TAMBAYOYI DA SUKA SHAFI MALA’IKU

SU WAYE MALA’IKU? YAYA SUKE?

SU HALITTA CE DAGA CIKIN HALITTUN ALLAH, AN HALICCE SU NE DAGA HASKE, ALLAH YA HALICCE SU NE KAFIN MUTANE, SUNA DA NUFI, DA TUNANI DA FUKA-FUKAI, KUMA YANAYIN HALITTARSU NA DA KYAU, KUMA SUNA DA IKON KWAIKWAYON SURAR MUTANE, BA SA CI BA SA SHA, KUMA SU BAYIN ALLAH NE WADANDA SUKE AIKATA ABIN DA AKA UMARCE SU, KUMA MATSAYI-MATSAYI SUKE DA SHI , SHI JIBRILU AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI – AN BA SHI AIKIN ISAR DA WAHAYI GA MANZANNI – AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SU – KUMA AKWAI MIKAEL, ISRAFIL DA SAURANSU, DAGA CIKINSU AKWAI MASU KULA WAƊANDA AKA ƊORA WA ALHAKIN KIYAYE AYYUKAN BAYI A KOWANE LOKACI, KUMA AKWAI ADADI MAI YAWA NA MALA`IKU, KUMA KOWANE DAGA CIKIN MALA`IKU YANA DA AIKINSA WANDA DOLE NE YA AIWATAR DA SHI.

YAYA SUNAYEN MALA’IKU?

MALA’IKU NA DA YAWA, KUMA ALLAH – MAI ALBARKA DA DAUKAKA – NE KADAI YA SAN ADADIN SU. DAGA CIKIN SUNAYEN SU: JIBRIL, MIKA’ILU, ISRAFIL, RADWAN, DA MALIK.

– AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SU -, KUMA AKWAI MASU RIKE DA AL`ARSHI, DA MASU KIYAYE AYYUKAN BAYI, DA SAURANSU.

SABODA ME ALLAH YA HALICCE SU?

ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA HALICCI MALA’IKU. DON AIKATA ALHERI, GABA DAYANSU ALHERI NE BASA AIKATA MUGUNTA BASU MA SANTA BA, KUMA MALA’IKU TUN ASALI SUNA SAMA, SAI DAI SAUKOWAR MUTUM ZUWA DUNIYA YA SANYA DOLE NE SAUKOWAR MALA’IKU ZUWA GURINSUDOMIN YIN WASU AYYUKAN DA ALLAH YA UMURCE SU DASU, NA DAGA KIYAYEWA, KULAWA, LURA, SADARWA, TAIMAKAWA, NEMAN GAFARA, HALARTAR TARUKAN ZIKIRI, DA SAURAN AYYUKA, KUMA ANA IYA FADAWA YARO CEWA MALA’IKU SUNA DA MANYAN AYYUKA GUDA BIYU : BAUTA WA ALLAH MADAUKAKI, DA TAFIYAR DA AL’AMURAN DUNIYA.

ME YASA BAMA GANIN MALA’IKU?

’YAN ADAM BA SU DA IKON GANIN MALA’IKU A CIKIN SURAR DA ALLAH YA HALICCE SU, SABODA HAKA; MALA’IKU SUNA ZAMA SURAR MUTUM; DON MUTANE SU GANSU SU YI MU’AMALA DA SU, KAMAR YADDA MALA`IKA JIBRILU – AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI YA ZO A SIGAR BALARABE, KAMAR YADDA YAKE A HADISIN KARANTAR DA AL’AMURAN ADDINI.

SU WAYE ALJANU?

HALITTA CE DAGA CIKIN HALITTUN ALLAH, ALLAH YA HALICCE SU DAGA WUTA, KUMA AN DORA MASU NAUYIN YIN BIYAYYA GA UMARNI DA HANI, KUMA SU HALITTA NE DA KE MUTUWA KAMAR SAURAN HALITTU, BA ZA MU IYA GANIN SU BA KUMA BA MU DA IKON YIN HAKAN, KUMA ALLAH YA HALICCE SU DA ABUBUWAN DA SUKA BAMBANTA DA NA MUTUM, DON HAKA ZA SU IYA TASHI, SU YI SAURI, KUMA SU IYA SAUYAWA, KUMA HALITTAR ALJANU TA BANBANTA DA TA MUTANE. DOMIN AN HALICCI MUTANE DAGA YUMBU, ALHALI KUWA ALJANI AN HALICCE SHI NE DAGA WUTA.

WANENE YA FI KARFI: MALA’IKU KO ALJANNU?

MALA’IKU HALITTACE MAI ZARCEWA, KUMA BASA MUTUWA HAR SAI RANAR DA ZA A BUSA KAHO, AMMA ALJANNU, SUNA MUTUWA GABANIN HAKAN, SABODA SUN KASANCE A HAKA. MALA’IKAN MUTUWA SHI NE WANDA YAKE KARBAR RAYUKA DA UMARNIN ALLAH MADAUKAKIN SARKI IDAN YA YANKE HUKUNCIN MUTUWARSU: (ALLAH YANA KARBAR RAYUKA YAYIN  MUTUWARSU) (AZ-ZUMAR: 42), DON HAKA MALA’IKU SUN FI KARFI A WANNAN BANGARE, KUMA KODA A RAYUWAR DUNIYA CE. ALJANU SUNA TSORON MALA’IKU, KAMAR A YAKIN BADAR LOKACIN DA SHAIDAN YA GA MALA’IKUN DA ALLAH YA AIKO DON TALLAFAWA MUMINAI. YA CE WA KAFIRAI: “NI BARRANTACCE NE DAGA GARE KU, DOMIN NA GA ABIN DA BA KWA GANI NA JI TSORON ALLAH KUMA ALLAH MAI TSANANIN UKUBA NE” (AL-ANFAL: 48)

SHIN MALA’IKU SUNA MUTUWA?

E, MALA’IKU HALITTA CE DAGA HALITTAR ALLAH, KUMA KOMAI YANA MUTUWA FACE ALLAH – TSARKI YA TABBATA A GARE SHI DA BUWAYA – DOMIN SHI RAYAYYE NE KUMA TSAYAYYE, (KOMAI MAI MUTUWA NE  FACE FUSKARSA) (ALKASAS: 88). DON HAKA DUK MUTANEN DUNIYA ZASU MUTU, HAKA MA NA SAMA ZASU MUTU SAI WANDA ALLAH YASO, KUMA BABU WANDA ZAI WANZU SAI ALLAH MADAUKAKI, DOMIN SHI RAYAYYE NE WANDA BAYA MUTUWA.

'Fel a tetejéhez' gomb