)) DA SON IYALANSA DA MATAN SHI DA SAHABBAN SHI BAKI DAYA BA TARE DA WUCE GONA DA IRI.
- KOYAR DA YARA GIRMAMA ADDINI DA ABUWAN DA YA SHAR’ANTA DA KUMA TSORATAR DA SU AKAN YIN IZGILANCI DA SHI DA RASHIN DAMUWA DA SHI.
- KARANTAR DA SU CEWA CIKAKKEN IMANI BAYA KASANCEWA SAI DA AYYUKA NAGARI DA KUMA CEWA IMANI YANA KARUWA DA AIYUKA NAGARI KUMA YANA RAGUWA SANADIN AIKATA ZUNUBAI. TARBIYYAR DASA INGANTACCEN IMANI DOLE CE, HAR DADIN TA YA ZO ACIKIN DABI’U NAGARI DA IBADA.
- TABBATAR DA IMANI DA RANAR ALKIYAMA A ZUKATAN SU DA GIRMAN RANAR, DA KUMA SAKAMAKO MAI KYAU KO MARA KYAU DA BAWA ZAI SAMU TA DALILIN AIYUKAN SHI A DUNIYA, WANDA YA KYAUTATA YA SAMU ALJANNAH, WANDA KUMA YA MUNANA YA SHIGA WUTA.
- TABBATAR DA CEWA SUNA KIYAYE ALLAH ACIKIN IDADUNSU, SU SAN CEWA YANA GANIN SU YANA KUMA JIN SU, KUMA BA ABINDA KE BOYUWA AGARE SHI, YANA GANIN KOMAI DA KOWA. YA SAN KOMAI DA KOWA.
- ZURFAFA MAI JIN CEWA YANA KAN GASKIYA, WANNAN ZAI SA YA RIKE ADDININ SHI DA KARFIN GASKE.
HANYOYIN DASA
TARBIYYAR IMANI
ZAMU IYA KASA WADANNAN HANYOYIN ZUWA GIDA BIYU:
1- SHEKARUN KAFIN WAYO GA YARO.
2- SHEKARUN BAYAN WAYO GA YARO.
DAGA CIKIN ABUBUWANDA SUKE TAIMAKAWA WAJAN KARFAFA IMANI KAFIN SHEKARUN FAHIMTA:
- YIN BAYANI AKAN SUNAYE NA BAUTA DA YA SABA JIN SU KAMAR: ABDULLAHI, ABDUR-RAHMAN, ABDUL-KARIM, DA KOKARIN BAYYANA DUKKAN MA’ANONIN SU (SUNAYEN) A DUNKULE, DA BADA MUHIMMANCI WAJEN JIYAR DA SHI KIRAN SALLAH, DA KOYAR DA SHI ZIKIRAN YAU DA KULLUM, DA ADDU’O’I DA KIYAYE SU DA AMBATONSU A GABAN SHI, DA TUNATAR DA SHI NI’IMOMIN ALLAH A GARE SHI, MUSAMMAN LOKACIN CIN ABINCI; DA MAIMAITA SHI DA KOYAR DA SHI BASMALA A FARKON CIN ABINCI DA HAMDALA A KARSHEN CIN ABINCIN.
- HADDATAR DA SHI WASU DAGA SURORIN AL-QUR’AN, TARE DA FAHIMTAR DA SHI CEWA MAGANAR ALLAH TA’ALA CE. KUMA FARKON ABINDA ZA A FARA KOYA MAI SHI NE ; SURATUL FATIHA, IKHLAAS DA QUL’A’UZAI. HAKA ZA’A IYA A HADDATAR DA SHI WASU ƘASIDU DA WAƘOƘIN DA YA KAMATA A KOYAR DA YARA SU NA DAGA ABINDA KE NUNI AKAN MA’ANONIN INGANTACCEN IMANI.
- A KULA DA AMBATON SUNAN ALLAH GA YARO TA HANYAR ABUBUWAN DA AKE SO DA SUKE FARANTA RAI. YA KUMA WAJABA KAR A GWAMA AMBATON ALLAH TA’ALA DA ƘEƘASHEWA DA AZABTARWA A SHEKARUN YARINTA, KAR A YAWAITA MAGANA AKAN FUSHIN ALLAH DA AZABAR SHI DA WUTAR SHI (GA YARO).
