TAMBAYOYIN DA KED A ALAKA DA KADDARA

ME AKE NUFI DA HUKUNCI DA KUMA KADDARA?

HUKUNCIN ALLAH DA KUMA KADDARA RUKUNI NE DAGA CIKIN RUKUNAN IMANI, ALLAH MADAUKAKI YA CE: (KUMA YA HALICCI KOMAI, KUMA YA KADDARA SHI KADDARAWA) (AL-FURQAN: 2) KUMA MA’ANAR HUKUNCIN ALLAH DA KADDARARSA SHI NE: ALLAH YA SAN YAWAN ABUBUWA KAFIN SAMUWARSU, YA KUMA RUBUTA SHI, DA GANIN DAMARSA, YA KUMA HALICCE SU DA ITA KADDARAR.

TA YAYA ALLAH YAKE SANIN ABIN DA ZAI FARU TUN KAFIN YA FARU?

ZA A IYA CE MASA DA MISALI MAI SAUƘIN FAHIMTA: CEWA WANI MAI KERA ABIN WASA DA YAKE WASA YA SAN ABIN DA WASAN ZAI HAIFAR TUN KAFIN YA YI SHI; DOMIN SHI NE WANDA YA KIRKIRE SHI KUMA YA KAYYADE AIKIN KOWANE ABU KARAMI DA BABBA A CIKIN WANNAN WASAN, DOMIN YA SAN CIKAKKEN BAYANI GAME DA WANNAN WASAN DA WURAREN DA ZAI IYA MOTSAWA, KUMA ALLAH SHI NE WANDA YA HALICCI WANNAN MUTUMIN DA YAKE DA IKON WADANNAN ABUBUWA, DOMIN ALLAH SHI NE MAFI GIRMAN IYAWA, MAFI YALWAR ILIMI KUMA MAFI KAMMALA, ALLAH YA KEWAYE DUK ABINDA YA HALITTA DA ILIMINSA TUN KAFIN YA HALICCE SHI, DA YAYIN HALITTAR SA, DA KUMA BAYAN YA HALICCE SHI, TO ALLAH SHI NE WANDA YA HALICCI MUTUM, DA  LOKACI DA WURI, DOMIN ALLAH YA SAN ABIN DA YA KASANCE, ABIN DA YAKE KASANCEWA DA ABIN DA ZAI KASANCE BAYAN HAKAN.

SHIN AN TILASTA MANA NE? SHIN MUTUM YANA DA ZAƁI A CIKIN AYYUKANSA?

AN TILASTA WA MUTUM CIKIN WASU ABUBUWA, KUMA AN BASHI ZAƁI A CIKIN WASU ABUBUWA, SABODA AN TILASTA MANA HAIHUWA DA MUTUWA, DA KUMA TSAWON RAYUWA, KUMA BAMU DA ZABI AKAN SUWANENE IYAYENMU DA KAKANNINMU, KUMA AN TILASTA MANA SADA ZUMUNCI DA DANGINMU, YAYIN DA AKA BAMU ZABIN MUYI SALLA KO KAR MUYI, IMANI KO KAFIRCI, KUMA DUK DA WANNAN ZABIN; NUFINMU YANA CIKIN NUFIN ALLAH; DA ALLAH MADAUKAKIN SARKI YANA SO YA HANA MU ZABI, DA YA YI, KUMA DA YANA SON HANA MU KIN YIN WANI ABU, DA YA YI HAKAN, AMMA YA HUKUNTA CEWA MUTUM YA YI ZABI SANNAN KUMA ZA A YI MASA HISABI KAN WANNAN ZABIN, KUMA WANNAN ITA CE MA’ANAR FADINSA MADAUKAKI: (KUMA BA ZA KU SO BA, FACE ABINDA  ALLAH UBANGIJIN TALIKAI YA GA DAMA,) (AT-TAKWIR: 29), KUMA ANA IYA BAYANIN BATUN TILAS DA KUMA ZABI A AIKACE: DON HAKA MAI BADA TARBIYYAR SAI YA KAWO KOFIN GILASHI YA CE WA YARON: SHIN ZA KA IYA JEFAR DA WANNAN ƘOƘON A ƘASA KA FASA SHI? YARON ZAI AMSA: TABBAS: ZAN IYA. MAI BADA TARBIYYAR  ZAI FARA YANA MAI TAMBAYA: ME YA HANA KA? YARO ZAI BA DA AMSA: WANNAN BA DAIDAI BA NE KUMA BAI KAMATA A YI HAKA BA, DON HAKA MALAM SAI YA YI TSOKACI YANA MAI CEWA: ALLAH – MADAUKAKI – YA SANI TUN A DA CEWA BA ZA KA FASA WANNAN ƘOƘON BA. SABODA KAI YARO NE NAGARI, KUMA YA SAN – HAR ABADA – CEWA YARON BANZA ZAI FASA WANNAN KOFIN, SHIN WANI NE YA HANA KA JEFAR DA WANNAN KOFIN A ƘASA? KO KUWA WANI NE YA TILASTAWA FITINANNEN YARON YA FASA KOFIN? WANNAN SHI NE YADDA SHIRIYA DA BATA SUKE, SANNAN SAI A CE MASA: MUTUM BAI SAN ABIN DA ALLAH YA RUBUTA A KANSA BA, KUMA BA A BUKATAR KA SAN ABIN DA AKA RUBUTA, AMMA ANA BUKATAR KA YI IMANI DA CEWA SANIN ALLAH SHI NE CIKAKKE KUMA KAMMALALLE, DAGA CIKI HARDA  RUBUTUN KADDARA, KUMA KAI KE DA ALHAKIN NUFINKA DA KUMA GWARGWADON  BIYAYYARKA DA UMARNI DA BARIN HARAMTATTUN ABABE, WANNAN NA KARKASHIN DAMARKA DA NUFINKA.

