GAME DA TARBIYYAR IMANI TARBIYYA

TARBIYYA ABIN BUKATUWA CE NA DAN ADAM, TANA DAGA CIKIN LALURORIN GINA MUTUM, ITACE KAYAN GINA YARO DA BUNKASA SHI TA DUKKAN BANGARORIN RAYUWA. TA HANYAR TARBIYYA NE AKE GINA HALAYYAN YARO NA ZAMANTAKEWA DA ILIMI DA RAYUWA DA LAFIYA DA SAURAN SU.  KAFIN MU FARA MAGANA AKAN TARBIYYAR GINA IMANI DA MUHIMMANCIN TA, ZAI YI KYAU MU FAHIMCI MECECE TARBIYYAR ITA KAN TA, ME AKE NUFI DA ITA? KUMA ME MA`ABOTA TARBIYYA KE BUKATA GAME DA ITA?

MA`ANAR

TARBIYYA

TARBIYYA AIKI NE MAI MANUFA, WACCA MANUFARTA ITA CE CI GABA , KUMA TANA DA DOKOKI DA KA`IDOJI, TANA KAI WA ZUWA GA GINA DABI`U NAGARI TA HANYAR SHIRYARWA DA HORARWA DA WAYARWA DA TARBIYYANTARWA DA YAWAN AIKI. KUMA TARBIYYA NA NUFIN KIYAYE ABINDA AKA GINA YARO AKAN SHI DA KUMA KULA DA SHI, TARE DA BUNKASA BAIWAR SHI A RAYUWA, SANNAN A FUSKANTAR DA ASALIN HALITTAR YARO ZUWA GABA DA ZUWA GA ABINDA ZAI TABBATAR DA GYARUWA  DA CIKAR TA DA TA DACE DA ITA, WACCA TAKE TAIMAKAWA WAJEN SHIRYA MUTUM  YA ZAMA NAGARI DAN YA GINA KAN SHI. KUMA TARBIYYA ITA CE MAKAMMASHIN DAKE SAITA MUTUM A DUKKAN FANNONIN RAYUWA.

MUHIMMANCIN

TARBIYYAR IMANI

IMANI SHINE HAKIKANIN SAMUWA BABBA DA KUMA ABU MAI GIRMA DA YA SHAFI MUTUM, YANA DA HANYOYI MABANBANTA ACIKIN TAFIYAR MUTUM A RAYUWAR DUNIYA. ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA CE:

{DAGA CIKIN SU AKWAI WADANDA SUKAYI IMANI, KUMA DAGA CIKIN SU AKWAI WADANDA SUKA KAFIRCE.} [AL-BAKARAT: 253].

KUMA AKAN SHI AKE GINA HALAYYARSU DA AYYUKAN SU, KUMA SHINE ABINDA ZAI BANBANCE MAKOMARSU A RAYUWAR LAHIRA. DAGA CIKIN MATAKAN RARRABEWA A RAYUWAR MUTUM SHI NE RAYUWAR YARINTA SABODA ABINDA AKE DASAWA A ZUCIYAR YARO A WANNAN MATAKIN NA DAGA AKIDU DA DABI`U DA AL`ADU TA FUSKOKIN DA ZAI WAHALAR KO YA CI TURA WAJEN CANZA SHI MAIMAKON TABBATAR DA SHI. KILA MA TABONSA YA ZAUNA A ZUCIYAR MUTUM TSAWON RAYUWASA; DON HAKA TARBIYYAR IMANI A MATAKIN YARINTA TANA DAGA CIKIN MATAKAN GINI DA AKE GINA RAYUWAR MUTUM AKAN TA TSAWON RAYUWARSA A WANNAN DUNIYA.