- FUSKANTAR DA YARO AKAN KYAWUN DAKE CIKIN HALITTA, DA KARFIN IKO DA HIKIMAR ALAKAR DA KE TATTARE DA HAKAN, DAN YA JI GIRMAN MAHALICCI DA IKON SHI, YA KUMA SO ALLAH TA’ALA; DOMIN SHI ALLAH NA SON SHI, KUMA YA DAUKAKA SHI SAMA DA SAURAN HALITTU.
- HORAR DA YARO AKAN LADUBBAN DABI’U, DA SABAR MASA DA JIN KAI, DA TAIMAKON JUNA, DA LADUBBAN MAGANA DA SAURARO YAYIN DA YAKE TATTAUNAWA DA WANI, DA DASA MAI DABI’UN MUSULUNCI TA HANYAR HALAYE NAGARI, LAMARIN DA ZAI SANYA SHI RAYUWA CIKIN YANAYIN DAUKAKA, DA KOYON DUKKAN ALKAHIRAI DAGA WADANDA KE KEWAYE DA SHI.
AMMA BAYAN SHEKARUN DA YARO KE IYA TANTANCE ABUBUWA, SAI A KARA DA WADANNAN HANYOYIN TARE DA LURA DA SANYA TUNANI. HANYOYIN SU NE:
- SANAR DA YARO GIRMAN WANNAN DUNIYAR DA KYAWUN HALITTUNTA DA KYAUTATUWARTA, ZA A YI HAKAN NE DAN MUTUM YA GIRMAMA UBANGIJIN SHI YA KUMA DAUKAKA SHI. ALLAH TA’ALA YA CE: {HALITTAR ALLAH WANDA YA KYAUTATA KOWANE ABU.} [NAML: 88]
- TUNASAR DA SHI HIKIMAR ALLAH TA’ALA ACIKIN AYYUKAN SHI DA HALITTUN SHI, ZA A TUNASAR DA SHI HAKAN NE DOMIN YA SO ALLAH YA KUMA GODE MAI, KAMAR HIKIMAR DA KE CIKIN HALITTAR DARE DA YINI, DA RANA DA WATA DA HIKIMAR HALITTAR GABBAN JI, (GUDA BIYAR) KAMAR JI DA GANI DA HARSHE DA SAURAN SU. ALLAH TA’ALA YA CE: {SHIN BA ZASU YI TUNANI ACIKIN ZUKATAN SU CEWA ALLAH BAI HALICCI SAMMAI DA KASSAI DA ABINDA KE TSAKANIN SU BA FACE DA GASKIYA.}[RUM: 8]
- FA’IDANTUWA DA DAMAR DA AKA SAMU DON NUSASSHE DA YARO ABUBUWAN DA KE FARUWA TA HANYAR HIKMA DA ZAI SA SHI YASO AIKIN ALKHAIRI YA KUMA GUJE MA SHARRI. MISALI: IDAN YAYI RASHIN LAFIYA ZUCIYAR SHI TA DANFARU DA ALLAH, MU KOYA MAI ADDU’A DAN SAMUN WARAKA, MU KOYA MISHI KYAUTATA ZATO GA ALLAH. IDAN MUKA BASHI ALAWA KO KAYAN MARMARI DA YAKE SO TO, A NEMI YA GODE MA ALLAH DAGA WANNAN NI’IMAR KUMA MU FADA MISHI WANNAN KYAUTAR ALLAH NE YA BASHI, KUMA IYAYE SU GUJI KOYA MA YARO ABUBUWAN IMANI LOKACIN DA YAKE CIKIN HALI MARA DADI DOMIN BAI DA WAYON DA ZAI IYA BANBANCE TSAKANIN HAKAN.