ME YASA YA SHIRYAR DA WASU MUTANEN BAN DA WASU?

ALLAH MADAUKAKI YA SHIRYAR DA DUKKAN MUTANE SABODA FADINSA – MADAUKAKI -: (KUMA MUN SHIRYAR ZUWA HANYOYI BIYU) (AL-BALAD: 10), KUMA MA’ANAR WANNAN SHIRIYAR ITA CE: TSAKANIN SHIRIYA NE DAKE BAYYANE GA MUTANE KUMA YA YI MU SU BAYANI GAME DA MADAIDAICIYAR HANYA, DON GASKIYA TA BAYYANA KUMA KARYA TA BAYYANA, KUMA ALLAH YA BAR ‘YANCI GA MUTANE. AKWAI WADANDA SUKA ZABI HANYA MADAIDAICIYA KUMA AKWAI WADANDA SUKA ZABI HANYAR DA BA DAIDAI BA.

IDAN HAR ALLAH TUN ASALI YA KADDARA CEWA A CIKINMU ZA A SAMI MASU ZUNUBI DA ƁATA TO ME YASA ZAI HUKUNTA MU?

WANNAN ILIMIN ILIMI NE NA ALLAH, KUMA DAN ADAM BASHI DA WANI ILMI GAME DASHI, KUMA ABINDA SUKE DASHI KAWAI ZATO NE, DA JAHILCI, SABILI DA HAKA MUTUM YANA DA HISABI AKAN ABINDA YA AIKATA A RAYUWARSA TA DUNIYA, KUMA BABU YADDA BAWA ZAI SAN GAIBI WANDA ALLAH YA SANI HAR SAI YA AIWATAR DA AIKIN SA YA GAMA SANNAN YA SAN SHI. DON HAKA KADDARAR DA AKA RUBUTA BA HUJJA BACE AKAN ABIN DA YA GABATA BA WAI ABINDA ZAI ZO A NAN GABA BA. HAKA KUMA, SAI A CE MASA: ALLAH YA RUBUTA MUKA AL’AMURAN DUNIYA … DON HAKA ME YASA KAKE AIKATA ABINDA ZAI AMFANE KA KUMA KA BAR ABINDA ZAI CUTAR DA KAI?! ZAI IYA BA SHI MISALI YA CE: IDAN MUTUM YANA SON TAFIYA ZUWA WATA ƘASA, KUMA WANNAN ƘASAR TANA DA HANYOYI BIYU, ƊAYANSU TANA DA AMINCI, ƊAYAR KUMA BA TA DA AMINCI, TO WACCE DAGA CIKINSU ZAI ZAƁA? TABBAS, ZAI ZABI HANYA TA FARKO, TO HAKA ABIN YAKE WAJEN TAFIYA ZUWA LAHIRA, MUTUM YANA ZABAR HANYA MADAIDAICIYA DON ISA ALJANNA – WACCE ITACE BIN UMARNI DA NISANTAR HANI – DA ACE KUWA KADDARA HUJJA CE GA WANI DA BAMU IYA KAMA MASU LAIFI BA; SABODA ZA SUN BADA HANZARI DA KADDARA GAME DA AYYUKANSU, SABODA HAKA; WAJIBI NE MUTUM YA YARDA KUMA YA MIKA WUYA GA ALLAH MADAUKAKI, DOMIN ALLAH (BA A TAMBAYAR SA GAME DA ABIN DA YAKE AIKATAWA SU KUMA (MUTANE DA ALJANU) ANA TAMBAYARSU) (AL-ANBIYA‘: 23), DON HAKA HALITTA HALITTARSA CE KUMA AL’AMARI AL`AMARINSA NE – TSARKI YA TABBATA GA SHI.

