RUKUNAN TARBIYYAR DASA IMANI

RUKUNI NA FARKO:

IMANI DA ALLAH

FIDIRA DA HANKALI DA SHARI’A SUN YI NUNI AKAN SAMUWAR ALLAH, KO WACCEE HALITTA TANA KAN IMANI DA ABIN HALITTARTA NE, HANKALI YAYI NUNI AKAN WADANNAN HALITTUN DOLE YA KASANCE AKWAI ABINDA YA SAMAR DA SU, ITA KUMA SHARI’A TA YI NUNI AKAN DUKKAN ADDINAN DUNIYA SUN TABBATAR DA SAMUWAR MAHALICCI. DAN HAKA IMANI DA ALLAH YA KUNSHI AL’AMURA GUDA HUDU:

1- SAMUWAR ALLAH.

2- IMANI DA RUBUBIYYAR SHI. DA KUMA CEWA SHINE ME BADAWA, MAHALICCI, MAI AZURTAWA, MAI KUMA JUJJUYA AL’AMURA.

3- IMANI DA KADAITUWAR ALLAH, BASHI DA ABOKIN TARAYYA.

4- IMANI DA SUNAYEN SHI DA SIFFOFIN SHI MASU TABBATAR DA CIKAR KAMALA DA KYAWUN.

ZAMU KOYA MA YARO WADANNAN ABUBUWAN GUDA HUDU, YA TARBIYYARTU AKAN SANIN ALLAH DA GIRMAMA SHI DA SON SHI. WANNAN RUKUNIN SHI NE TUSHEN SAURAN RUKUNAN. IN YA KIYAYE YA SAN SHI TO ZAI GANE SAURAN IN SHA ALLAH.

ME YASA ZAMU KOYA MUSU SON ALLAH?

  1. SABODA ALLAH DA SHA’ANIN SHI YA GIRMAMA SHI NE YA SAMAR DA MU DAGA RASHI, YA KUMA DAIDAITA HALITTAR MU YAYI MU DA SURA MAI KYAU, YA KUMA DAUKAKA MU AKAN DA YAWA DAGA SAURAN HALITTU, YA KUMA YI MANA MAFI GIRMAN NI’IMA WATO MUSULUNCI, SANNAN YA AZURTA MU DA ABUBUWA MASU YAWA DAGA FALALAR SA BA TARE DA MUN CANCANCI HAKAN BA, SANNAN SHI DIN ZAI MAI DA MU CIKIN ALJANNA SAKAMAKON AYYUKAN DA MUKA AIKATA, WANDA HAKAN KYAUTAR SHI CE DA FALALAR SHI A GARE MU. DAN HAKA ALLAH SHINE YA KAMATA A DAUKAKA TUN FARKO DA KARSHEN RAYUWA.
  2. SABODA SO NA HAIFAR DA GIRMAMAWA DA KWARJINI A ASIRCE DA BAYYANE, AMMA BUKATUWAR MU ZUWA GA YARAN MU SU GIRMAMA UBANGIJIN SU SUJI KWARJININ SHI YAFI FIYE DA A CE ALAKAR SU DA SHI TA TSAYU NE AKAN TSORO DA UKUBAR SHI KO AZABAR JAHANNAMA KADAI. IN AKA GINA SU AKAN HAKAN, TO, SAI YA KASANCE SUNA JIN DADIN BAUTA MAI SU RAYU ACIKIN JIN DADI SABODA ITA, SU KUMA KU BUTA DAGA DUKKAN WATA ZAMIYA.
  3. SABODA ALLAH SHINE RAYAYYE TSAYAYYE AKODA YAUSHE WANZAJJE WANDA BA YA MUTUWA, WANDA GYANGYADI KO BACCI BASA DAUKAR SHI, SHI YANA TARE DA SU A DUK INDA SUKE, SHI YAKE KIYAYE SU YA KULA DA SU FIYE DA IYAYEN SU, DAN HAKA, DANFARUWAR SU DA SHI DA SON SHI YA ZAMA DOLE HAR SU SAN CEWA SUNA DA ABIN DOGARO MAI KARFI WATO ALLAH (S.W.T).
  4. SABODA KUMA IDAN SUN SO ALLAH AZZA WAJALLA TO ZA SU SO KUR’ANI, SU RINKA SALLAH. IDAN KUMA SUKA SAN ALLAH MAI KYAU NE YANA SO ABU MAI KYAU TO ZASU AIKATA DUK ABINDA SUKA SAN YANA DA KYAU,IDAN KUMA SUKA SAN ALLAH YANA SON MASU TUBA KUMA YANA SON TSARKAKKU, DA MASU KYAUTATAWA DA MASU GASKIYA DA MASU HAKURI DA MASU TAWAKKALI, DA MASU TSORON ALLAH, TO ZASU YI KOKARI DAN SU SIFFATU DA DUKKAN WADANNAN SIFFOFIN DOMIN NEMAN YARDAR SHI DA SOYAYYAR SHI DA TSIRA DA SAMUN YARDARSA AGARE SU DA KARIYAR SHI AGARE SU. IDAN KUMA SUKA SAN ALLAH BAYA SON MASU HA’INCI KUMA KAFIRAI MASU GIRMAN KAI DA TSAURIN IDO, DA ZALUNCI MASU FASADI A DORON KASA TO ZASU NISANCI WADANNAN MUNANAN AYYUKAN GWARGWADON IYAWAR SU. ZASU NISANCE SU NE DUKA DOMIN SON SU GA ALLAH DA KWADAYIN NEMAN YARDAR SHI.
  5. SABODA SON ALLAH NA NUFIN JIN SAMUWAR ALLAH TARE DA MU WANDA YAKE SA MUTUM YA SAMU NATSUWA DA JIN DADI DA TABBATUWA, DA RASHIN SHIGA DAMUWA DA BAKINCIKI, DA KUBUTAR ZUCIYA DA JIKI DAGA CIWUKAN ZUCIYA DA GABBAI, WANDA YAFI WANNAN MUHIMMANCI SHI NE KUBUTA DAGA SABUKA DA ZUNUBAI.

YAYA ZAMU KOYAWA ‘YA’YANMU SON ALLAH (S.W.T)?