- DOLE MAI TARBIYYA YA ZAMANA YANA YAWAN AIKATA ABUBUWAN NA ADDINI DOMIN YARO YA GANI YA SABA DA AIKATA SU SHIMA, SHIYASA AKE SON MAI TARBIYYA YA ZAMA MAI DABI’U NAGARI DAN YARO YAYI KOYI DA SHI, ZAMA MUTUM MAI ADDINI GAMI DA DABI’U NAGARI NA DAGA CIKIN ABUBUWAN DA KE SANYA TARBIYYAR MU TA ZAMA TARBIYYA TA GASKIYA BA WAI A BAKI BA KAWAI
- FA’IDANTUWA DAGA KISSOSHI MASU FA’IDA DA ZASU SA YARO YA GANE ABINDA AKE SO DA NISANTAR WANDA BA A SO, KUMA ANA IYA GABATAR DA KISSAR TA HANYAR WASAN KWAIKWAIYO TARE DA BAYYANA SAKON DA KISSAR KE ISARWA. HAKA ANA IYA BADA KISSAR TA HANYAR WAKA WADDA ITAMA TANA TAIMAKAWA WAJEN GYARA DABI’UN YARO. KUMA ANA IYA SA YARO YA SAN WAYE ANNABI ((S.A.W)) TA HANYAR BA SHI TARIHIN SHI ((S.A.W)) DOMIN YA SO SHI YA KUMA YI MAI BIYAYYA MUSAMMAN ABINDA YA KEBANCI YARINTAR SHI DA ABUBUWAN DA SUKA FARU TSAKANIN SHI DA YARA NA KYAUTATA MU’AMALA A GARE SU DA TAUSAYIN SHI AGARE SU, DA SIFFANTA YANAYIN SHI DON HAKA ANA IYA BASHI TARIHIN SAHABBAI DA MATAN MUMINAI DA MUTANEN GIDAN MANZON ALLAH ((S.A.W)) BAKI DAYA.
- DAIDAITUWA AKAN TARBIYYANTAR DA YARA AKAN ADDINI DA RASHIN DORA MUSU ABINDA BA ZASU IYA BA. KADA MU MANTA WASANNI SU NE DUNIYAR YARO TA ASALI, KADA MU DANKWAFAR DA SHI GA ABINDA ZAI HANA SHI CI GABAN DABI’UN SHI DA GYARAN ZUCIYAR SHI TA HANYAR DORA MAI NAUYIN BIN ABINDA BA ZAI IYA BA DA YAWAITA JAN SHI AKAN ABUNHWAN DA ZASU HARAMTA MAI JIN DADIN YARINTAR SHI, DOMIN WUCE GONA DA IRI AKAN HAKA YANA IYA JAWO SHARRUKA DA SANYA SHI YAJI YA CIKA AIKATA LAIFI. SO DA DAMA AN FI SAMUN HAKA AKAN DAN FARI (YARON DA AKA FARA HAIFA AGIDA) SABODA IYAYE GALIBI SUNA SON YA ZAMA ABIN MISALI GA ‘YAN BAYA SAI SU TAKURA SHI BA SU SAN SUN TAKURA SHI BA.
- YANA DA KYAU ARINKA BARIN YARO AKAN DABI’UN SHI BA TARE DA MANYA SUNA MAI SHISSHIGI AKODA YAUSHE BA SABODA YAJI DADIN BINCIKO WASANNI DA KAN SHI GWARGWADON WAYON SHI DA HANGEN SHI GA IRIN WURIN DA YAKE RAYUWA. ZA A BAR SHI AKAN HAKAN NE SABODA YARO NA SON BAYYANA ABINDA KE TARE DA SHI DA KUMA TSAYUWA AKAN KAYAN SHI.
- KARFAFA MA YARO GUIWA YANA TASIRI A ZUCIYAR SHI TASIRI MAI KYAU, KUMA YANA KWADAITAR DA SHI WAJEN DAGEWA YA AIKATA ABINDA AKE SO YA AIKATA, KUMA IDAN TARBIYYAR YARO TA KASANCE ANA YIN TA NE TA HANYAR NUNA KAUNA DA KYAUTATAWA, TO, HAKAN ZAI KAI GA SA ASAMU HALAYYA TAGARI SOSAI AWAJEN YARON. KUMA DOLE A TAIMAKAMA YARO WAJEN SANIN HAKKOKIN SHI, YA SAN ME YA KAMATA A YI MAI ME KUMA SHI YA KAMATA YA YI, YA KUMA SAN MEYE DAIDAI DA WANDA BA DAIDAI BANE A AIKATA SHI, TARE DA SANYA SHI YA SAN MATSAYIN SHI DA GIRMAN SHI, A DAIDAITA SHI AGUJI SHAGWABA SHI.