ME YASA ALLAH YA HALICCE MU? MENENE ASALIN HALITTA? ME YASA AKA HALICCI DABBA

ALLAH MADAUKAKI YA CE: (KUMA BAN HALICCI ALJANNU DA MUTANE BA SAI DON SU BAUTA MIN) (AZ-ZARIYAT: 56). AN HALICCE MU NE DON WATA MANUFA WACCE ZA TA AMFANE MU – WACCE ITA CE BAUTA MASA, TSARKI YA TABBATA A GARE SHI, DA KUMA SAMUN SAKAMAKO A LAHIRA GWARGWADON AYYUKANMU. ALJANNA TA MASU KYAUTATAWA CE KUMA ITA WUTA TA MASU MUNANAWA CE, KUMA WANNAN DUNIYA GABA DAYANTA ALLAH MADAUKAKIN SARKI NE YA HALICCE TA, DOMIN AN YI TA NE DA DAIDAITO DA ILIMI. YA HALICCI SAMMAI DA KASSAI YA KUMA YADA TAURARI A CIKI, AN HALICCI TAURARI DON SU ZAMA ALAMU DA IZINA DA KWALLIYA, AN HALICCI RANA DOMIN BAMU DUMI DA ZAFI DA KUMA BADA GUDUMMAWA GA TSIROWAR TSIRE-TSIRE DA KAWAR DA KWAYOYIN CUTA, AN HALICCI DABBOBI DOMIN MUTUM YA CI DA SU KUMA DAUKE SU ALLAH MADAUKAKI YA CE: «KUMA DAWAKAI, DA ALFADARAI, DA JAKUNA, DOMIN KU HAU SU NE DA KUMA ADO , KUMA YANA HALITTAR ABIN DA BA KU SANI BA.” (AN-NAHL: 8). SHIRYA KASA DOMIN ZAMA DA KUMA KIRKIRAR WADANNAN ABUBUWA KAFIN HALITTAR MUTUM. LAMARI NE NA GIRMAMAWA DA ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA YI WA MUTUM, BUGU DA KARI KAN CEWA DUKKAN WADANNAN ABUBUWA SUNA YABON ALLAH MADAUKAKIN SARKI, ITA KANTA WANNAN BAUTA CE A KANSU. . (BABU WANI ABU FACE YANA TASBIHI DA GODIYA A GARE SHI, AMMA KU BAKWA FAHIMTAR TASBIHINSU, DOMIN SHI YA KASANCE MAI HAKURI NE KUMA MAI GAFARA) (AL-ISRAA: 44).

SHIN ALLAH ZAI BINCIKI WADANDA MANZO BAI ZO MUSU BA?

SUNA ƘARƘASHIN HISABI DA LISSAFI. SABODA ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA BA SU HANKALI, DON HAKA NE ALLAH ZAI JARRABE SU RANAR TASHIN KIYAMA KUMA YA UMARCE SU. IDAN SUKA YI BIYAYYA, ZASU SHIGA ALJANNA, IDAN KUMA BASU YI BIYAYYA BA, ZASU SHIGA WUTA.

ME YASA AKE SAMUN SHARRI?