TARBIYYA A DUNKULE ITACE KULA. BABU TARBIYYA IN BA KULA, KUMA MAFI ABINDA ZA A FI KULA DA SHI SHI NE YA KASANCE A BANGAREN IMANI. MUNA CIKIN ZAMANIN DA MAFI YAWAN MASU BINCIKE AKAN TARBIYYA SUN FI KARKATA  A FANNIN TARBIYYAR HANKALI DA JIKI TARE DA WOFANTAR DA BANGAREN IMANI DA RUHI, SUNA FUSKANTAR DA TUNANIN SU WAJEN TABBATUWAR CIN NASARA DA TSIRA A DUNIYA DA SAMUN DUKIYA, BA TARE DA BADA MUHIMMANCI AKAN SHIRIYA WADDA ZATA KAI  SU ZUWA GA JIN DADIN LAHIRA BA, WANNAN NE YASA KALLON MU GA  TARBIYYA YA BANBANTA SOSAI  DA IRIN KALLON DA SU SUKE MA TARBIYYAR.

KUMA BABU TANTAMA CEWA TARBIYYAR IMANI ACIKIN MUSULUNCI ITA CE DAYA DAGA CIKIN RUKUNAN GINA TARBIYYA A RAYUWAR MANZON ALLAH ((S.A.W)) MAI TSARKI. DAGA IBN  UMAR ((R.A)) YA CE:NA JI MANZAON ALLAH ((S.A.W)) YANA CEWA: ((DUKKAN KU MASU KIWO NE KUMA KOWANENKU ABIN TAMBAYA NE AKAN KIWON SHI, SHUGABA MAI KIWO NE KUMA ZA A TAMBAYE SHI AKAN KIWON SHI, MACE MAI KIWO CE A GIDAN MIJIN TA KUMA ZA`A TAMBAYE TA AKAN KIWON TA.)) [BUKHARY 2558, MUSLIM 1829].

MANZON ALLAH ((S.A.W)) YA TUNASAR AKAN GIRMAN NAUYIN DAKE RATAYE AWUYAN KOWANNEN MU, KUMA NAUYI NE DA BA MAKAWA KOWA SAI AN TAMBAYE SHI AKAN SHI: MAI KA GABATAR GA WANDA KE KARKASHIN KULAWAR KA? KUMA YA ZO DAGA MANZON ALLAH ((S.A.W)): (( DUK WANDA ALLAH YA BASHI KIWO BE KULA DA KIWON NAN TA HANYAR NASIHA  BA TO, BA ZAI JI KAMSHIN ALJANNAH BA.)) [BUKHARY 7150]. ANAN MANZON ALLAH ((S.A.W)) YA YI ISHARA ZUWA GA MUHIMMANCIN GABATAR DA NASIHA TA GASKIYA DA AMANA, TA YADDA NASIHA ZATA MAGANCE MATSALAR WANDA AKE MA NASIHA TA KOWANE GEFE. KUMA YANA DAGA CIKIN ABINDA AKE RAWAITOWA A WANNAN BABIN MAGANAR IBN UMAR ((R.A)) CEWA: (KA LADABTAR DA DAN KA DOMIN ZA`A TANBAYE KA AKAN SHI. AKAN ME KA LADABTAR DA SHI? KUMA ME KA KOYA MAI? KUMA SHI ABIN TAMBAYA NE AKAN YI MAKA BIYAYYA DA KUMA BIN UMURNIN KA). [SHU`ABUL IMAN:8141]. ANAN IBN UMAR YANA TABBATAR MANA DA CEWA NAUYIN `YA`YA NA RATAYE NE AKAN WUYAN IYAYE, SUNE MAKOMA TA FARKO WAJEN KARANTAR DA SU DA LADABTAR DA SU.

AN KUMA RAWAITO CEWA TARBIYYA TAFI SADAKA ALKHAIRI, IN DA AKA CE: (MUTUM YA LADABTAR DA DAN SHI YA FI ALKHAIRI FIYE DA YAYI SADAKA DA SA`I DAYA) [ TIRMIZIY:1951] KAMAR YADDA AKA RAWAITO CEWA KOYA MA YARO DABI`U NAGARI YAFI FIYE DA ABUBUWAN DA AKE BASHI. KUMA YANA DAGA CIKIN ABINDA AKE RAWAITOWA (UBA BE TABA BAMA DAN SHI WANI ABU BA FIYE DA DABI`U NAGARI) [TIRMIZI 1952]. DUKKAN WADANNAN NASSOSHIN DA SAURAN SU SUNA NUNI AKAN TARBIYYA DA KARANTARWA SU NE MAFI MUHIMMANCIN ABINDA IYAYE ZASU BAMA DANSU.