- DASA AKIDAR MUTUNTA ALKUR’ANI DA TABBATAR DA SHI A ZUCIYAR YARO, DAN YA JI GIRMAN TSARKAKAR SHI DA KUMA BIN UMURNIN ABINDA ALKUR’ANIN YA ZO DA SHI, ZA A YI HAKAN NE TA HANYA MAI JANYO HANKALI, YARO YA SAN CEWA IN DAI YA KYAUTATA TILAWAR ALKUR’ANI TO ZAI SAMI GIRMAN DARAJAR MALA’IKU KUBUTATTU. SANNAN YA KULA DA LADUBBAN TILAWA TUN DAGA FARAWA DA ISTI’AZA DA BASMALA DA GIRMAMA QUR’ANIN DA KYAUTATA SAURARON SHI. MU KUMA SABAWA YARO DA SAURARON AYOYIN ALKUR’ANI DOMIN WANNAN ZAI KARA MAI KARFIN LARABCI DA KUMA KARFAFA AKAN KARATUN QUR’ANI. KUMA ZA A IYA KOYA MAI TAFSIRIN WASU AYOYI DA SUKA SHAFI MA’ANONA NA AKIDA DAGA CIKIN SURORIN DA YAKE HADDACEWA KAMAR SURATUL FATIHA, IKHLAS, FALAK, NAS DA SAURAN SU, KUMA MU YAWAITA BIJIRO MUSU DA KISSOSHI DAGA ALKUR’ANI A TAKAICE TA YADDA YARO ZAI FAHIMTA, A RINKA MAIMATA HAKAN TA HANYOYI DABAN-DABAN.
- ANA IYA AMFANI DA HANYAR TAMBAYA DA AMSA WAJEN TARBIYYAR YARO, TAMBAYOYIN KANSU SU ZAMANA AKAN IRIN SAKON DA AKE SON ISARWA GA YARO, SANNAN AMSAR TAMBAYAR TA ZAMA A TAKAICE TA YADDA YARO ZAI YI SAURIN RIKEWA, KUMA SU ZAMANA SUNDACE DA SHEKARUN SHI DA HANGEN NESAN SHI, YIN HAKAN NA DA MATUKAR TASIRI WAJEN SAMAR DA DABI’U NAGARI GA YARO DA KUMA CANZA MUNANAN DABI’UN SHI ZUWA NAGARI.
- ANA IYA AMFANI DA KALOLI WAJEN TARBIYYA, INDA HOTUNAN DA ZA A SANYA MUSU KALA SUKA ZAMANA SUN KUNSHI MA’ANONI NA IMANI DA ZA A RINKA CANZA SU KODA YAUSHE. HAKA MA ZA A IYA KOYAR DA YARA TA HANYAR MUSABAKA TA HANYAYOYI DABAN-DABAN, KUMA AN FI SO MUSABAKAR TA ZAMA TA ABUBUWA MASU MOTSI, SABODA YARO NA SON IRIN WADANNAN KUMA YANA JAN HANKALINSU.
- AYI MA YARO SHARHIN WASU HADISAI DA SUKA SHAFI AKIDA KO WANI YANKI DAGA CIKIN SU TA YADDA ZAI YI DAI-DAI DA TUNANIN SU KUMA ABI TA HANYA MAI SAUKI KUMA MAI SOYUWA GA YARO, KUMA AYI ANFANI DA GAJERIYAR KALA TA YADDA HANKALIN YARO ZAI DAUKA, TARE DA MAIMAITA KALAMAN DA ZASU KARFAFA IMANI A ZUCIYAR YARO DON YAYI AMFANI DA SU KAI TSAYE. MISALI «ABINDA ALLAH YA KADDARA KUMA YA SO SHI KE FARUWA» «KA DOGARA GA ALLAH» «ALLAH MAI IKO NE GA DUKKAN KOMAI». SANNAN IYAYE KO MASU TARBIYYA SU TAIMAKAWA YARO WAJEN KAWATA DAKIN SHI KO AJIN SHI DA KALMOMIN IMANI MASU KYAU KAMAR: «NI MUSULMI NE. NI INA SON UBANGIJI NA. RUKUNAN IMANI DA SAURAN SU». WADANNAN HANYOYIN KOYARWAR SUNA ZAUNAR DA ABINDA AKA KARANTAR GA YARO YA ZAUNA ACIKIN KWAKWALWAR SHI TARE DA YAWAN HALARTO DA SU.