  1. ANA KIRGA CEWA  HANYA DAYA DA ZA A BI WAJEN DASA MA YARO TAUHIDI SHI NE TA HANYAR GANI KARARA, MA’ANA MU MUKAN DOGARA AKAN GABBAN JI WAJEN KARFAFA IMANIN YARO GA UBANGIJIN SHI, SAI MU YI AMFANI DA ABUBUWAN DA YAKE GANI A TARE DA SHI KAMAR RANA, RUWA, ISKA, DAGA WADANNAN ABUBUWAN DA YAKE GANI ZAMU KOYA MA YARO CEWA AKWAI MAHALICCI WANDA SHI KE JUYA WANNAN DUNIYAR, KUMA MU KWADAITAR DA SHI AKAN YA RINKA TAMBAYA ANA MAI BAYANIN ABINDA BE GANE BA ANA MAI BAYANI, MU KUMA YI KOKARI WAJEN NUNA MA YARO ABUBUWA DA ZASU KARA IMANI SU GANI DA IDO TA YADDA ZASU GANE HUJJAR CEWA LALLAI AKWAI ALLAH A DUKKAN KOMAI, A WARWARE MUSU SU, SANAR DA SHI FANNONIN ILIMI, MU NUNA MUSU IKON ALLAH AKAN MU`UJIZOZI NA ALLAH, DAGA CIKIN IRIN ABINDA ZA A NUNA MUSU WANDA DOLE ZAI SA SU GANE HAKAN SHI NE FARKON HALITTAR DAN ADAM WATO YADDA AKA HALICCI DAN ADAM, ALLAH (S.W.T) YA CE, { MUTUM YA DUBA DAGA ME AKA HALICCE SHI.) [TARIK:5], YA KUMA CE { KUMA ACIKIN KAWUNAN KU AKWAI AYOYI SHIN BA ZAKU DUBA BA? } [ZARIYAT: 21], HAKA MA DUBI ZUWA GA ABINCIN MUTUM DA YADDA ALLAH YA SAMAR DA SHI YA KUMA BAYYANA MATAKAN SHI. ALLAH (S.W.T) YA CE: {MUTUM YAYI DUBI ZUWA GA ABINCIN SHI.} [ABASA: 24], HAKA DUBA ZUWA GA IRIN IKO NA ALLAH TA HANYAR DUBA ZUWA GA HALITTUN SHI DA SUKE NUNI AKAN GIRMAN SHI KAMAR YADDA ALLAH (S.W.T) YA FADA: {ASHE BA KUYI DUBI ZUWA GA RAKUMI BA YADDA A KA HALICCE SHI (17) DA SAMA YADDA AKA DAGA TA (18) DA DUWATSU YADDA AKA KAFE SU (19) DA KASA YADDA AKA SHIMFIDA TA} [AL-GHASHIYAT: 17- 20]. ANA IYA MATSO DA WADANNAN MANYAN MA’ANONIN DA ABINDA KE CIKIN SU NA KYAWUN HALITTA DA GIRMAN MAHALICCI A KWAKWALWAR YARA DAI-DAI DA SHEKARUN SU, ARINKA CANZA MUSU HANYOYIN BAYANAN DON SAKON YA ISA TA HANYAR AMFANI DA HANYOYIN KOYARWA KALA-KALA NA DA DA NA ZAMANI. A YADDA YARO YAKE, ZAI SO WANDA YA HALITTA MAI IRIN WADANNAN KYAWAWAN ABUBUWAN MASU GIRMA.
  2. KOYA MA YARO SUNAYEN ALLAH KYAWAWA DA SIFFOFIN SHI DA SUKE NUNI  AKAN KAMALA DA KYAWUN SHI, ALLAH (S.W.T) SHI NE MAI RAHMA MAI JIN KAI, WANDA RAHAMAR SHI TA MAMAYE DUKKAN KOMAI, SHI NE MAI AFUWAN DA YAKE YAFIYAR KOWACCE IRIN ZAMIYAR DA MUTUM YA SAMU, KUMA SHI NE MAI GAFARAR DA YA TATTARA AFUWA MAI SITIRTAWA, KUMA MAI KARAMCI DA YAKE BAYARWA GA MABUKACI BA TARE DA DALILI BA, KUMA MAI SHIRYARWA DA YAKE SHIRYAR DA BAYI ZUWA GA DUKKAN ABUBUWA MASU AMFANI, MASOYI DA YAKE SO A KUMA SO SHI, SANIN WADANNAN ABUBUWAN BA MAKAWA ZASU TAIMAKAWA YARO WAJEN SON ALLAH.
  3. YA WAJABA MU NISANCI FADA MA YARO CEWA IDAN BAKA JIN MAGANA TABA KUMA KA YI MIN BIYAYYA TO ALLAH ZAI MAKA UKUBA, AKWAI BANBANCI TSAKANIN SANAR DA YARO CEWA ALLAH NA YIN UKUBA GA WADANDA YA SABA MAI DA KUMA HADA UKUBAR ALLAH DA YIN BIYAYYA AKODA YAUSHE KAR A YI WA YARO BARAZANA AKAI, WANNAN NA DAGA CIKIN ABIN DA ZAI HANA DAN KU YIN TUNANI MAI ZURFI AKAN KUDIRAR ALLAH DA GIRMAN SHI, BAI KAMATA A DOGARA DA TARBIYYAR AKAN YI MAI BARAZANA DA UKUBAR ALLAH BA, SAI DAI WAJIBIN MU NE MU KOYA MAI SON ALLAH DA GIRMAMA SHI KADA MU JINGINA DUK ABINDA MUKA SAN ZAI MA YARO TASIRI A MAHANGAR SHI GAME DA ALLAH (S.W.T).
  4. ALOKACIN DA YARO YA GA IYAYEN SHI SUNA GABATAR DA SALLAH KO WANI ABU NA FARILLA, KO SUNA YIN WANI ABU DA YAKE HARAMUN NE, SO DA DAMA YA KAN TAMBAYI DALIKIN AIKATA HAKAN, DOLE A WANNAN LOKACIN TAMBAYAR TA ZAMANA AMSAR DA ZA A BASU TA KUNSHI AMBATON ALLAH TA’ALA TARE DA YI MAI BIYAYYA, HAKAN SAI YA KASANCE TARBIYYA DA KOYI GA WANDA KE TARBIYYAR SHI AKAN SON ALLAH, SABODA SHI YARO YANA KWAIKWAYON IYAYEN SHI NE, KUMA DAGA ACIKIN ABUBUWAN DA KE DASA SON ALLAH ACIKIN ZUCIYAR YARO SHI NE BA SU LABARI AKAN ALJANNAH DA ABINDA ALLAH YA TANADAR ACIKIN TA GA BAYIN SHI MASU TSORON SHI NA DAGA NI’IMA DA BATA GUSHEWA.
  5. IDAN YARO YA KAI SHEKARUN DA YA GANE ME AKE NUFI DA WAJIBI, TO SAI A KOYA MAI WAJABCIN WANNAN SON GA ALLAH, SABODA ALLAH (S.W.T) SHI NE WANDA YA HALICCE MU YA KUMA DAIDAITA HALITTAR MU YA AZURTA MU YA KUMA DAUKAKA MU AKAN DA YAWA DAGA CIKIN SAURAN HALITTUN SHI YA KUMA YI MANA NI’IMA DA MUSULUNCI, KUMA MU KOYA MA YARO CEWA DUKKAN NI’IMOMIN DA KE KEWAYE DA SHI DAGA ALLAH NE, MU KUMA KOYA MAI YADDA AKE GODEMA ALLAH AKAN WADANNAN NI’IMOMIN AKUMA TAMBAYE SHI KARI AKAI.
  6. AKOYA MAI HANYOYIN DA ZAI DOGARA DA SU WAJEN SAMUN SOYAYYAR ALLAH DA MANZON SHI (S.A.W) NA DAGA MAGANGANU DA AYYUKAN SHI.