MUN KASANCE A BAYA MUNA TARBIYYAR IYALAN MU A YANAYI WANDA YAKE KAMAR A RUFE, AMMA YANZU MUNA TARIBIYYAR AMMA KOFOFIN GIDAJEN MU DA WINDUNAN MU SUNA BUDE AKAN DUNIYA, DAN HAKA SUNA GANIN ABUBUWA MASU KYAU DA MARA SA KYAU GAME DA DUNIYA. AMMA IDAN BA MU KULA MUN SAN ME KE GUDANA BA DA KYAU HAKIKA MUNANAN ABUBUWA ZA SU KORE KYAWAWA, ZAMU IYA FAHIMTAR ALAMUN CANJE-CANJEN ABUBUWAN DA KE FARUWA IDAN MUKA BADA MUHIMMANCI WAJEN BIBIYAR SAURIN CANJIN DA KE FARUWA A KEWAYEN MU DA KUMA KARANTAR CIGABAN TARBIYYA SOSAI DA KUMA BADA MUHIMMANCIN MAI TARBIYYA AKAN WANNAN, ZAI BASHI DAMA WAJEN KOKARIN DASA IMANI ACIKIN ZUKATAN YARA TUN DAGA GIDA, WANDA KOWA ZAI TAIMAKA WAJEN GINA SHI TA HANYAR ZABAR MAKARANTAR DA ZA A SA YARO TUN DAGA NURSERY HAR ZUWA FIRAMARE DA SAKANDARE WADANDA SUKE KULA DA WANNAN FANNIN NA DASA IMANI. GAFALA DAGA FAHIMTAR ABINDA KE FARUWA A KEWAYEN MU NA NUFIN FARUWAR ASARAR DA BA WATA HANYAR DA ZAMU IYA MAYAR DA ITA. SAI DAI A CI GABA DA TARBIYYA DA HAKURI ZAMU SAMU BABBAN SAKAMAKO DA YARDAR ALLAH. TARBIYYA BA IYA LURAR DA SHI NA WANI DAN LOKACI BANE KADAI, TANA BUKATAR BIBIYA DA CI GABA DA DORA SHI AKAN HANYA.

TARBIYYAR

IMANI DOLE CE

LALLAI YARA MASU TASOWA A WANNAN ZAMANI SUNA FAMA DA WATA IRIN FIZGA A ZUKATANSU DA TUNNINSU, SAKAMAKON YADDA ABUBUWA SUKE A BUDE HANHAI, WANNAN YASA IRE-IREN ABUBUWAN DA SUKE KEWAYE DA MATASA SUKE FIZGAR SU TA KO INA SUNADA MATUKAR HATSARIN DA BAI KAMATA MUYI WASA DASU BA, MU KUMA TASHI TSAYE MU KAMA AIKI MAFI WAHALA A SAMUWAR DAN ADAM WANDA SHI NE TARBIYYA. DAGA CIKIN ABINDA KE NUNI AKAN DOLE A GINA YARO AKAN TARBIYYA TA IMANI DA KUMA TSANANIN BUKATUWAR AL`UMMA AKAN HAKA SHINE: ANNABAWA DA SALIHAN BAYI DA MAGABATA SUN KASANCE SUNA BADA MUHIMMANCI WAJEN GINA IMANI DA KARANTAR DA SU AKAN SHI MUSAMMAN MA GA YARA. KADAN DAGA CIKIN MISALAI AKAN HAKA SHI NE FADAR ALLAH MADAUKAKIN SARKI GAME DA ANNABI NUHU ACIKIN KIRAN SHI GAME DA DAN SHI DA KUMA TSORATAR DA SHI GAME DA ABOKANTAKA DA MA`ABOTA BATA, INDA YACE: { YA KAI DANA ZO KA HAU TARE DA MU KADA KA KASANCE TARE DA KAFIRAI.} [HUD:42]. HAKA KUMA ALLAH MADAUKAKIN SARKI YANA BAMU LABARIN WASIYYAR ANNABI IBRAHIM GA DANSA CEWA: { KUMA IBRAHIM YAYI WASIYYA DA ITA GA `YA`YAN SHI HAKA MA YA`AKUB YA KU  `YA`YA NA LALLAI NE ALLAH YA ZABA MUKU ADDINI, DAN HAKA KADA KU MUTU FACE SAI KUNA MUSULMAI} [BAKARA: 132]. KUMA A FARKON WASIIYAR ANNABI LUKUMAN YANA TSORATAR DA DAN SHI AKAN SHIRKA YA CE: {YA KAI DANA KADA KAYI SHIRKA DOMIN SHIRKA ZALUNCI NE MAI GIRMA} [LUKMAN:13]. ANNABI ((S.A.W)) YANA YIMA IBN ABBAS WASIYYA YANA CEWA (( YA KAI YARO ZAN SANAR DA KAI WASU KALMOMI. KA KIYAYE ALLAH ZAI KIYAYE KA, KA KIYAYE ALLAH ZAKA SAME SHI  GABAN KA, IDAN ZAKA YI ROKO TO KA ROKI ALLAH, KUMA IDAN ZAKA NEMI TAIMAKO TO KA NEMA TAIMAKON ALLAH.)) [TIRMIZIYYU:2516]. AKWAI KWADAITARWA AKAN GINA IMANI ACIKIN WANNAN.