- A KARANTAR DA YARO CEWA BA WANDA KE KUBUTA DAGA BALA’I, DUKKAN MUTANEN DUNIYA ALLAH KAN JARRABE SU DA WASU BALA’O’A, KOWA DA IRIN JARRABAWAR SHI, MU KARANTAR DA SHI CEWA ALLAH BAI SA ABU YA FARU BA FACE SAI AKWAI WATA HIKIMA ACIKIN HAKAN, A DASA MAI CEWA MAI JANYO AMFANUWA GA MUTUM DA KUMA KARE SHI DAGA CUTUWA SHI NE ALLAH, KUMA RAHAMAR SHI TA RINJAYI FUSHIN SHI, KUMA A YI MAI BAYANIN CEWA KODAYAUSHE MAFITA KAN ZO NE BAYAN KUNCI, WANNAN SHI NE ABINDA MAGABATAN MU SUMA SUKA FUSKANTA, KUMA MU KARANTAR DA SHI KYAUTATA ZATO GA ALLAH, HAKAN SHIMA IBADA CE A KARAN KANTA, MU TABBATAR MAI DACEWA ZABIN ALLAH SHI NE ZABI BA ZABINMU BA, DUK ABINDA YA ZABA MANA SHI NE DAIDAI, DAN HAKA BA ABINDA YAFI MA MUTUM ALKHAIRI FIYE DA YIN HAKURI LOKACIN DA MUSIBA TA FADA MAI, KUMA YAYI AMFANI DA ABUBUWAN SHARI’A WAJEN MU’AMALA DA WADANNAN MUSIBUN, YA KUMA YARDA DA HUKUNCIN ALLAH SAI YA SAMU LADA. A KARSHE MU KOYA MAI RIKO DA ADDU’A KODA YAUSHE. HAKAN SHI NE KASUWANCI MAFI RIBA GA BAWA KODA YAUSHE.
HANYOYIN
TARBIYYA
DAGA CIKIN MUHIMMAN HANYOYIN TARBIYYA DA ZASU TAIMAKA WAJEN DASA IMANI ACIKIN ZUCIYAR YARO SUNE:
- ABIN KOYI NAGARI: ANA KIRGA ZAMA ABIN KOYI NAGARI DAYA DAGA CIKIN MANYAN HANYOYIN TARBIYYA DA KUMA TASIRI AKAN YARO, MANZON ALLAH ((S.A.W)) YA TUNASAR AKAN MUHIMMANCIN ZAMA ABIN KOYI NAGARI GA RAYUWAR YARO. YA ZO A HADISIN ABDILLAHI BINI AMIR ((R.A)) YA CE: (WATA RANA MAHAIFIYA TA TA KIRA NI ALHALI MANZON ALLAH ((S.A.W)) YANA WAJEN MU, SAI TA CE: YA ABDALLAHI ZO KA KARBA, SAI MANZON ALLAH ((S.A.W)) YA CE: ((ME ZAKI BA SHI)) TA CE: INA SO IN BASHI DABINO NE, SAI MANZON ALLAH ((S.A.W)) YA CE: ((DA ACE KE BAKI BASHI KOMAI BA DA AN RUBUTA MIKI KIN YI KARYA)) [ABU-DAWUD: 4991]. YA ZO ACIKIN WATA RUWAYA ((DUK WANDA YA CE MA YARO ZO KA KARBA KUMA YAKI BASHI KOMAI TO YAYI KARYA.)) [AHMAD: 9624]. WANNAN HADISIN YA NUSASSHE MU DA MUHIMMANCIN YIN GASKIYA AGABAN YARA.
- WA’AZI NA GASKIYA: ANA IYA GABATAR DA WA’AZI TA HANYOYI DABAN-DABAN, KO DAI AYI SHI KAI TSAYE KO KUMA TA HANYAR BUGA MISALI, KO TA HANYAR BADA KISSA, KO TATTAUNAWA KO MAKAMANCIN HAKA, KUMA A TAKAITA MAI WA’AZIN DAN KAR YA KOSA.
- KWADAITARWA DA TSORATARWA: WANNAN HANYAR, ANA KIRAN WADANNAN HANYOYI GUDA BIYU, KYAUTATAWA DA UKUBA, KUMA ANA KIRGA WANNAN SALON DAGA CIKIN MAFI BAYYANAR HANYOYIN TAUSAYI, TA INDA YAKE TABA FIDIRAR MUTUM DA ALLAH YA HALICCE SHI AKAI. WANDA SHI NE SON ABU MAI AMFANI DA KUMA JAWO SO GA YARO. DA TUNKUDE CUTUWA. HAKAN YANA WAJABA YA KASANCE DA ADALCI DA GASKIYA BA TARE DA WUCE GONA DA IRI AKAN HAKAN BA. YARO MUTUM NE ME TSARKAKEKKIYAR ZUCIYA, BAYA KAMATUWA A TSORATAR DA SHI KO A FIRGITA SHI SABODA ZUCIYA TANA DA SAURIN TASIRANTUWA, DAN HAKA YA KAMATA A RINJAYAR DA BANGAREN KWADAITARWA SABODA YARO A WADANNAN SHEKARUN YAFI BUKATAR KWADAITARWA FIYE DA TSORATARWA.