RUKUNI NA BIYU:

IMANI DA MALAIKU

GASGATA SAMUWAR SU, DA IMANI DA ABINDA MUKA SANI NA SUNAYEN SU, DA ABINDA YA INGANTA NA DAGA LABARAI AKAN SU DA SOYAYYAR SU, DAGA CIKIN MANYAN ABINDA YA KAMATA A DASA MA YARO A ZUCIYAR SHI AGAME DA MALA’IKU SU NE:

  1. SANAR DA SHI CEWA SU MALA’IKU HALITTU NE DA AKA HALICCE SU DAGA HASKE. DAGA AISHA (R.A) TA CE: MANZON ALLAH (S.A.W) YA CE: ((AN HALICCI MALA’IKU DAGA HASKE, KUMA AN HALICCI ALJANU DAGA WUTA, KUMA AN HALICCI ADAM DAGA ABINDA AKA SIFFANTA MUKU)) [MUSLIM: 2996],  ASIFFANTA MUSU A DUNKULE BA TARE DA AN TSAYA RARRABE MUSU WANNAN HALITTA TA MALA`KU DA DABI`ARSU BA.
  2. A KOYA MISHI SUNAYEN SU DA AYYUKAN SU, KAMAR ACE MAI JIBRIL SHI NE AMINTACCEN MALA’IKU KUMA SHI NE SHUGABAN SU SHI NE ALLAH YA SAUKAR DA AL KUR’ANI TA HANNUN SHI. MIKA’IL SHI NE ME KULA DA SAUKAR RUWAN SAMA, ISRAFIL SHI NE ME BUSA RAI, KUMA AKWAI MASU DAUKE DA AL’ARSHIN ALLAH, AKWAI MASU RUBUTA AYYUKAN BAYI, AKWAI MASU TSARON ‘YAN ADAM DA SAURAN SU.
  3. YI MUSU BAYANIN CEWA ADADIN MALA’IKU NA DA YAWA SOSAI DAN HAKA BA WANDA YA SAN ADADIN SU SAI ALLAH, KUMA AN HALICCE SU KAWAI DON YI MA ALLAH BIYAYYA DA BIN UMURNIN ALLAH, KUMA KO WANE MALA’IKA AKWAI AIKIN SHI DA AKA DORA MAI YAKE YI.
  4. A SANAR DA SU CEWA SU BASA ZUNUBI, SUNA BAUTA MA ALLAH IBADAR DA BATA YANKEWA, BASA GAJIYA DA BAUTA MAI KUMA BASA GIRMAN KAI, KUMA SUNA SON MUMINAI SUNA TAIMAKON SU SUNA YI MUSU ADDU’A SUNA BASU KARIYA, KUMA SUNA HALATTAR MAJALISAN DA AKE AMBATON ALLAH SUNA BIBIYARSU.
  5. A SANYA MA YARO SON MALA’IKU TA HANYAR SANAR DA SU YANAYIN AIKIN ALKHAIRI NA MALA’IKU DA NUNA MUSU HALAYEN MALA’IKU NA KULA DA KWADAYIN SU GA MUMINAI, INDA AKE SANYA SO GA WADANNAN HALITTUN MASU ALBARKA DA SALIHANCI, SABODA SUNA TASBIHI DA ISTIGFARI DA ADDU’A GA MUMINAI DA KUMA YIN BUSHARAR SHIGA ALJANNAH GA MUMINAN DA SUKA TSAYU AKAN HANYAR GASKIYA DA IMANI DA AIKI NAGARI, KUMA SUNA YIN SALATI GA MUMINAI SUNA TAIMAKON SU SU TABBATAR DA SU, DA KUMA CEWA SU MASU KIYAYEWA NE GA AYYUKAN SU, ALLAH YANA AIKO SU DON KIYAYE BAYI. ALLAH TA’ALA YA CE: { KOWANNEN KU YANA DA WADANSU MALA’IKU MASU MAYEWA JUNA A GABA GARE SHI DA BAYA GARE SHI, SUNA TSARE SHI DA UMURNIN ALLAH…} [ RA’AD: 11)]
  6. IMANI DA SU SHI NE KE WAJABTA A GIRMAMA SU A DAUKAKA SU, SU BAYI NE MASU GIRMA BA SA SABA ABINDA ALLAH YA UMURCE SU, KUMA SUNA AIKATA ABINDA YA UMURCE SU, KUMA YA WAJABA A TSARKAKE SU DAGA SIFFOFIN DA BAI DACE DA SU BA.
  7. KWADAITARWA GAME DA TSAFTA  TA YADDA MALA`IKU KAN CUTU DAGA IRIN ABINDA YAN ADAM KAN CUTU DAGA GARE SHI. DAGA JABIR (R.A) YA CE: MANZON ALLAH (S.A.W) YA CE: (( DUK WANDA YA CI DAGA WANNAN BAKLIYYAR, TAFARNUWA (BAKALIYYA SHI NE DUK ABINDA SHUKARTA KE FITOWA DAGA KASA KAMAR DOYA) SAI YA KUMA MAIMAITA; DUK WANDA YA CI ALBASA DA TAFARNUWA DA KURRAS TO KADA YA KUSANCI MASALLACIN MU, DOMIN MALA’IKU SUNA CUTUWA DAGA ABINDA ‘YAN ADAM KE CUTUWA DA SHI [MUSLIM: 564]
  8. ACIKIN SAMUWAR MALA’IKU AKWAI HIKIMOMI MASU YAWA; DAGA CIKI SHI NE DAN MUTUM YAKE SANIN GIRMAN ILIMIN ALLAH DA GIRMAN IKON SHI DA GIRMAN HIKIMAR SHI. DAGA CIKI SAMUWAR MALA’IKU NA SA MUTUM MUSULMI YA JI NATSUWA SABODA YA SAN AKWAI MASU BASHI KARIYA BISA UMURNIN ALLAH KUMA SUNA TAIMAKON SHI.
  9. ALAKAR MALA’IKU DA MU WAJEN HALITTA DA SAMAR DA MU DA KULAWAR DA SUKE BAMU TUN KAFIN A SAMAR DA MU HAR AKA SAME MU  TANA SA ASAN CEWA LALLAI DAN ADAM YANA DA MUHIMMANCI, YANA DA KIMA, KUMA TANA KORE TUNANIN CEWA SHI BA KOWA BANE KO KUMA SHI KARAMIN ABU NE, DAN HAKA TA HAKA NE ZAI SAN GIRMAN KAN SHI, KUMA YAYI IYA KOKARIN SHI WAJEN SAUKAR DA ABUBUWAN DA YA KAMATA YAYI A RAYUWAR SHI TA DUNIYA.

RUKUNI NA UKU:

IMANI DA LITTAFAI

IMANI DA LITTAFAI YA KUN SHI ABUBUWA KAMAR HAKA:

  1. IMANI DA LITTAFAN DA ALLAH YA SAUKAR, KUMA WANNAN YANA DAGA CIKIN MANYAN RAHAMAR ALLAH GA BAYIN SHI, INDA YA SAUKAR DA LITTAFI GA KOWACE AL’UMMA DA YA ZAMA SHIRIYA A GARE SU TA YADDA YA DACE DA SU NA DAGA SHARI’O’A DA HUKUNCE-HUKUNCE. KUMA A BAYYANA MA YARO CEWA SAUKAR DA LITTAFAI DA ALLAH YAYI BA KARAMAR NI’IMA BA CE GA BAYI, SABODA DALILIN HAKAN MUKA SAN ALLAH DA RANAR LAHIRA MUKA KUMA SAN ABINDA YAKE DAI-DAI DA WANDA BA DAI-DAI BA.
  2. GASGATAWA GA SUNAYEN SU DA AKA FADA MANA, KAMAR LITTAFIN ANNABI IBRAHIM, DA ATTAURAH DA AKA SAUKAR DA ITA GA ANNABI MUSA (A.S), DA ZABURA TA ANNABI DAWUD (A.S), DA INJILA DA AKA SAUKAR DA ITA GA ANNABI ISA (A.S), SAI ALKUR’ANI DA AKA SAUKAR DA SHI GA ANNABI MUHAMMAD (S.A.W).
  3. CEWA WADANNAN LITATTAFAN SASHIN SU NA GASGATA SASHI, BABU KARYATAWA A TSAKANINSU, KUMA BABU TUFKA-DA-WARWARA DA CIN KARO A TSAKANIN SU. ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA CE: {… YANA ME GASGATAWA GA ABINDA YAKE GABA GARE SHI NA DAGA LITTAFI} [MA’IDAH:48]
  4. GASGATA ABINDA YA INGANTA NA LABARAN DA SUKA ZO MANA GAME DA SU LITTAFAN, A SANAR DA SHI CEWA DUKKAN LITTAFAN DA ALLAH YA SAUKAR WADANDA SUKA GABATA AKWAI CANJE-CANJE ACIKIN SU SABODA SU SUN TAKAITU NE NA ZUWA WANI LOKACI KEBANTACCE IYA ZAMANIN DA AKA SAUKAR DA SU KAWAI, SAI DAI ALKUR’ANI SHI ALLAH YA KARE SHI BA ME IYA CANJA SHI.
  5. ALKUR’ANI YA SHAFE HUKUNCE-HUKUNCEN DUKKAN SAURAN LITTAFAI DAKE GABANIN SHI, SANNAN AIKI DA HUKUNCE-HUKUNCE NA ALKUR’ANI  DOLE NE HAR ZUWA RANAR TASHIN ALKIYAMAH. YA WAJABA A YI AIKI DA UMURNIN SHI A KUMA GUJE MA ABINDA YAYI HANI DA SHI, A HARAMTA ABINDA YA HARAMTA A KUMA HALASTA ABIN DA YA HALASTA, DA AIKI DA FAYYACACCEN BAYANIN SHI DA MIKA WUYA GA ABINDA KE DA RIKITARWA A CIKIN SHI, DA TSAYAWA INDA YACE A TSAYA DA KUMA TSAYUWA AKAN KOYARWAN SHI.

KUMA DAGA CIKIN AL’AMURA MASU MUHIMMANCI DA ZA SU SHIGA CIKIN BABIN IMANI DA LITTAFAI SU NE: MAS’ALAR HADDATAR DA YARA ALKUR’ANI TUN SUNA KANANA, KUMA ANA SANYA HADDAR ALKUR’ANI DAYA DAGA CIKIN ABUBUWA MASU MUHIMMANCI WAJEN KARA KAIFIN BASIRA GA YARA, IDAN AKA KYAUTATA SHI KUMA MAI TARBIYYA YA IYA SA YARON YA RAYU TARE DA TUNO MA’ANONIN AYOYI, ALKUR’ANI YANA KIRAN MU ZUWA GA LURA DA TUNANI AKAN HALITTUN SAMMAI DA KASSAI, DA KUMA HALITTAR DAN`ADAM DA ABUBUWAN DA AKA HALITTA A KEWAYE DA MU DON YA KARA MANA IMANI YA SA MUYI AIKI DA ILIMI, KUMA HADDAR ALKUR’ANI MAI GIRMA DA SANIN MA’ANONIN SHI YANA KAI MUTUM ZUWA GA ZAMA MAI WAYO SOSAI, KUMA YANA SA YARO YA ZAMA MAI FASAHA DA IYA BAYANI, WANNAN KUMA ZAI FARU NE TA DALILIN SABA MA HARSHEN YARO DA KARATUN KUR’ANI DA KYAU SANNAN YANA TARBIYYANTAR DA ZUCIWA WAJEN TUNA ALLAH DA SANYA TSORO, DA KHUSHU’I, DA KWADAITARWA DA TSORATARWA DA KUMA TAUSHIN ZUCIYA, KUMA YARO ZAI SABA DA AIKI DA ABINDA KUR’ANI YA KOYAR DA LADUBBAN SHI A KOWA NE BANGARE DAGA BANGARORIN RAYUWA NA YAU DA KULLUM, KUMA YARO ZAI TARBIYYARTU AKAN RAYUWA MAI TSARI DA DABI’U NAGARI. DAGA CIKIN FA’IDAR IMANI DA LITTAFAI SHI NE ABINDA MUTUM ZAI SAMU NA LADA MAI GIRMA DA FALALA MAI YAWA DAGA ALLAH MADAUKAKIN SARKI A HALKA TA HADDAR ALKUR’ANI.

TA YAYA ZAMU KWADAITAR DA YARO YIN HADDAR ALKUR’ANI?

  1. ZA A YI MISHI BAYANI YA SAN FALALAR ALKUR’ANI, DA FALALAR HADDACE SHI DA TILAWAR SHI DA AIKI DA SHI, KAMAR YADDA MANZON ALLAH (S.A.W) YA CE: «KU KARANTA ALKUR’ANI, DOMIN ZAI  ZO A RANAR KIYAMA A MATSAYIN MAI CETO GA MA`ABOTANSA» (MUSLIM (804)), KUMA DA FADIN MANZON ALLAH TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI – YA CE: «ZA A CE WA MA’ABOCIN ALKUR’ANI: KARANTA, KA HAU, KA KARANTA KAMAR YADDA KAKE KARANTAWA A DUNIYA, SABODA MATSAYINKA YANA AYAR KARSHE DA ZAKA KARANTA». (TIRMIZI: 2914)), DA FADINSA – TSIRA  DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI: “MISALIN MUMINI WANDA YAKE KARANTA ALKUR’ANI KAMAR GWANDAR DAJI NE, KAMSHINTA MAI DADI NE KUMA DANDANOTSA YANA DA DADI, KUMA MISALIN MUMINI WANDA BA YA KARANTA ALKUR’ANI. KAMAR DABINO NE, BA SHI DA KANSHI AMMA YANA DA ZAKI, KUMA MISALIN MUNAFIKIN DA YAKE KARANTA ALKUR’ANI KAMAR FULAWA EE, TANA DA KANSHI AMMA TANA DA DACI, KUMA MISALIN MUNAFIKIN DA BA YA KARANTA ALKUR’ANI KAMAR GUNA NE, BATA DA KANSHI KUMA GATA DA DACI”. (BUKHARI (5427)), DA FADINSA – ALLAH YA YI SALATI DA SALAMA A GARE SHI:» MAFIFICINKU SHI NE WANDA YA KOYI ALKUR’ANI KUMA YA KOYAR DA SHI”. (BUKHARI (5027)), KUMA A AMBACI MISALAI NA MAGABATA GAME DA ALKUR’ANI, KUMA WANNAN YANA DAYA DAGA CIKIN MANYA-MANYAN HANYOYIN KARA KWAZO.
  2. A SANYA SHI A MAKARANTU KO HALKOKI NA KOYAR DA ALKUR’ANI KO A NEMA MISHI MALAMI DA ZAI RINKA KOYAR DA SHI ALKUR’ANI. KUMA A SAMAR DA KYAUTUTTUKA DA WAJE ME KYAU DON SANYA GASA TSAKANIN YARA KO DALIBAI.
  3. DOLE A BIYO MAI TA HANYAR SAUKI NA YIN HADDAR DAGA FARKO DON YA SO ABIN SOSAI. SAI A FARA MAI HADDAR DAGA JUZU’IN (AMMA) SABODA YAFI SAUKIN HADDACEWA GA YARA TUNDA AYOYIN SU GAJERU NE KUMA SURORIN BASU DA TSAWO BARE YARO YAJI KOSAWA, KUMA SURORIN SUN KUN SHI ABUBUWAN DA SUKA SHAFI RUKUNAN IMANI, DON HAKA ZASU INGANTA IMANI SU KUMA GYARA DABI’UN YARO. KUMA ZASU KIYAYE LAFIYAR YARO SU AMINTAR DA SHI DOMIN SHI ALKUR’ANI TUNATARWA NE DA KUMA MAGANI. KARI AKAN HAKA SHI NE YANA SAITA HARSHEN YARO YA IYA MAGANA YA KUMA IYA BAYANI.
  4. A MAIDA HANKALI WAJEN YIMA YARO SHARHIN WASU AYOYI ATAKAICE LOKACIN DA AKE MAI TILAWA KUMA AKE HADDATAR DA SHI QUR’ANI. KADA MU JI CEWA YARO NE BASHI DA BUKATAR HAKAN DOMIN KWAKWALWAR YARO TANA DA ABIN MAMAKI WAJEN HADDA DA KUMA FAHIMTA.
  5. A FAHIMTAR DA SHI CEWA ALKUR’ANI WARAKA CE KUMA RAHAMA DA ALBARKA NE A RAYUWAR MUTUM. ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA CE: {KUMA MUNA SASSAUKARWA DAGA ALKUR’ANI ABINDA YA KE WARAKA NE DA RAHAMA GA MUMINAI..} [ISRA’I: 82]. SANNAN KUMA WANDA YA HADDACE SHI KO YA HADDACE WANI YANKI DAGA CIKI TO ZAI IYA YIWA KAN SHI ADDU’A LOKACIN DA BASHI DA LAFIYA HAKA KUMA ZAI IYA WA WANDA KE TARE DA SHI ADDU’A.