KUMA DAGA CIKIN ABIN DA KE NUNI AKAN TARBIYYA DOLE CE SHI NE SANIN CEWA KOYAR DA IMANI SHINE GINSHIKIN ILIMOMI DA TUSHEN SHI, IDAN YARO YA SAN IMANI KUMA AKA DASA MAI SHI A ZUCIYA KAMAR YADDA ANNABI ((S.A.W)) YAZO DA SHI, TO IBADU DA SAURAN FANNONAN ADDINI ZASU ZO DAGA BAYA, BADA MUHIMMANCI AKAN HAKAN DALILI NE NA DACEWA DA SHIRIYA DA YARDAR ALLAH. DA YAWA DAGA CIKIN AL`AMURA AN KULLA SU NE DA IMANI DA ALLAH DA RANAR LAHIRA, SHI KUMA IMANI DUK LOKACIN DA YA KASANCE ANA HALARTO DA SHI DA KARFI TO YANA TOSHE MA MUTUM BIN HANYAR DA AKA HANA BI.

HAKA, DAGA CIKIN ABINDA KE BAYYANA MUHIMMANCIN TARBIYYA SHI NE ABIN DA MUKE GANI DAGA WAJEN WASU IYAYE NA WOFANTAR DA KARANTARA DA YARANSU AL`AMURAN DA SUKA SHAFI IMANI DA HUJJAR CEWA YARA NE WANDA IDAN SUN GIRMA KUMA BA ZASU IYA KARANTAR DASU HAKAN BA. DUK WANDA YA WOFANTAR DA KARANTAR DA DAN SHI ABINDA ZAI AMFANE SHI YA BARSHI HAKANAN SAKAKA HAKIKA YA SABA MATUKAR SABAWA, DA YAWA DAGA CIKIN YARA LALACEWARSU TA ZO NE DAGA IYAYENSU SANADIN SAKACINSU DA RASHIN KARANTAR DASU FARILLAN ADDINI DA SUNNONIN SHI, SUKA BATA MUSU LOKACIN YARINTARSU BASU AMFANAR DA KAN SU BA KUMA BASU AMFANI IYAYEN BA BAYAN SUN GIRMA.