- HORARWA DA SABARWA DA YAWAITA YIN ABU: A SABARMA YARO DA KWADAYIN NEMAN YARDAR ALLAH DA TSORON SHI DA JIN KUNYAR SHI, DA KUMA DOGARO DA SHI AKODA YAUSHE, A KUMA SANYA SHI YA SABA DA CEWA DUKKANIN AL’AMURA AGURIN ALLAH ((S.W.T)) SUKE. DUKKAN WADANNAN ABUBUWAN ZASU SA YA YI KWADAYI DA KUMA YIN RIKO DA RA’AYIN SHI AKAN KOWANE AIKI, ZAI KUMA HAIFAR MAI DA YARDA DA YAKINI DA ZUCIYAR SHI ZATA NATSU DA SHI YA SAMU JIN DADI A ZUCIYAR SHI.
- MAIMAITAWA: HANYA CE TA TABBATAR DA ILIMI, YAWAN MAIMAITA ABU NA SA YA ZAUNA ACIKIN KWAKWALWA, BAMA GA YARO BA HATTA GA BABBA.
- TATTAUNAWA: TATTAUNAWA DA YARO KAN SA SHI YA SAMU HANGEN NESA KUMA YA BUDE MAI KOFOFIN SANIN ABUBUWA, SAI DAI DOLE A GIRMAMA RA’AYIN YARO SHI KAN SHI A KUMA KYAUTATA SAURARON SHI TARE DA TATTAUNAWA DA SHI CIKIN NATSUWA DON A SAMU NASARA A CIKI. TA DALILIN TATTAUNAWAR ZA A IYA TARBIYYAR YARON DA NUSASSHE SHI AKAN ABUBUWA DA DAMA.
- LITTAFI: DAGA CIKIN HANYOYI NA TARBIYYA AKWAI SAMAR DA DAKIN KARATU MAI KYAU DA YA DACE DA BUKATUWAN YARO DA WAYEWA DA IMANI, ZAI YI KYAU YA ZAMA NAU’I-NAU’I TSAKANIN NA JI DA GANI DA KUMA NA LANTARKI. MAFI MUHIMMANCI SHI NE DAKIN KARATUN YA ZAMANA YA KUNSHI BANGAREN KISSOSHI, DOMIN KISSA HANYA CE TA CI GABAN TARBIYYA, KUMA A CIKIN TARIHIN MANZON ALLAH ((S.A.W)), DA NA SAHABBAI ALLAH YA YARDA DA SU AKWAI KISSOSHI DA SUKE DA MANUFA GA ABUBUWA MASU YAWA DA ZA A FADA MA YARO.
- AMFANI DA KAYAN KARANTARWA NA ZAMANI: WADANNAN KAYAYYAKIN SUNA BUDE TUNANIN YARO SU KUMA TABBATAR DA SHI SU MATSO MAI DA ABU KUSA, HAR YA IYA FAHIMTAR ABUN NAN YA HARARO MA’ANONINSA. TA YADDA ZA A BIJIRO MAI DA WADANNAN TUNANIKAN TA HANYA MAI DAUKAR HANKALI DA AMFANI DA LAUNUKA DA ZASU JA HANKALIN YARO SU KWANTAR MAI DA HANKALI SU KUMA DACE DA ABINDA YAKE SO.