WANNAN DUNIYA GIDAN JARRABAWA NE, KUMA ITA KAMAR FARKON BABIN LABARI NE WANDA YAKE DA FASALAI GUDA BIYU, ITA KUMA LAHIRA ITA CE GIDAN SAKAMAKO DA HISABI, DA KUMA FITAR DA HAKKI DAGA AZZALUMAI ZUWA GA WADANDA AKA ZALUNTA, KUMA ITA CE A MATSAYIN BABI NA BIYU NA LABARIN, KUMA DON WANNAN; KASANCEWAR FAJIRAI DA RASHIN AZABTAR DASU A WANNAN DUNIYA JARRABAWA CE A GARE SU, KUMA WANNAN BA YANA NUFIN KARSHEN LAMARIN BANE, A’A YA ZAMA DOLE KOWA YA TASHI RANAR TASHIN KIYAMA TA YADDA KOWANE MUTUM ZAI SAMI LADAN AYYUKANSA. ALLAH MADAUKAKI YA CE: «WANDA YA YI AIKI KODA NAUYIN KWAYAR ZARRA NE ZAI GAN SHI (7) KUMA WANDA YA YI AIKI NA SHARRI KODA NAUYIN KWAYAR ZARRA NE ZAI GAN SHI.» (ZALZALAH: 7-8).

ME YASA ALLAH YA HALICCI MASU SHARRI?

ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA HALICCI MUTANE KUMA YA BASU ‘YANCIN ZABAR AIKATA ALHERI KO SHARRI, DOMIN ZAKA IYA ZAMA MAI LADABI, KUMA ZAKA IYA NUNA RASHIN LADABI, AMMA DOLE NE KA KARBI SAKAMAKO, KUMA WANNAN WATA NI’IMA CE DAGA ALLAH DA HIKIMA. MIYAGU ZA SU IYA ZAMA MASU KIRKI KUMA AIKINMU SHI NE MU TAIMAKA MUSU A KAN HAKAN, AMMA IDAN SUKA ƘI KUMA SUKA NACE KAN MUGUNTA; HAKKINMU SHI NE MU HANA SHARRINSU ISA GA MUTANE. DON ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA SO MU KUMA YA BAMU LADA, KUMA ALLAH MADAUKAKIN SARKI SHI NE MAHALICCIN KOMAI A WANNAN RAYUWAR, KUMA WANNAN RAYUWAR GIDAN FITINA CE DA JARABAWA, ALLAH  MADAUKAKI YACE: (WANDA YA HALICCI MUTUWA DA RAYUWA DON YA JARRABA KU WANENE DAGA CIKINKU YA FI KYAN AIKI) (ALMULK: 2), KUMA NA DAGA JARRABAWA: SAMUWAR SHARRI A TSAKANIN SHEDANU DA FANDARARRU DAGA CIKIN MUTANE.

ME YASA WASU MUTANE AKE HAIFAR SU DA MUNI KO NAKASA?

ALLAH YANA JARRABAR  WASU DA RASHI DA CUTA. DON SU YI HAKURI SU YAWAITA AYYUKANSU NA ALHERI, KUMA DON ALLAH – MADAUKAKI  YA TUNATAR DA MU NI’IMAR DA YA YI MANA TA SAMAR DA MAFI YAWANMU LAFIYA, DON HAKA MUNA GODE MASA A KAN HAKA, KUMA DON TUNATAR DA MU RAUNINMU TA FUSKAR IKONSA, DON KADA MU YI GIRMAN KAI, SAI DAI MU YI TAWALI’U DA TAIMAKON JUNA, KUMA BAYAN RANAR  SAKAMAKO: WAƊANDA SUKA AIKATA NAGARTA ZA SU YI RAYUWA TA HAR ABADA, CIKIN KOSHIN LAFIYA AALJANNATAI NA NI’IMA – INSHA ALLAH.

ME YASA AKE SAMUN MASU WADATA DA MATALAUTA? KUMA :ME YASA WASU DAGA CIKIN MUTANEN BANZA SUKE ZAUNE A FADOJI KUMA WASU DAGA CIKIN MUTANEN KIRKI SUNA ZAUNE A BUKKOKI?