RUKUNI NA HUDU:

IMANI DA MANZONNI

IMANI MANZONNI YA KUNSHI IMANI DA GASGANTA SU DA IMANI DA LABARAN DA SUKA ZO MANA DA SU, DA KUMA CEWA ALLAH YA ZABE SU DAGA CIKIN MUTANEN SU, DAN HANKALIN SU DA DABI’UN SU YA BANBANTA DA NA SAURAN MUTANE DON KUMA SU ISAR DA SAKON ALLAH (S.W.T). ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA CE: {BA MU AIKO WANI MANZO BA FACE DA HARSHEN MUTANENSA DOMIN YA BAYYANA MUSU.} [IBRAHIM:4], DA ACE MANZO MALA’IKA NE DA BA A FAHIMCE SHI BA, KUMA BAYA HALATTA AGARE MU MU BANBANCE TSAKANIN WADANNAN MANZONNIN, BA ZA MU YI IMANI DA WASU MU KAFIRCE MA WASU BA, SAI DAI MUYI IMANI DA SU BAKI DAYA, DUKKAN MANZONNI MASU GASKIYA NE A SAKONNIN DA SUKA ZO DA SHI, KAMAR YADDA SUKE MASU BIYAYYA GA ALLAH WAJEN YI MA AL’UMMAR SU NASIHA, BA MASU SABAWA BANE GA ABINDA SUKE ISARWA NA SAKON ALLAH, KUMA BAYA HALATTA MUYI AIKI DA WATA SHARI’A FACE SHARI’AR CIKAMAKIN ANNABAWA MUHAMMAD (S.A.W). DAGA CIKIN ABINDA YA KAMATA A DASA MA YARA A ZUCIYA GAME DA IMANI DA ANNABAWA SU NE:

  1. BAYANIN CEWA ALLAH YA AIKO MA KOWACE AL’UMMA DA MANZO DAGA CIKINSU, YANA KIRAN SU ZUWA GA BAUTA MA ALLAH SHI KADAI DA KUMA KAFIRCE MA ABINDA SUKE BAUTA WA KOMA BAYAN ALLAH, KUMA DUKKANIN SU MASU GASKIYA NE MASU GASGATAWA DA BIYAYYA GA ALLAH KUMA MASU SHIRYARWA DA TSORON ALLAH KUMA AMINTATTU.
  2. BAYANIN CEWA DA’AWAR SU IRI DAYA CE TUN DAGA NA FARKONSU HAR ZUWA NA KARSHENSU AKAN BAUTA DA TUSHEN TA WANDA YAKE SHI NE KADAITA ALLAH DAGA DUKKAN SAURAN ABIN BAUTA, TARE DA GASGATA HAKAN A ZUCIYA DA FADI A BAKI DA KUMA AIKI, YA KUMA KAFIRCE MA DUK ABINDA AKE BAUTA MA KOMA BAYAN ALLAH.
  3. BAYANIN HIKIMAR ALLAH DA YA AIKO SU ZUWA GA MUTANE, DAGA CIKIN WADANNAN HIKIMOMIN AKWAI BAUTAR ALLAH (S.W.T) DA KADAITA SHI, HAKA SHIRYAR DA MUTANE ZUWA GA HANYA MADAIDAICIYA, DA KARANTAR DA MUTANE AL’AMURAN ADDININSU DA DUNIYARSU DA KUMA FITAR DA SU DAGA DUHU ZUWA HASKE, DAGA CIKIN TA AKWAI SHUGABANTAR AL’UMMA DA AIKATA SHARI’AR ALLAH ACIKINSU, DAGA CIKIN TA AKWAI KOYI DA SU DA TAFIYA AKAN MANHAJINSU.
  4. SANIN RAHAMAR ALLAH DA KIYAYE SHI DA BAUTAR SHI, INDA YA AIKO MANZONNIN SHI DOMIN SU SHIRYAR DA SU ZUWA GA HANYA MADAIDAICIYA, DA TUNASAR DA SU AKAN GODE MA ALLAH TA’ALA AKAN WANNAN BABBAR NI’IMAR, DA SON MANZONNI DA ANNABAWA DOMIN SUN TSAYU AKAN ISAR DA SAKON SHI DA YIN NASIHA GA BAYIN SHI, DOMIN MUTANE DUK YADDA AKA BASU FAHIMTA DA HANKALI DA WAYO TO BA YADDA ZA A YI SU FI KARFIN HANKULAN SU WAJEN TSARIN ABINDA ZAI ZAMA MASLAHA GA AL’UMMA BAKI DAYAN TA HAR SU ZAMA KAMAR AL’UMMA DAYA WAJEN BAMA ME HAKKI HAKKIN SHI. MANZONNI SUNA KOYA MA MUTANE ABINDA ZAI AMFANE SU NE SU KUMA HANA SU YIN ABINDA ZAI CUTAR DA SU.
  5. DASA SON MANZON ALLAH (S.A.W) A ZUCIYAR YARO DON SU IYA YI MAI BIYAYYA SU KUMA BI KOYARWAR SHI KUMA SU GIRMAMA SHI (S.A.W), DON KUMA SU FIFITA SOYAYYAR SHI AKAN TA KOWA DA SON WANDA YAKE SON SHI SU KUMA KI WANDA KE KIN SHI, DAGA CIKI AKWAI GIRMAMA SUNAN SHI DA GIRMAMA SHI A LOKACIN DA AKA AMBACI SUNAN SHI, IN ANCE MUHAMMAD SAI SU CE (S.A.W). DA YIN SALATI A GARE SHI DA GIRMAMA DUK WASU ABUBUWAN DA SUKA KEBANCE SHI DA SANIN FALALAR SHI, SHI NE YAFI KOWA JIN KAI DA TAUSAYI, DA GIRMAMA SHI AWAJEN KABARIN SHI DA MASALLACIN SHI GA WANDA YA SAMU ZIYARAR MASALLACIN SHI YA KUMA SAMU TSAYUWA A KABARIN SHI TA FUSKAR RASHIN DAGA MURYA AWAJEN.
  6. AMBATA MUSU KISSOSHIN SAHABBAI DA YADDA MANZON ALLAH (S.A.W) YAKE GIRMAMA SU DA YADDA SUKE GIRMAMA ANNABI (S.A.W) SUKE KUMA KISHIN SHI, MUSAMMAN MA KISSOSHIN KANANAN SAHABBAI KAMAR KISSAR ANAS BIN MALIK (R.A) DA IRIN KOYIN SHI GA ANNABI (S.A.W). WATARANA WANI MADINKI YA GAYYACI MANZON ALLAH (S.A.W) DAN CIN ABINCI, ANAS (R.A) YA CE: ( SAI NA TAFI TARE DA MANZON ALLAH (S.A.W) DON CIN WANNAN ABINCIN, SAI AKA MATSOMA MANZON ALLAH (S.A.W) DA BIREDI NA ALKAMA DA KUMA ROMO WANDA AKWAI KABEWA DA NAMA BUSASSHE ACIKI, SAI ANAS (R.A) YA CE; SAI NAGA MANZON ALLAH (S.A.W) YANA BIN INDA KABEWAR TAKE ACIKIN KWANON (YANA TSINTA YANA CI), YA CE: BAN GUSHE INA SON KABEWA BA TUN DAGA WANNAN RANAR. SUMAMATA (R.A) YA CE: DAGA ANAS (R.A) YA CE SAI NA RINKA TSINTAR KABEWAR INA TURAWA GABAN SHI.) [BUKHARI: 5439]. DON HAKA MAI TARBIYYA YA KWADAITU DA YIN BAYANIN YADDA SAHABBAN SHI SUKA KASANCE SUNA SON SHI KUMA SUKE SADAUKARWA WAJEN BIN HANYAR SHI (S.A.W) DA KAWO MUSU KISSOSSHI AKAN HAKAN.
  7. A SANAR DA SHI TASIRIN DA KE TATTARE DA WANNAN SON NA MANZON ALLAH (S.A.W), DAGA CIKIN TASIRIN HAKA SHI NE HADISIN DA YA ZO DAGA ANAS (R.A) CEWA WANI MUTUM YA TAMBAYI MANZON ALLAH (S.A.W) AKAN TASHIN ALKIYAMA YA CE: (YAUSHE ZA A YI TASHIN ALKIYAMA? SAI MANZON ALLAH (S.A.W) YACE: ((ME KA SHIRYA MATA?)) SAI MUTUMIN YA CE BA KOMAI, SAI DAI NI INA SON ALLAH DA MANZON SHI, SAI MANZON ALLAH (S.A.W) YA CE: ((KANA TARE DA WANDA KAKE SO.)) ANAS YA CE: MUNYI FARINCIKI DA FADIN MANZON ALLAH (S.A.W) ((KANA TARE DA WANDA KAKE SO.)) ANAS YA CE: NI INA SON MANZON ALLAH (S.A.W) DA ABUBAKAR DA UMAR (R.A) KUMA NI INA SON KASANCEWA TARE DA SU DA WANNAN SON DA NAKE MUSU KO DA BAN YI IRIN AYYUKAN SU BA. ) [BUKHARI: 5439]
  8. TAIMAKON YARO WAJEN KIRKIRAR CI GABA GAME DA ABINDA YA SHAFI SON MANZON ALLAH (S.A.W) KAMAR RUBUTA WAKE DA KISSA DA HUDUBA DA RUBUCE-RUBUCE DA SHIRYA GASA KALA-KALA DUKA AKAN ABINDA YA KEBANCI SON MANZON ALLAH (S.A.W)