- ABINDA AKA HALICCI MUTUM AKAN SHI: AKWAI WASU ABUBUWA MASU YAWA GA YARO DA AKA HAIFE SHI DA SHI KAMAR; WASANNI DA TAIMAKO DA KWAIKWAYON MUTANE DA MAKAMANCIN HAKA, TA HANYAR WASA YARO ZAI IYA GANE IRIN DUNIYAR DA YAKE CIKI, DA KUMA FITAR DA ABINDA YAKE SURANTAWA DA KUMA IYAKACE HANGEN NESAN SHI, ZA A IYA FITAR DA HAKA TA HANYAR FAYYACE INGANTATTUN MA’ANONIN ABUBUWAN DAKE GEWAYE DA SHI, HAR WA YAU KUMA SABODA DASA DABI’U NAGARI A ZUCIYAR YARO, ZA A YI HAKAN NE TA HANYA MAFI SAUKI KUMA TA HANYAR DA TA DACE
- ADDU’A: ADDU’A DALILI NE DA BAWA ZAI KANKAN DA KAI GA UBANGIJIN SHI DA BUKATUWAR SHI ZUWA GARESHI DA KUMA FATAN SHI GA FALALAR SHI ((S.W.T)), ALLAH YA KWADAITAR DA BAYAIN SHI AKAN YIN ADDU`A KUMA YAYI MUSU ALKAWARIN AMSAWA. ALLAH ((S.W.T)) YA CE: {KUMA UBANGIJIN KU YA CE KU ROKE NI ZAN AMSA MUKU.} [ GHAFIR: 60], KUMA ADDU’A NA DAGA CIKIN MAFI GIRMAN HANYOYIN DA MAI TARBIYYA ZAI KAI GA KOLOLUWAR ABINDA YAKE SO YA KAI A TARBIYYA, ITA CE HANYAR DA MANYAN MASU TARBIYYA SUKA YI AMFANI DA ITA WAJEN TARBIYYA, WATO ANNABAWAN ALLAH ALAIHIMUSSALAM DAN SU TABBATAR DA IMANI DA TAUHIDI. ALLAH ((S.W.T)) YA CE: {KA TUNA SANDA IBRAHIM YA CE: YA UBANGIJI NA KA SANYA WANNAN GARI AMINTACCE KUMA KA NISANTA NI DA ‘YA’YA NA DAGA BAUTA MA GUMAKA [IBRAHIM: 35] ADDU’A GA YARO NA DA MUHIMMANCI MATUKA.
- KAMANTAWA DA KWAIKWAYO: YARO A DABI’AR SHI YANA SON KWAIKWAYO, TUNDA HAKA NE, SAI A SAMU WATARANA MISALI YA ZAMA LIMAMIN MASALLACI, YAYI SALLAH YAYI KARATU, KO YA YI HUDUBA, YA TASHI YAYI MAGANA, KO YA TASHI A MATSAYIN MALAMI YA KOYAR TARE DA YIN BAYANI, DA MAKAMANTAN HAKA. WANNAN SHI NE ABINDA ZAI BAYYANA MAI ABUBUWAN DA AKE NUFI YA KUMA KIYAYE KIMAR WADANNAN ABUBUWAN AGARE SHI.
SIFFOFIN
ME TARBIYYAH
- TAUSAYI DA JIN KAI. DADIN TARBIYYA BAYA ZUWA MATUKA BA IDAN BA A HADA DA TAUSAYI BA DAN ZUCIYA TA MAMAYE DA RAHMA, GA AKRA’U BIN HABIS YANA KALLON MANZON ALLAH. ((S.A.W)) YANA SUMBATAR HASAN DA HUSAIN, SAI YA CE: INA DA ‘YA’YA GOMA BAN TABA SUMBATAR DAYA DAGA CIKIN SU BA, SAI MANZON ALLAH ((S.A.W)) YA CE:(( DUK WANDA BAYA JIN KAI BA ZA A JI KAN SHI BA.)) [BUKHARY: 5997], KUMA MANZON ALLAH ((S.A.W)) YA CE (( MASU RAHMA AR-RAHMAN YANA JIN KAN SU, KU JI TAUSAYIN WADANDA KE DORON KASA, SAI WANDA KE SAMA YA JI KAN KU)) [ ABU-DAWUD: 4941]
- HAKURI DA YAFIYA: MANZON ALLAH (S.A.W) YA KAI KOLOLUWA A WADANNAN DABI’UN, ANAS BIN MALIK (R.A) YA RAWAITO CEWA (WATA RANA INA TAFIYA TARE DA MANZON ALLAH (S.A.W) YANA SANYE DA MAYAFI DAN NAJRANA MAI CIN BAKI, SAI WANI BALARABEN KAUYE YA HADU DA SHI, SAI YA JA MAI MAYAFINSA DA KARFI HAR SAI DA NA GA KAFADAR MANZON ALLAH (S.A.W) BAKIN MAYAFIN YAYI MATA SHEDA SABODA TSANANIN FIZGAR DA YAYI MAI, SAI YA CE YA MUHAMMAD KA BANI DAGA DUKIYAR ALLAH DA KE WAJEN KA, SAI MANZON ALLAH (S.A.W) YA JUYA ZUWA GARE SHI YAYI DARIYA SANNAN YAYI UMURNIN A BASHI. [BUKHARY: 5809].