DUK WANNAN A RAYUWAR TA DUNIYA DAGA ALLAH NE, TSARKI YA TABBATA A GARE SHI, KUMA ALLAH YANA JARRABAR BAYINSA, WANI LOKACI KUMA YANA AZURTA MUTUMIN KIRKI. DON GWADA KARAMCINSA GA WASU, WANI LOKACIN KUMA YANA HANA SHI WADATA; DON YA GWADA HAƘURINSA JURIYARSA WAJEN GANIN BA ZAI YI SATA BA KO YA KULLACI WANI, DUK LOKACIN DA MUTUMIN KIRKI YA RAYU A WANNAN RAYUWAR NA ƊAN LOKACI YA YI HAƘURI; TO LADANSA MAI GIRMA NE A RANAR LAHIRA, AMMA MUTUMIN DA AKA BASHI BASHI ARZIKI KUMA BAI BA WASU BA KUMA YA WULAKANTA SU. ZA’AYI MASA AZABA ARANAR ALQIYAMAH. DOMIN BAI YABA DA ALHERIN ALLAH BA.

KUMA MUNA IYA CE MASA: HAKIKA ALLAH – TSARKI YA TABBATA A GARE SHI – YA HALICCI MUTANE MASU DARAJOJI DABAN-DABAN – WASU DAGA CIKINSU TALAKAWA WASU KUMA ATTAJIRAI. DON MASU ARZIKI SU TAUSAYA WA TALAKAWA, KUMA MASU KARFI SU TAIMAKI MASU RAUNI. HIKIMAR ALLAH TA HUKUNTA CEWA MUTANE SU ZAMA DABAN A CIKIN KOMAI, HARSUNAN SU SUN BAMBANTA KUMA LAUNUKAN SU SUNA DA YAWA. SUN KASANCE A LAUNIN FATA DA YANAYI MABANBANTA NE, MASU KUZARI DA MALALATA, MASU FIFITA WASU DA MASU SON KAI, MASU KARIMCI DA MAROWATA. WADATA JARRABAWA CE, TALAUCI MA JARRABAWA CE, ANA JARRABAR ATTAJIRAI:SHIN ZAI CIYAR? SHIN ZAI BA DA SHIN ZAI YI ZAKKA? SHIN ZAI YI KARAMCI?  ZAI BADA SADAKA? TALAKAWA ZA A JARRABAWA SU: SHIN ZAI YI HAƘURI? SHIN ZAI SHA WAHALA? SHIN ZAI NEMI HANYOYIN NEMAN ARZIKIN DUNIYA? SHIN ZAI BADA CIN HANCI? ZAI YI SATA? DUK WANNAN JARRABAWA CE, AMMA AKWAI GARANTI GA DUKKAN BANGARORIN BIYU: CEWA RAYUWA TANA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI, KUMA DUKIYA DA TALAUCI BA SU HANA SHIGA ALJANNA DA WUTA, DON HAKA ANA CAJIN KOWA GWARGWADON ABIN DA YA MALLAKA, DA ACE KUWA MUTANE AJI DAYA NE MASU KUDI. DA BASU YIWA JUNA HIDIMA BA, DA KUMA BASU BUKACI JUNA BA, ALLAH MADAUKAKI YA CE: (DON WASU SASHEN SU DAUKI WASU SASHEN A MATSAYIN ABIN IZGILI) (AL-ZUKHRUF: 32), MA’ANA, SU YI WA JUNA IZGILI, KUMA DA WANNAN NE YANAYIN RAYUWAR YAKE JUYAWA, AMMA A YANAYIN AJI DAYA, TO RAYUWA ZATA TSAYA.

ME YASA MUKE RASHIN LAFIYA? ME YASA MUTANE KE FADAWA MASIFA?