DAGA CIKIN MUHIMMANCIN HAKA SHI NE YAWAN SHIRYE-SHIRYEN DA AKE GABATAR DA SU GA YARA A TASHOHIN TALABIJIN DA REDIYO DA JARIDU WANDA SUKE YADA TUNANI MAI YAWA WANDA HAKAN KE GURBATA ABUBUWAN DA YARO KE SURANTAWA DA KUMA MUMMUNAR FAHIMTA AZUKATAN YARA.  DAN HAKA YA ZAMA DOLE YA KASANCE AN FUSKANCI WANNAN MAS`ALAR. ITA TARBIYYAR IMANI AIKI NE DA AKA SHAR`ANTA, KUMA AIKI NE NA RIGAFIN GUJEMA AFKAWAR YARO GA MATSALOLIN TARBIYYA KAFIN YA AFKA MUSU KUMA ZAI YI MAGANIN TA IDAN TA AFKA. KUMA HAKKI NE DAGA CIKIN HAKKOKAN `YA`YA AKAN IYAYE KIYAYE HAKAN. KUMA DALILI NE NA JIN DADIN DUNIYA DA TSIRA A LAHIRA IN ALLAH YA YARDA KUMA DALILI NE DA ZAI BANBANTA MUTANE A RAYUWAR SU.

A KARSHE TARBIYYAR IMANI ITA CE NUTSUWAR RUHI DA AMINTAR DA ZUKATAN YARA DOMIN TANA BADA AMSA AKAN MANYAN TAMBAYOYI NA RAYUWA. BA KOMAI BA CE FACE SHIRIYAR LITTAFIN ALLAH DA HASKAKUWA DA SUNNAR MANZONSA – TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI – WANDA AKA BANBANTA SHI TA HANYAR TSARKAKEKKEN TUSHE, BAYYANANNIYAR HANYA DA SANYA ALLAH A CIKIN MANUFOFI, TARE DA SANIN BUKATUN YARO DA SANIN HAKIKANINSA DA KUMA GASKIYAR ILIMINSA. DON ISA GA KAMALA DA DAIDAITO A CIKIN HALAYEN YARON.

MANUFOFIN

TARBIYYAR IMANI

BABBAR MANUFAR TARBIYYAR IMANI ITA CE TABBATAR DA GASKIYAR BAUTA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI. WANNAN MANUFAR NA BUKATAR TABBATAR DA MANUFOFI DABAN`DABAN MASU YAWA. DAGA CIKIN SU AKWAI:

NA FARKO: DASA INGANTACCIYYAR AKIDA GA `YA`YAN MUSULMI DOMIN A SAMAR DA MUTUM NAGARI DA ZAI BAUTA MA ALLAH AKAN SHIRIYA DA HANGEN NESA.

NA BIYU: MUTUM YA DABI`ANTU DA DABI`U NAGARI ACIKIN AL`UMMAN MUSULMAI YANA MAI KOYI DA MANZON ALLAH ((S.A.W)) ACKIN HAKA. WANDA ALLAH MADAUKAKIN SARKI YAYI SHAIDAR SHI AKAN HAKAN INDA YACE: { KUMA HAKIKA LALLAI KANA KAN HALAYEN KIRKI MANYA} [KALAM:4] DA KUMA AIKI DA FADAN SA ((S.A.W)) (( AN AIKO NI NE DAN IN CIKA DABI`U NAGARI)) [AHMAD 8939]

NA UKU: YADA FAHIMTAR CEWA MUSULMAI AL`UMMA DAYA CE, TA YADDA MUTUM ZAI JI CEWA SHI WANI YANKI NE NA MUSULMAI, YA DAMU DA ALAMURANSU DA DAMUWARSU, YA DANFARU DA `YAN`UWAN SHI SABODA FADAR SA MADAUKAKIN SARKI: { LALLAI MUMINAI `YAN UWA NE} [ HUJURAT: 10]. MANZON ALLAH ((S.A.W)) YA CE: ((MUMINI DA MUMINI KAMAR GINI NE SASHINSA NA KARFAFA SASHI)) [BUKHARY; 6026]. SANNAN KUMA YA SAKE CEWA A WANI HADISIN (( ZA KA GA MUMINAI ACIKIN SOYAYYARSU DA TAUSAYINSU KAMAR JIKI NE, IDAN WATA GABA BATA DA LAFIYA SAI DUKKAN JIKIN YA KAMU DA RASHIN BACCI DA ZAZZABI.)) [BUKHARI: 6011]. DAN HAKA IYAYE DA MASU JIBINTAR LAMARIN YARO SU TABBATAR DA KULLA `YAN`UWANTAKA AKAN IMANI TA GASKIYA TSAKANIN YAYAN MUSULMAI.