YAYA ZA MU KOYA MA YARO SON ANNABI (S.A.W)?

  1. DOLE A TABBATAR MAI DA CEWA ALLAH TA’ALA YANA SON ANNABIN SHI (S.A.W), ALLAH YA ZABE SHI KUMA YA DAUKAKA SHI AKAN MUTANE BAKI DAYA, KUMA YA WAJABTA MU SO SHI, KUMA MU SANAR DA SHI CEWA SON ANNABI (S.A.W) YANA DAGA CIKIN ALAMOMIN SON ALLAH TA’ALA, WANDA KUMA YA SO MANZON ALLAH (S.A.W) TO YANA SON ALLAH NE SO NA GASKIYA.
  2. TUNASAR DA YARO CEWA MANZON ALLAH (S.A.W) YA KASANCE RAHMA NE GA MUTANE TA HANYAR SHIRIYAR DA SU DA KUMA ISAR DA WANNAN ADDININ, KUMA ZAI KASANCE RAHAMA GA MUMINAI TA CETON SU DA ZAI YI A RANAR ALKIYAMAH.
  3. KARANTAR DA TARIHIN ANNABI (S.A.W), YARO YA SAN CEWA MANZON ALLAH (S.A.W) MADUBI NE KUMA ABIN KWATANCE NE MAI GIRMA GA DUKKAN MUTANE, A FADA MUSU MU’UJIZOZAN SHI DA DABI’UN SHI MADAUKAKA DA TAIMAKON SHI GA WANDA AKA ZALUNTA DA TAUSAYIN SHI GA TALAKAWA DA KUMA WASIYYAR SHI GAME DA MARAYU, DA IRIN JIN KAN SHI GA MASU RAUNI. KUMA YA KASANCE MUN YI AMFANI DA KALAMAI DAIDAI DA FAHIMTAR YARO, DA KUMA TAKAITUWA AKAN AL’AMURA DA HANKALIN SHI ZAI IYA DAUKA, DON YA IYA FAHIMTAR SU, KUMA MU KULA DA CACCANZA HANYOYIN ISAR DA SAKON DON MU KAI GA ABINDA MUKE SO DA KUMA ABUBUWAN DA AKE BUKATA WAJEN BUNKASUWAN YARO WANDA YA DACE DA SHEKARUN DA YARO KE RAYUWA KUMA A KULA DA BANBANCIN DA KE TSAKANIN YARA TA WAJEN FAHIMTAR ABUBUWA DA SAURAN SU DA KUMA YANAYIN WAJE ZAMAN SU.
  4. YARO YA GA GIRMAMA MANZON ALLAH (S.A.W) DA GIRMAMA SUNNAR SHI DA MAGANGANUN SHI TA HANYAR KOYI DA SHI DA BIN ABINDA YAYI UMJRNI DA SHI DA KIYAYE SALATI A GARE SHI DUK SANDA AKA AMBACE SHI TUN DAGA IYAYEN SHI DA WADANDA KE KEWAYE DA SHI. HANYAR DA IYAYE KE BI A AIKACE WAJEN TARBIYYAR YARO NA DAGA CIKIN MANYAN ABIN DA KE MA YARO TASIRI DOMIN YAFI SAURIN DAUKA. YANZU A MISALI- ALOKACIN DA MAHAIFI YA ZO DA ABINDA YAKE SUNNA NE DA KUMA YIN NAFILOLI SAI YA CE MA ‘YA’YAN SHI HAKA MANZON ALLAH (S.A.W) YA KASANCE YANA AIKATAWA, DOLE SUMA ZASU DAUKA. ZAMA ABIN KOYI AWAJEN TARBIYYA NA DA TASIRI SOSAI WAJEN SAMUN INGANTACCIYAR RAYUWA DA AKIDA TSAFTATACCIYA, MANZON ALLAH (S.A.W) SHI NE ABIN KOYI MAFI GIRMA DA IYAYE YA KAMATA SU RIKA KOYI DA SHI TARE DA BIN SHIRYARWAR SHI DA KUMA AIKATA SUNNAR SHI TARE DA ‘YA’YANSU.
  5. HADDATAR DA YARO WASU INGANTATTUN HADISAI DA SUKE NUNI AKAN CIKAR KAMALA DA KYAWUN MUSULUNCI DA ABUBUWAN DA SUKA SHAFI MANZON ALLAH (S.A.W) DA FALALAR SAHABBAN SHI. HADISAI NADA TASIRIN GASKE WAJEN DASA IMANI DA GYARAN DABI’U DA GINA ZUCIYA. KUMA ANA IYA YI MUSU MUSABAKA, AMMA YA KASANCE WADANCAN GAJERUN HADISAN MA’ANARSU A BAYYANE TAKE BA SAI AN YI DOGON SHARHI BA KUMA YA ZAMANA SUN KUNSHI WASU DABI’U NAGARI MASU MUHIMMANCI AWANNAN MATAKIN SHEKARUN NA YARO. A KULA DA YIN AMFANI DA HANYOYI MASU JAN HANKALI DA KYAUTUTTUKA DA SAKAMAKO.