ALLAH YANA JARRABAR KOWANE MUTUM; SHIN ZAI YI HAƘURI KO KUWA ZAI YI FUSHI? KUMA ALLAH MADAUKAKIN SARKI ZAI SAKA WA WADANDA SUKA YI HAKURI DA LADA MAI YAWA, KUMA MUMINI ZAI YI FARIN CIKI DA SHI A RANAR TASHIN KIYAMA, CUTA, DA BALA’I, DA RADADI SU NA DAGA KADDARAR ALLAH DA SU YAKE DAUKAKA DARAJOJI DA TSARKAKE ZUKATANMU DA DABI’UNMU DAGA GIRMAN KAI, JIJI-DA-KAI DA GIRMAN KAI, KUMA A CIKINSU MUMINI YAKAN KUSANCI UBANGIJINSA DA ADDU’A DA HAƘURI, DON HAKA IMANINSA DA KYAWAWAN AYYUKANSA SU ƘARU, KUMA UBANGIJINSA YA SO SHI, KUMA MUTUM YANA SANIN ƘIMAR LAFIYA DA KUMA NI’IMA, KUMA ZA MU IYA BA SHI MISALI DA MOTA, DON HAKA SAI MU TAMBAYE SHI: ME YA SA AKA ƘIRƘIRA MOTAR? DON TA YI TAFIYA, KO BA HAKA BA? DON HAKA; TO ME  YASA MASANA’ANTAR  MOTAR TAKE MATA  BIRKI? SHIN WANNAN BAI CI KARO DA MANUFAR YIN MOTAR BA NA TA DINGA TAFIYA? YIN AMFANI DA BIRKI YA ZAMA DOLE DOMIN KARE LAFIYARTA, AN SANYA MOTAR GUDU, SAI BIRKI YA TSAYAR DA ITA A LOKACIN DA YA DACE DON KAR A HALAKA MAI ITA, KAMAR YADDA ALLAH – MADAUKAKI – YA HALICCE MU DON YA FARANTA MANA A CIKIN BAUTARSA DA NI’IMOMINSA A KANMU, DON HAKA ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA HALICCI BALA’I DON TUNATAR DA MUTUMIN MAI SHAGALA GAME DA BABBAN AIKIN DA AKA HALICCE SHI DOMIN SHI, DON HAKA YA DAINA SHAGALARSA DA SAKACINSA, YA TINA UBANGIJINSA, KUMA YA DINGA NEMAN GAFARA DA HAƘURI DA NEMAN LADA.

SHIN ALLAH NE YA HALICCI DABBOBI DA KWARI MASU CUTARWA?

ALLAH SHI NE MAHALICCIN KOMAI, KUMA SHINE UBANGIJIN KOMAI, DAN HAKA YA HALICCI WADANNAN HALITTU, DAN HAKA YA HALICCE SU DA HIKIMARSA – KUMA -. DOMIN SHI MAI HIKIMA NE, MAI ILIMI, WANDA YA SAN WASU AL’AMURAN NASU DA BA MU SANI BA. DOMIN ILIMINMU DA ILIMIN DA ALLAH YA HORE MANA KADAN NE DANGANE DA ILIMI DA HIKIMAR ALLAH, SABODA HAKA; ALLAH MADAUKAKI YANA CEWA: (KUMA BA A BA KU ILIMI BA FACE KADAN) (AL-ISRAA: 85) BA ZA MU IYA SANIN DUK HIKIMOMIN DA YASA ALLAH YA HALICCI WADANNAN DABBOBI BA, DAGA CIKIN HIKIMAR HALITTAR IRIN WADANNAN HALITTU: BAYYANA KYAN HALITTAR ALLAH A CIKIN HALITTUNSA DA GUDANARWARSA – TSARKI YA TABBATA GA ALLAH. KUMA MAFI YAWA – A CIKIN HALITTUNSA, DUK DA YAWANSU, YANA RAYA SU DUKA, HAKA KUMA, ALLAH DAUKAKA TA TABBATA A GARE SHI, YANA JARRABAR BAYI DA SU KUMA YANA SAKA WA WAƊANDA SUKE CUTU DAGA SU KUMA SUNA NUNA ƘARFIN HALIN MUTUM WAJEN KASHE SU, HAKA NAN KUMA YANA NUNA RAUNI DA DA JIN ZAFI NA MUTUM DA RASHIN LAFIYARSA SABODA WATA HALITTA DA TAKE ƘASA DA SHI A CIKIN HALITTA, KUMA YA BAYYANA TA HANYAR LIKITANCI DA GWAJE-GWAJE: CEWA DA YAWA DAGA CIKIN MAGUNGUNA MASU FA’IDA ANA FITAR DA SU NE DAGA GUBAR MACIZAI DA MAKAMANTANSU, KAMAR YADDA MACIJIN YAKE CIN BERAYEN GONAR DA SUKE LALATA AMFANIN GONA, SANNAN KUMA DA YAWA DAGA CIKIN WADANNAN DABBOBIN MASU CUTARWA ABINCI NE GA WASU DABBOBI MASU FA’IDA, WANDA YAKE SAMAR DA DAIDAITAR YANAYI A DABI’A DA MUHALLIN DA ALLAH YA KYAUTATA HALITTARSA.

