TAMBAYOYI DA SUKA SHAFI LITTATTAFAI

WADANNE NE LITTATTAFAN DA ALLAH YA SAUKAR?

LITTATTAFAI NE WADANDA ALLAH YA SAUKAR DA SU GA MANZANNIN SHI, TSIRA DA AMINCI SU KARA TABBATA A GARE SU. DON SU ISAR DA SAƘO DA HUKUNCE-HUKUNCEN DOKOKI, DON SHIRIYA NE GA HALITTA KUMA RAHAMA CE A GARE SU. DAN SU RABAUTA A DUNIYA DA LAHIRA, WADANDA LABARI YA SAME MU CEWA: ALLAH YA SAUKARWA IBRAHIM – AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI – TAKADDU, DA KUMA ANNABI DAUDA – AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI AN BASHI – ZABURA, KUMA ANNABI MUSA – AMINCI YA TABBATA A GARE SHI AN BASHI – ATTAURA, ANNABI ISA – AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI – KUMA AN BASHI -INJILA, DA KUMA ANNABINMU MUHAMMAD – ALLAH YA YI TSIRA A GARE SHI KUMA AN BASHI – ALQURANI.

ME YASA MUKE BUKATAR ALQURANI? KUMA ME YASA KUR’ANI YA KASANCE MU’UJIZA TA HAR ABADA?

IDAN INJI MAI SAUƘI DA ƊAN ADAM YA KERA YANA BUƘATAR LITTAFIN JAGORA WANDA KE KOYA MANA YADDA ZA MU YI AMFANI DA SHI DA KYAU; TO MUTUM – WANDA HALITTAR ALLAH NE – YANA BUKATAR LITTAFIN SHIRIYA DA SHIRYARWA WANDA KE KARANTAR DA SHI HANYAR CIN NASARA, CI GABA DA ADALCI A DUNIYA DA LAHIRA. ALLAH MADAUKAKI YA CE: (SHIN BAI SAN WANDA YA YI HALITTA BA, SHI MAI TAUSASAWA NE KUMA MASANI) (MALIK: 14). KASANCEWAR ALKUR`ANI MU`UJIZA CE  SABODA ANNABI MUHAMMAD – TSIRA DA AMINCI SU TABBATA A GARE SHI – SHI NE KARSHEN ANNABAWA, SABODA HAKA DOLE NE MU’UJIZARSA TA CI GABA DA KASANCE HAR ABADA. SABODA BABU WANI ANNABI A BAYANSA, TILAS NE HUJJA KAN HALITTA TA KASANCE A TSAYE KUMA KALUBALEN DOLE NE YA CI GABA HAR TASHIN KIYAMA, KUMA HUJJOJIN MU’UJIZAR ALKUR’ANI SUNA DA YAWA MATUKA, MAFI MAHIMMANCI DAGA CIKINSU SHI NE GAGARA TA FUSKAR HARSHE DA MAGANA, WANDA SHINE ABIN DA ALLAH YA KALUBALANCI LARABAWA WADANDA SU NE MAGABATA WAJEN IYA BAYANI DA KAIFIN HARSHE CEWA SU KAWO IRIN WANNAN ALKUR’ANI MAI GIRMA, KUMA WANNAN ALAMA CE TA ASALIN ALKURANI CEWA DAGA ALLAH YAKE.

ME YASA ALLAH BAIYI ALKAWARIN KIYAYE LITATTAFAN DA SUKA GABATA BA?

ALLAH – MADAUKAKI – YANA AIKATA ABIN DA YA GA DAMA, KUMA YANA DA HIKIMA DA MUKA SAN WASU DAGA CIKINSU KUMA BA MU SAN WASU BA, AMMA BAYYANANNUN HUJJOJI SUN NUNA CEWA LITTATTAFAN DA SUKA GABATA BA MU’UJIZA BA NE, DON HAKA BA A BUKATAR CI GABANSU, HUKUNCINSU  NA ƊAN LOKACI NE DON WASU MUTANE IYAKANTATTU.

MECECE HUJJAR CEWA BA ABINDA YA CANZA DAGA KUR’ANI?

IRIN WANNAN TAMBAYAR GALIBI WAƊANDA SUKE MAKARANTAR SAKANDARE NE  DA GABANTA NE KAWAI SUKE GABATAR DA ITA, SABODA HAKA; YA KAMATA MU YI MASA BAYANI CIKIN NUTSUWA DA MAHANGAR HANKALI DA KE TABBATAR DA INGANCIN KUR’ANI, DON HAKA SAI MU CE MASA: IDAN ABUBUWA SUN MAIMAITA TABBATA SUKE YI, KUMA IDAN SUKA YADU SUKAN TABBATA, TO ALKUR’ANI «AN RAWAITO SHI NE TA HANYAR TAWATIRI, SAI MU YI MASA BAYANIN MA’ANAR TAWATIRI- WANDA SHI NE ISAR DA SAKO DAGA WATA JAMA`A WACCE BA ZATA HADU WAJEN YIN KARYA BA – WANDA MALAMAI DA GAMA-GARI KOWA YA SAN WANNAN SAKON. KUMA MUSULMAI SUKA GAJE SHI DAGA ZURIYA ZUWA ZURIYA, SUNA NAZARIN SA A CIKIN TARON SU, SUNA KARANTA SHI A CIKIN ADDU’O’IN SU, KUMA SUNA KARANTAR DA SHI GA YAYAN SU, KODA KUWA A CEWA WANI DATTIJO MAI DARAJA DA GIRMA, IDAN YAYI KUSKURE A CIKIN SAKON, WANI YARO ZAI MARTINI A GARE SHI TUN KAFIN MANYA HAR SAI YA ISO ZUWA GARE MU TSARKAKAKKE DAGA ƘARI, ABIN KAREWA DAGA TAWAYA DA KUMA CANJI, KODA KUWA ZA A IYA MUSUN WANNAN DALILIN; DON KAIWA GA MUSUN TABBATATTUN HUJJOJI, KAMAR SAMUWAR ANNABI DA SAHABBAI MASU DARAJA, DA WADANDA SUKA SHAHARA A TARIHI, TO DUKKAN MASU HANKALI BA ZASU KARBI WANNAN BA, HAKA KUMA, A CIKIN KUR’ANI ALLAH YA KALUBALANCI MUTANE DA ALJANNU SU ZO DA WANI ABU MAKAMANCIN SA KUMA AMMA SUKA KASA, KUMA KUR’ANI DUK DA YAWANSA BA SHI DA WANI SAƁANI, KO CIN-KARO KO TAWAYA, SABODA ABIN DA YA ƘUNSA NA MU’UJIZOZI A LABARAI, DA DOKOKI, DA HUKUNCE-HUKUNCE DA MAGANGANU .. YANA NUNA CEWA BABU WANI CANJI DAGA MUTANEN DA AIKINSU DA MAGANGANUNSU SUKE CANZAWA. TO SHI DAGA ALLAH YAKE, KUMA ALLAH YA NE YA DAU GABARAR KIYAYE SHI..

'Fel a tetejéhez' gomb