NA HUDU: SAMAR DA MUTUM MAI DAIDAITON ZUCIYA DA TAUSAYI WANDA HAKAN ZAI TAIMAKA WAJEN SAMAR DA MUTUM MAI AMFANAR DA  JAMA`AR SHI, WANDA ZAI IYA TSAYUWA DA AIKIN SHI DA AKA DORA MAI WAJEN JAGORANCI DA KUMA GINA KASA, DA KUMA IYA GUDANAR DA JAGORANCI A DORON KASA DA SAUKE NAUYE NAUYEN DA ALLAH YA SANYA SHI SHUGABA AKANSU.

DAGA NAN; BUKATAR FARAWA DA TARBIYYAR IMANI – DA MA’ANARTA TA DAIDAI – YA BAYYANA, WANDA KE CI GABA DA AIKI DON SAMAR DA ƘARFI NA RUHI, HAƁAKA BUNKASAR KAI, ƘARFAFA HANKALI, DA YADA SANIN YA-KAMATA CIKIN KALMOMI DA AYYUKA, SANNAN KUMA SAUƘAƘA WA MUTUM BAYANI DON YIN AYYUKAN DA AKE BUƘATA DON CIMMA BURIN TARBIYYAR HALAYYAR MUTUM DA NA MOTSA JIKI.

الأسس

التربوية

GINSHIKAN

TARBIYYA

AKWAI TARIN GINSHIKAI DA GININ TARBIYYA TA DOGARA DA SU KUMA ZAMU IYA TAKAIKATA SU AKAN GINSHIKAI GUDA BIYU:

1- GINSHIKI NA ILIMI.

2- GINSHIKI NA AIKI.

GINSHIKI NA ILIMI YA KASU GIDA BIYU:

A-ILIMI        B–IMANI.

KASHI NA FARKO: ILIMI SHI MABUDI NE BABBA NA FAHIMTA DA GYARA DABI`U. ALLAH YACE: {KACE ASHE WADANDA SUKA SANI SUNA DAIDAITA DA WADANDA BASU SANI BA? MASU HANKALI NE KAWAI KE YIN TUNATUWA.} [ZUMAR; 9]. MANZON ALLAH ((S.A.W)) YA KWADAITAR DA SAHABBAN SHI ILIMI MAI AMFANI, KUMA YA KOYAR DA SU NEMAN TSARI DAGA ILIMI MARA AMFANI. YANA  CEWA ACIKIN ADDU`AR DA YA KOYAR DA SU (( YA ALLAH INA NEMAN TSARIN KA DAGA ILIMI MARA AMFANI DA ZUCIYAR DA BATA TSORON KA)) [MUSLIM: 2722]

KASHI NA BIYU: SHI NE ABINDA ZAI TABBATA A ZUKATAN YARA  NA DAGA IMANI DA RUKUNAN MUSULUNCI GUDA SHIDA, SHI NE ABINDA YA KE ZAGAYE DA RAYUWA DA MUTUWA. MANZON ALLAH ((S.A.W)) YA KWADAITAR DA DASA INGANTACCEN IMANI KUMA TSAYAYYE A ZUKATAN YARA DA SUKE A ZAMANIN SHI.

GINSHIKI NA AIKI: SHI KUMA YA KASU GIDA UKU:

A- BAUTA      B- AIKI    C- DABI`U

KASHI NA FARKO: BAUTA; TARBIYYA DOLE CE TA KASANCE CIKIN TSARI NA ZAHIRI, HALAYE NA MUSAMMAN, WAƊANDA YARA ZASU IYA GINUWA AKANSU, DON YA FUSKANCI RAYUWARSA DA GASKE KUMA KOYAUSHE YA ZAMA YANA DA ALAƘA DA ALLAHNSA, DON HALAYENSA DA TUNANINSA SU ZAMA MADAIDAITA, HAR MA DA FATANSA DA BURINSA, DOMIN GA ANNABI – (SA.W)- YANA CEWA MU`AZ: WALLAHI, INA KAUNAR KA, KAR KA BAR WANNAN ADDU’AR BAYAN KOWACCE SALLA, KA CE: «YA ALLAH, KA TAIMAKE NI WAJEN BAUTARKA, DA GODE MAKA, DA KUMA KYAUTATA BAUTARKA» (ABU DAWUD (1522)), KUMA YA KOYAR DA SHI CEWA IBADA FALALA CE DAGA ALLAH ZUWA GARE SHI KUMA BA WAI KAWAI KWAZON MUTUM BA NE, DACE NE NA ALLAH .HAKA KUMA KUMA A SANAR DA SHI CEWA IBADA KOYAUSHE TANA BUKATAR TAIMAKON ALLAH, DON HAKA YA SA A ZUCIYARSA CEWA IDAN MUMINI YA BAUTAWA UBANGIJINSA, DOLE NE YA NEMI TAIMAKONSA KUMA YA AMINCE DA SHI A BAUTARSA. DOMIN SHI, ALLAH TSARKI YA TABBATA A GARE SHI, SHI NE WANDA KE DATARWA WAJEN YI MASA BIYAYYA.

KASHI NA BIYU: AIKATAWA: BABU ILIMI IN BABU AIKI, AIKI SHI NE HANYAR DAUKAKA A TSAKANIN BAYI A LAHIRA, WATO SHI NE ABINDA KE SA DARAJAR WANI TAFI TA WANI A RANAR LAHIRA. ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA CE:{ WANDA YA AIKATA ALKHAIRI GWARGWADON KWAYAR ZARRA ZAI GAN SHI, HAKA WANDA YA AIKATA SHARRI GWARGWADON KWAYAR ZARRA ZAI GAN SHI} [ZALZALAT: 7-8]

KASHI NA UKU: DABI`U: ADDININ MUSULUNCI YANA GINA MUTUM NE AKAN HALAYE NAGARI, HATTA MANZON ALLAH ((S.A.W)) YANA GANIN CEWA SAKON DA YAKE ISARWA GABADAYANSA YANA TANA TATTARUWA NE AKAN ABU DAYA WANDA SHI NE KYAWAWAN DABI`U DA TARBIYYANTARWA AKAN SU. DA KAN SHI YAKE CEWA: ((AN AIKO NI NE DAN IN CIKA DABI`U NAGARI.)) [AHMAD: 8939] KUMA YANA ZABURAR DA SAHABBABSA IZUWA GA DABI`U NAGARI, IN DA YAKE CEWA ((MAFI SOYUWA DA KUMA KUSANCIN WAJEN ZAMA AGARE NI A RANAR ALKIYAMA SHI NE WANDA YA FI KU DABI`U NAGARI.)) [TIRMIZI: 2018]. DABI`U NAGARI SU NE ABINDA KE NUNAR DA TARBIYYAR IMANI A BAYYANE.

MISALAI

NA TARBIYYA

BUGA MISALAI A AIKACE NA DAGA CIKIN AL`AMURA MASU MUHIMMANCI DA KE TAIMAKAWA WAJEN TABBATAR DA DOKOKI DA TSARE-TSARE, DAN HAKA GA WASU MISALAI DA ZASU BAYYANA MANA YADDA MANZON ALLAH ((S.A.W)) DA SAHABBAN SHI SUKE GINA YARA AKAN IMANI.