ME YASA A KULLUM DOLE SAI NA YI SALLA SAU BIYAR A DARE DA RANA?

IBADUN DA ALLAH YA DORA AKANMU WATA HANYA CE TA TSARKAKE RUHIN MUMINI DA INGANTA RUHINSA, DUK DA  KANKANTAR KOKARIN DA YAKE YI, BAN DA ALHERIN DA YAKE SAMU DAGA GARE TA, KUMA TUNDA SALLA TA KUNSHI KARATU, ZIKIRI DA ROKO, KUMA TA HADA DUKKAN BANGARORIN BAUTA A MAFI CIKAR HANYA. ITA KADAI TA FI DUKKAN WANI KARATU, ZIKIRI, DA ADDU’A; DON TA TATTARA SU DUKA TARE DA SANYA SAURAN GABBAI IBADA.

MUMINAI SUNA YIN FARIN CIKI DA SALLA; SABODA SUNA TARE DA ALLAH – TSARKI YA TABBATA A GARE SHI A CIKIN TA -, SUNA ROKON SHI DA DUK ABIN DA SUKE SO KUMA YANA AMSA MUSU, KUMA MUNA YIN SALLA; DOMIN ALLAH – MADAUKAKI – YA UMURCE MU DA YIN HAKA, KUMA A KODA YAUSHE MUNA SON YIN ABIN DA ALLAH YA UMURCE MU DA AIKATAWA, DON HAKA MUKE BAUTA WA ALLAH. DOMIN SHI NE MAHALICCINMU KUMA MAI AZURTA MU, KUMA SABODA YA CANCANCI A BAUTA MASA SABODA YAWAN BAIWAR DA YA YI MANA, ALLAH MADAUKAKI YA CE: (KUMA IDAN KUKA KIRGA NI’IMOMIN ALLAH, BA ZA KU IYA LISSAFE SU BA) (AN-NAHL: 18) . HAKIKAWANNAN BAUTAR ITA CE KE NUNA KAUNARMU DA GODIYARMU GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI DA KUMA TABBATAR DA BUKATARMU IZUWA GARE SHI, DON YA KIYAYE LAFIYARMU DA TAIMAKA MANA ZUWA GA ALHERI DA KIYAYE SHARRI DAGA GARE MU, KUMA ALLAH BA YA BUKATAR HAKAN. SABODA SHI MAWADACI NE DAGA GARE MU DA KUMA AYYUKAN MU KUMA BASA AMFANAR SA, KASANCEWAR IBADA UMARNI NE DAGA ALLAH WANDA YAKE SO MU BAUTA MASA TA YADDA ANNABIN SA MUHAMMAD ((S.A.W)) YA ZO DA ITA. HAKA NAN, WADANNAN IBADUN WATA HANYA CE A GAREMU DON SAMUN LADA MAI GIRMA WADANDA SUKE SABABIN SHIGA ALJANNA, HIKIMAR ALLAH TA HUKUNTA CEWA BA ZAA  BA MUTUM LADA BA SAI DA AIKI, SABODA HAKA: ALJANNA KAYAN  ALLAH NE MAI TSADA, KUMA TANA BUƘATAR FARASHI MAI GIRMA – WANDA SHI NE BIYAYYA.

NA TA YIN ADDU’A A CIKIN SALLATA DON IN GIRMA DA SAURI, AMMA ALLAH BAI  AMSA MIN BA?

ADDU’A TANA DA LADUBBA WADANDA DOLE NE A KIYAYE SU, KUMA DAGA CIKIN LADUBBAN ADDU’AR AKWAI CEWA MAI ROKO YA GIRMAMA DOKOKI DA KA`IDOJIN DA ALLAH MADAUKAKI YA SANYA DOMIN TAFIYAR DA WANNAN DUNIYA, KUMA MUNA ROKON ALLAH ALHALI SHI, TSARKI YA TABBATA A GARE SHI YANA YIN ABINDA ZAI ZAMA ALHERIN NE A GARE MU. KANA TAMBAYAR MAHAIFINKU KA YI WASA DA KEKE A HANYA, AMMA YA ƘI; SABODA YANA KAUNAR KA KUMA YAYI IMANI CEWA RASHIN BIYAN BUKATAR KA SHI NE MAFI ALHERI A GARE KA, KUMA DAGA KARIMCIN ALLAH MADAUKAKIN SARKI CEWA ADDU`AR MU TANA DA HALAYE UKU; NA FARKO: ALLAH YA AMSA MANA YA KUMA CIKA MANA ITA, NA BIYU KUMA: ALLAH YA DAUKE WATA MUSIFA DA WANI MUMMUNAN ABU DA ZAI SAME MU, NA UKU: ALLAH ZAI ADANA MANA ITA HAR SAI RANAR TASHIN KIYAMA. DON CIMMA ABIN DA YA FI TA A CIKIN ALJANNA.