RUKUNI NA BIYAR:

IMANI DA RANAR LAHIRA

IMANI DA RANAR LAHIRA YA KUNSHI IMANI DA CEWA AKWAI MUTUWA DA TASHI BAYAN MUTUWA DA SAKAMAKO DA HISABI DA SIRADI DA MIZANI DA ALJANNAH DA WUTA. YARO ZAI FARA TUNANIN WASU MAS’ALOLI NA RANAR ALKIYAMA BAYAN YA WUCE SHEKARUN DA YAKE IYA TANTANCE ABUBUWA SOSAI. AMMA KAFIN HAKA, ZEYI KYAU YA KASANCE MAGANGANUN DA ZA A FADA MAI SU KASANCE A TAKAICE KUMA A DUNKULE, MU BAYYANA MA YARO CEWA AKWAI RAYUWAR LAHIRA DA KUMA CEWA ALLAH YA HALICCI ALJANNA GIDAN MUMINAI, DA WUTA GIDAN KAFIRAI.

DAGA CIKIN ABINDA YA KAMATA A TARBIYYARTAR DA YARO WAJEN DASA MAI IMANI DA RANAR LAHIRA SU NE:

  1. YARO YA SAN CEWA ALLAH ZAI TADA MUTANE RANAR LAHIRA DAGA MUTUWAR DA SUKA YI DAN A BASU SAKAMAKON AYYUKAN SU DA SUKA YI A DUNIYA, IN ALKHAIRI MUTUM YA AIKATA ZAI SAMU ALKHAIRI, IN KUMA SHARRI YA AIKATA YA SAMU SHARRI.
  2. YARO YA SAN CEWA ALLAH YA SAMAR DA ALJANNA AWANNAN RANAR, ALJANNA GIDAN KARAMCI DA JIN DADI DA TABBATUWA ACIKIN TA HAR ABADA, ALLAH YA HALICCE TA DAN YA SAKA MA MUMINAI DA ITA BISA AYYUKA NAGARI DA SUKA YI, YA KUMA SAMAR DA WUTA DA AKA TANADE TA DAN KAFIRAI MASU SABAWA ALLAH. ZA A NUNA MA YARO HAKAN NE TA HANYAR KWADAITAR DA SHI AKAN IRIN NI’IMOMIN DA KE ALJANNA DA ABUBUWAN DA AKA TANADAR MA MUMINAI ACIKIN TA.
  3. TATTAUNAWA DA YARO AKAN MUTUWA DA RANAR ALKIYAMA TA HANYA MAI TAUSHI DA TAKE NUNI AKAN RAHAMAR ALLAH DA GAFARAR SHI DA TAUSAYIN SHI GA BAYI SABODA KAR WASU TUNANUKA KARKATATTU SU ZO MA YARO SU DAME SHI. ANA IYA HADA HAKA, WATO BASHI LABARIN ABUBUWAN DA KE RAYE WADANDA KE WUCEWA MATAKI-MATAKI, MISALI WANE YA FARA RAYUWA TUN DAGA LOKACI KAZA GASHI YAU BA SHI YA MUTU DA IRE-IREN HAKA. SAI DAI SHI MUTUM ALLAH YA BANBANTA SHI TA  HANYAR DORA MAI NAUYE-NAUYE KUMA YA SANYA DUK HALITTU SU ZAMA MASU YI MASHI HIDIMA KUMA SHI DAN ADAM ALLAH YA MAI ALKAWARIN KYAKKYAWAN SAKAMAKO MATUKAR YA KYAUTATA, SAURAN HALITTU KUMA BASU DA WANI SAKAMAKO.
  4. AYI MUSU BAYANIN CEWA ALLAH BAYA TABBATAR DA AZZALUMI KUMA BAYA BARIN AZZALUMI BA TARE DA YAYI MISHI UKUBA BA, HAKA BAYA BARIN WANDA AKA ZALUNTA BA TARE DA YA SAKA MAI BA. KUMA BAYA BARIN MAI KYAUTATAWA BA TARE DA YA SAKA MAI DA LADA BA. MU YANZU A DUNIYA MUNA GANIN WANDA KE RAYUWA AKAN ZALUNCI KUMA YA MUTU YANA AZZALUMI, DUKDA WANNAN BA MAKAWA DOLE AKWAI RAYUWAR LAHIRA BAYAN WANNAN RAYUWAR DA MUKE YI YANZU A DUNIYA WANDA ZA A SAKA MA WANDA YA KYAUTATA A KUMA YI MA WANDA YA SABA UKUBA, KUMA A BAMA KO WANE MAI HAKKI HAKKIN SHI.

RUKUNI NA SHIDA:

IMANI DA KADDARA

IMANI DA KADDARA YA KUNSHI CIKAKKEN IMANI DA ILIMIN ALLAH DA ABINDA YA RUBUTA TUN A LAUHIL MAHFUZ DA KADDARAR SHI DA RUBUTUN SHI DA MASHI’AR SHI, YARO A LOKACIN DA YAKE SHEKARUN FARKO BAYA IYA FAHIMTAR MENENE HUKUNCIN DA ALLAH YA YANKE DA KUMA KADDARA, WASU NA GANIN BA ZAI YIYU YA GANE MA’ANAR SU BA SAI BAYAN YA KAI SHEKARU TARA A RAYUWAR SHI. AMMA ASALIN MA’ANAR TARBIYYA YA KAMATA A DASA MA YARO ITA CIKIN ABINDA YA SHAFI HUKUNCI DA KUMA KADDARAR ALLAH. DAGA CIKIN HAKA AKWAI:

  1. ABINDA YAKE ASALI A WANNAN BABIN SHI NE ABINDA YA ZO DAGA ABIL-ABBAS ABDILLAHI BIN ABBAS (R.A) YA CE: WATA RANA NA KASANCE A BAYAN MANZON ALLAH (S.A.W) SAI YA CE:(( YA KAI YARO ZAN SANAR DA KAI WASU KALMOMI, KA KIYAYE ALLAH ZAI KIYAYE KA, KA KIYAYE ALLAH ZAKA SAME SHI A GABAN KA, IDAN ZAKA YI ROKO TO, KA ROKI ALLAH KUMA IDAN ZAKA NEMA TAIMAKO TO, KA NEMA TAIMAKO WAJEN ALLAH, KA SANI CEWA LALLAI DA ACE AL’UMMAH ZASU TARU DON SU AMFANAR DA KAI WANI ABU BA ZASU AMFANE KA DA KOMAI BA FACE ABINDA ALLAH YA RUBUTA MAKA, HAKA KUMA DA ZASU TARU DON SU CUTAR DA KAI AKAN WANI ABU TO, BA ZASU CUTAR DA KAI DA KOMAI BA FACE ABINDA ALLAH YA RUBUTA AKAN KA, AN DAGE ALKALUMA KUMA TAKARDU SUN BUSHE)) [TIRMIZI: 2516]. WANNAN HADISIN ANA DAUKAR SHI A MATSAYIN MABUBBUGAR TARBIYYA WADDA TA KUNSHI NUSASSHE DA YARO ABU MAI KYAU DAGA ANNABI (S.A.W) ZUWA GA AL’UMMAR SHI WAJEN BADA MUHIMMANCI GA RAINON YARA AKAN AKIDA INGANTACCIYYA.
  2. NISANTAR YAWAITA MAGANA AKAN KADDARAR ALLAH TARE DA YARO A IRIN WADANNAN SHEKARUN, ABINDA YA KAMATA A ISAR MA DA YARO SHI NE YIN BAYANI AKAN FADIN ILIMIN ALLAH DA KADDARAR SHI DA MAMAYEWAR SHI GA KOMAI DA HALITTAR SHI DA MASHI’AR SHI, ABINDA YA SO SHI YAKE AUKUWA, WANDA BE SO BA BAYA AUKUWA, TARE DA TABBATAR MAI DA ‘YANCIN ‘YAN ADAM. DA CIKAKKEN NAUYIN DA KE KAN SHI NA DAGA AYYUKAN SHI ZABABBU, DA HAKKIN BADA LADA GA WANDA YAYI ABIN KWARAI KO UKUBA GA WANDA YA SABA MAI. ZA A MA YARO WANNAN BAYANIN NE A DUNKULE. AMMA IDAN WANNAN YA ZAUNA A KWAKWALWAR YARO YA ZAMA YANA MAI SETI TO YA KAMATA GA MAI TARBIYYA A WANNAN LOKACIN YA FADADA MAI BAYANI AKAI TA YADDA KWAKWALWAR SHI ZATA DAUKA.
  3. TARBIYYANTAR DA YARO AKAN ROKON ALLAH BA ROKON WANI BA, KUMA YA DOGARA DA ALLAH SHI KADAI, A SANAR DA SHI CEWA ITA ADDU’A ANA FUSKANTAR DA ITA NE GA ALLAH SHI KADAI, KUMA YIN TAWAKKALI DA DOGARO GA ALLAH SHI KADAI DA KUMA YIN HAKURI AKAN HUKUNCI DA KADDARAR DA ALLAH YA YANKE GA MUTUM.
  4. YARO YA SAN CEWA ALLAH BE NUFIN SHI DA KOMAI FACE ALKHAIRI, SANNAN SHI YANA TAFIYA NE ACIKIN RAYUWA BISA KADDARAR ALLAH, DAN HAKA ZUCIYAR SHI BA ZATA SHIGA KUNCI BA KUMA BA ZAI KARAYA BA IN ABUBUWA SUKA FARU DA SHI. HAKAN ZAI SA IN YA FADA CIKIN TSANANI YA SAN CEWA KADDARA CE DA HUKUNCIN ALLAH AKAN SHI, YA SAN CEWA {BA ABINDA ZAI SAME MU FACE ABINDA ALLAH YA RUBUTA MANA} [ TAUBA: 51]
  5. YASAN CEWA FARUWAR AL’AMURA A HANNUN ALLAH SUKE, KUMA SHI ALLAH YANA AIKATA ABINDA YASO NE YA KUMA ZABA, DOMIN SHI YANA DA IKON JUJJUYA ABUBUWA A CIKIN MULKIN SHI, WANNAN ZAI SA YA KARA DANFARUWA DA UBANGIJIN SHI DA KUMA KOMAWA GARE SHI KUMA ZAI SA YA MAIDA CIKAR BURIKAN SHI DA ADDU’O’IN SHI DA FATAN SHI GA ALLAH.
  6. IMANI DA WANNAN RUKUNIN YANA TABBATAR DA NATSUWAR ZUCIYA DA KUMA AUNA ABUBUWA ACIKIN ZUCIYAR YARO, ALOKACIN DA MUMINI YAKE JIN CEWA DUKKAN ABUBUWAN DA KE FARUWA DA SHI NA ALKHAIRI KO NA SHARRI SHINE ALKAHIRI AGARE SHI, WANNAN ZAI SA YA SAMU NATSUWAR ZUCIYA DA TABBATUWA ACIKIN ZUCIYAR SHI, KUMA HAKAN ZAI SA YA FUSKANCI MATSALOLI DA WAHALHALU DA DAMUWOWIN SHI TA HANYAR MARABA DA HUKUNCIN ALLAH DA KADDARAR SHI, DAGA NAN KUMA ZAI MIKA AL’AMURAN SHI GA ALLAH YAYI RAYUWA CIKIN NATSUWAR ZUCIYA DA TUNANI. DUK WANDA YAYI IMANI DA KADDARAN ALLAH BA ZAI KARAYA BA KUMA BA ZAI YI FUSHI LOKACIN DA MUSIBU SUKA FADO MAI SAI DAI MA YA MIKA WUYA YA NEMA LADA AWAJEN ALLAH YA KUMA TUNA FADIN ALLAH GA WADANDA SUKA YI HAKURI YAYIN DA MUSIBA TA AFKA MUSU. INDA YACE: { KUMA KAYI MA MASU HAKURI BUSHARA (55) WADANDA IN MUSIBA TA FADA MUSU ZASU CE LALLAI MU NA ALLAH NE KUMA LALLAI MU GARE SHI MUKE KOMAWA (56) WADANNAN SUNA DA YABO GA UBANGIJIN SU DA RAHMA KUMA WADANNAN SUNE SHIRYAYYU.} [BAKARA: 155-157 ]
  7. ANA IYA BASHI HIKAYOYI DA KISSOSHI NA ABUBUWAN DAMUWA DA SUKA FARU DA WASU NA KADDARAN ALLAH, SANNAN A BAYAN HAKA ALKAHIRAI SUKA SAME SU TA DALILIN KUNCIN DA SUKA SHIGA SUKA YI HAKURI DA KADDARAN ALLAH. AL’AMURAN SU SUKA CANZA ZUWA MAFI KYAWU DUKA ADALILIN HAKAN.
  8. A MAI BAYANIN IMANI DA KADDARA A TAKAICE AKAN CEWA ALLAH YA SAN KOMAI A DUNKULE DA RARRABE, YA RUBUTA DUKKAN ABUBUWAN DA ZASU FARU ACIKIN LAUHIL MAHFUZ WANDA YA RIGA YA SAN SU TUN KAFIN YA RUBUTA SU NA DAGA  ABUBUWAN DA ZASU FARU GA HALITTUN SHI TUN RANAR DA AKA HALICCE SU HAR ZUWA RANAR TASHIN ALKIYAMAH. KUMA DUKKAN HALITTU DA SAURAN ABUBUWA BA SA KASANCEWA FACE SAI DA NUFI NA ALLAH.
'Fel a tetejéhez' gomb