  1.         DAGA IBN ABBAS ((R.A)) YA CE: MANZON ALLAH ((S.A.W)) YA KASANCE YANA NEMA MA HASAN DA HUSAINI TSARI YANA CEWA: ((BABANKU YA KASANCE YANA NEMA MA ISMA`IL DA ISHAK TSARI DASU (DA WANNAN ADDU`AR): A`UZU BI KALIMATILLAHITTAMMATI MIN KULLI SHAITANIN WA HAMMATI WA MIN KULLI AINILLAMMATI)) [BUKHARY: 3371].
  2.         DAGA ABI HURAIRATA ((R.A)) YA CE: MANZON ALLAH ((S.A.W)) YA CE: ((BABU WANI YARO FACE AN HAIFE SHI AKAN TURBA, SAI DAI IYAYEN SHI SU YAHUDANTAR DA SHI KO SU NASARANTAR DA SHI KO SU MAJUSANTAR DA SHI.)) [BUKHARY: 1358].
  3.           DAGA UMAR BIN ABI SALAMATA ((R.A)) YA CE: NA KASANCE INA KAN CINYAR MANZON ALLAH ((S.A.W)) A LOKACIN INA YARO, SAI INA TA YAWO DA HANNUNA ACIKIN KWANO (BAYA CIN GABAN SHI, YACI NAN YA CI CAN) SAI MANZON ALLAH ((S.A.W)) YACE MIN: ((YA KAI YARO, AMBACI ALLAH, KUMA KACI DA HANNUN DAMA, KUMA KA CI ABINDA KE GABANKA)) [BUKHARY: 5376, MUSLIM: 2022].
  4.           DAGA IBN ABBAS ((R.A)) YA CE: ((WATA RANA NA KASANCE A BAYAN MANZON ALLAH ((S.A.W)) SAI YA CE: ((YA KAI YARO, ZAN SANAR DA KAI WASU KALMOMI, KA KIYAYE ALLAH ZAI KIYAYE KA, KA KIYAYE ALLAH ZAKA SAME SHI A GABAN KA, IDAN ZAKA YI ROKO TO KA ROKI ALLAH, KUMA IDAN ZAKA NEMA TAIMAKO TO KA NEMI TAIMAKO WAJEN ALLAH, KUMA KA SANI CEWA LALLAI DA ACE AL`UMMA ZASU TARU DAN SU AMFANAR DA KAI AKAN WANI ABU, TO, BA ZASU AMFANE KA DA KOMAI BA FACE ABINDA ALLAH YA RUBUTA MAKA….)) [TIRMIZIY: 2156]
  5.           DAGA ALHASAN BIN ALIYU ((R.A)) YA CE: MANZON ALLAH ((S.A.W)) YA KOYA MIN WASU KALMOMI DA ZAN FADA ACIKIN KUNUTI NA SALLAR WITIRI: ((ALLAHUMMAH DINI FI MAN HADAITA, WA AFINI FI MAN AFAITA WA TAWALLANI FI MAN TAWALLAIT WA BARIK LI FI MA A`ATAITA WA KINI SHARRA MA KADAIT, INNAKA TAKDI WA LA YUKDA ALAIKA INNAHU LA YAZILLU MAN WALAITA, TABARAKTA RABBANA WA TA`ALAITA.)) [ABU-DAWUD: 1425]
  6.         DAGA ANAS ((R.A)) YA CE: MANZON ALLAH ((S.A.W)) YA CE MIN: (( YA DANA, IDAN ZAKA SHIGA WAJEN IYALAN KA KA YI SALLAMA, DOMIN HAKAN ZAI KASANCE ALBARKA A GAREKA TARE DA IYALAN KA)) [TIRMIZI: 2698]
  7.         DAGA JUNDUB AL-BAJALIYYU ((R.A)) YA CE: MUN KASANCE TARE DA MANZON ALLAH ((S.A.W)) A LOKACIN MUNA YARA, SAI MUKA KOYI IMANI KAFIN MU KOYI ALKUR`ANI, SANNAN SAI MUKA ZO MUKA KOYI ALKUR`ANI SAI MUKA KARA IMANI DA SHI (SABODA QUR`ANI) [IBN MAJAH (61)]
  8.         UMMU SULAIM WATO RUNAISA`U MAHAIFIYAR ANAS BN MALIK (R.A) TA MUSULUNTA A LOKACIN ANAS YANA YARO BA`A YAYE SHI BA, SAI TA RINKA LAKKANA MA ANAS TANA CE MAI KACE:  LAI`ILAHA ILLALLAH, KACE: ASH`HADU ANNA MUHAMMAN RASULULLAHI. SAI ANAS YA FADI HAKAN
  9.         DAGA IBRAHIM ATTAIMIYYU ALLAH YA YI MASA RAHAMA, YA CE: SUN KASANCE SUNA SON YA ZAMA FARKON ABINDA YARO ZAI FARA FADA SHI NE LA`ILAHA ILLALLAH SAU BAKWAI, SAI YA KASANCE SHI NE FARKON ABINDA YA FARA MAGANA DA SHI.
'Fel a tetejéhez' gomb