ME YASA BA ZAN IYA ZAMA KYAKKYAWA KAMAR KAWATA BA?

DOMIN ALLAH –MAI GIRMA DA DAUKAKA – YA HALICCI KOWA DA IRIN SURAR DA TAKE BAMBANCE SHI DA WANI, DON HAKA DUKKAN HALITTUN ALLAH SUNA DA KYAU, KAMAR YADDA ALLAH MADAUKAKI YAKE CEWA: (MUN HALICCI DAN ADAM A MAFI KYAWUN YANAYIN TSAIWA) (AL-TIN 4) . KUMA KOWANE MUTUM ANA RARRABE SHI DA TA BANGAREN  IRIN HALITTARSA, WANDA ALLAH YA HALICCE SHI DA KYAWU DOLE NE YA KARA GODEWA ALLAH, WANDA KUWA BA HAKA BA DOLE NE YA YADDA KUMA YA KARBA, KUMA DUK WANDA YAYI GODIYA KUMA YA YI HAKURI YANA DA DARAJA DA LADA MAI GIRMA.

IDAN ALLAH YANA SON MU TO ME YASA MIYAGUN

ABUBUWA SUKE SAMUN MU?

ALLAH YANA JARRABAR MU; DON RARRABE MAI KYAUTATAWA DAGA MAI MUNANAWA, KUMA ALLAH YANA IYA JARRABAR MUTUM DON YA NEMI MAFAKA A GARE SHI KUMA YA KUSANCI ALLAH A KOYAUSHE, DON HAKA JARRABAWA GWAJI NE DAGA ALLAH GA ƘAUNATATTU BAYINSA. DON GWADA SU DA HAƁAKA MATSAYIN SU: DON SU ZAMA ABIN KOYI GA WASUNSU; DON WASU SU YI HAQURI SU YI KOYI DA SU. SHI YASA ANNABI ((S.A.W)) YA CE: «WADANDA SUKA FI SAURAN MUTANE TSANANIN SHIGA JARRABAWA SU NE ANNABAWA, SAI WADANDA KE KASA DA SU  SAI WADANDA KE KASA DA SU.» (SAHIH AL -JAMI` (992)). SANNAN ANA JARRABAR MUTUM NE GWARGWADON ADDININSA, IDAN ADDININSA NA DA KARFI SAI JARRABAWARSA TA YI YAWA, SHI YA SA ALLAH YAKEWA ANNABAWA BABBAR JARRABAWA, AN KASHE WASU DAGA CIKINSU, WASU DAGA CIKINSU AN CUTAR DA SU, WASU KUMA DAGA CIKINSU SUN KAMU DA RASHIN LAFIYA MAI TSANANI KUMA MAI TSAWO KAMAR ANNABI AYUBA – AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI – KUMA ANNABINMU – YARDAR ALLAH TA TABBATA A GARE SHI – YA SHA WAHALA MAI GIRMA A MAKKA DA MADINA, KUMA DUK DA  WANNAN HAKURIN –AN ANNABI TSIRA DA AMINCI SU TABBATA A GARE SHI – BABBAN ABIN NUFI SHI NE: CUTARWA TANA FARUWA NE GA MA’ABUTA IMANI DA TSORON GWARGWADON TSORON ALLAHNSU. DA IMANINSU, TO YA ZAMA DOLE A YA TABBATA  A ZUCIYAR YARON: CEWA ALLAH – MADAUKAKI – YANA AIKATA ABIN DA YA GA DAMA KUMA YANA ZARTAR DA ABIN DA YAKE SO, KUMA BA A TAMBAYAR ALLAH MAI ALBARKA DA DAUKAKA GAME DA ABIN DA YAKE AIKATAWA. DOMIN SHI NEMAFI KYAUTATAWAR MASU MULKI.

'Fel a tetejéhez' gomb