- DAGA CIKIN AL’AMURAN DA SUKE TAFIYA TARE DA HAKURI AKWAI AFUWA. ALLAH (S.W.T) YA CE: {KA RIKI AFUWA KUMA KAYI UMURNI DA ABU MAI KYAU, KUMA KA KAU DA KAI GA BARIN JAHILAI} [A’ARAF: 199], DUK DAN A TABBATAR DA HAKURI MANZON ALLAH (S.A.W) YA KWADAITAR AKAN RASHIN YIN FUSHI KUMA YAYI HANI AKAN SHI, YA ZO A CIKIN HADISI INGANTACCE CEWA WANI MUTUM YA CE MA MANZON ALLAH (S.A.W) KAYI MIN WASIYYA, SAI ANNABI (S.A.W) YA CE: ((KADA KAYI FUSHI)) SAI MUTUMIN YA MAIMAITA, SAI YA CE MAI ((KADA KAYI FUSHI)) [BUKHARY: 6116]
- JURIYA: YA WAJABA GA MAI TARBIYYA YA KAWATU DA JURIYA DA KUMA RASHIN GAGGAWA YAYIN TARBIYYA KO KARANTAR DA ‘YA’YAN SHI, KUMA KADA MAI TARBIYYA YAYI GAGGAWA WAJEN BAYYANA SAKAMAKON ABINDA YA KE YI NA TARBIYYA, HAR YA SANYA MA KAN SHI DEBE TSAMMANI DA KUMA JIN SAMUN MATSALA ACIKIN TARBIYYAR DA YAKE YI, IDAN MAI TARBIYYA YA ZAMANA BASHI DA HAKURI TO KAMAR MAI TAFIYA NE BA GUZURI.
- ADALCI: IDAN AKA BANBANCE TSAKANIN MUTUM DA MUTUM BA TARE DA WANI DALILI BAYYANANNE BA TO, ZA A SAMU KARANCIN TASIRANTUWA DA CUREWA AWAJEN WADANDA AKE TARBIYYANTARWA, KUMA DUK SANDA AKA SAMU ZALUNCI ACIKIN WANI ABU TO SAI ZALUNCIN NAN YA MUNANA SHI.
- AMANA: YA WAJABA GA MAI TARBIYYA YA KASANCE MAI GASKIYA KUMA AMINTACCE AWAJEN MU’AMALAR SHI GA WADANDA YAKE TARBIYYA, AMANA NA DAGA CIKIN SIFFAR MANZONNI, KUMA ITA CE BABBAR ABINDA AKE NEMA WAJEN KYAUTATA AIKI DA KAIWA GA KOLOLUWAR SHI DA CIN NASARAR SHI.
- TSORON ALLAH: DUK WANDA YAJI TSORON ALLAH TO, ZAI DATAR DA SHI TA INDA BAYA TSAMMANI, TSORON ALLAH YANA SA A SAMU DACEWA DA TSIRA DA GYARUWA DA CIN NASARA DUNIYA DA LAHIRA.
- TSARKAKE ZUCIYA: DUK AIKIN DA YA KASANCE BA DAN ALLAH BA TO ZA A MAYAR MA MUTUM DA ABIN SHI, KUMA ZAI ZAMANA BABU KOMAI ACIKIN AIKIN SHI FACE AIKIN BANZA.
- ILIMI: SHI MAI ILIMI YA NA KASANCEWA NE MAI HANGEN ABINDA KE FARUWA YANZU DA WANDA ZAI BIYO BAYA, SABANIN JAHILI WANDA KE ASARAR ABINDA KE FARUWA YANZU YA KUMA MUNANA ABINDA ZAI ZO A GABA.
- HIKIMA: ANAN, MAI TARBIYYA ZAI SANYA KOMAI INDA YA DACE A SANYA SHI, DOMIN AL’AMURA SUNA BADA AMFANINSU NE, SAI TARBIYYA TA FIDDA SAKAMAKON, AIKIN MAI TARBIYYA SHI NE YA SHIGA ZUWA CIKIN ZUCIYA YA CI GABA DA NUSASSHE DA YARO DA TARBIYYAR SHI.
- IMANI DA AIKIN TARBIYYA: IMANI SADAUKARWAR ZUCIYA NE DA RUHI, WANDA BAI YI IMANI DA AIKIN TARBIYYA BA TO BA ZAI IYA GABATAR DA WANNAN NAU’IN NA SADAUKARWA BA.
- CI GABA: MAI TARBIYYA YA BADA MUHIMMANCI WAJEN CI GABAN ABUBUWAN DA YAKE YI DOMIN YA KAI ZUWA GA MATAKIN BADA ABINDA YA KAMATA YA BADA NA TARBIYYA.