GABATARWA

DUKKAN GODIYA TA TABBATA GA ALLAH, TSIRA DA AMINCI SU TABBATA GA MAFIFICIN ANNABAWA DA MANZANNI, ANNABINMU MUHAMMAD ((S.A.W)) DA MUTANEN GIDANSA DA SAHABBAN SA BAKI DAYA,

BAYAN HAKA:

A SHEKARUN FARKO NA YARO YANA DA MUHIMMANCI SOSAI A GINA YADDA HANGEN YARO YAKE GAME DA SAMUWAR ABUBUWA, TA INDA AKE KIRGA FAHIMTAR DA AKA GINA HANKALIN YARO AKANTA A MATSAYIN TUSHEN FARKO NA GINA MUTUNTAKARSA A DUKKAN BANGARORIN RAYUWARSA, WACCA YA KAMATA ACE TA KASANCE TA DACE DA BUKATUWAR YARO TA RAYUWA DA ZAMANTAKEWA DA ADDINI, KUMA AIKI NE NA GINA YARO CIKAKKEN GINI DA ZAI TAIMAKA MAI WAJEN TABBATUWA DON YA TSALLAKE MATSALOLIN RAYUWA YA KUMA CI GABA DA TAFIYA A MATSAYIN SHI NA DAN ADAM MAI AUNA ABUBUWA DA KIRKIRAR ABABE DA AIKATA SU DA KYAU, DAGA ABIN DA YAKE JI YAKE KUMA GANI YARO ZAI TSARA ABUBUWAN DA SUKA KEBANCE SHI A WANNAN DUNIYAR DA DUKKAN ABINDA ZAI SAURA A RAYUWAR SHI BAYAN HAKA, BABU WANI ABU FACE CANZAWA DA KUMA CI GABA GA WANNAN HANGE MAI TUSHE GWARGWADON YANAYIN DA ZAI BI.

KUMA TUSHEN ILIMIN DA YARO YAKE DOGARO AKANSU A WANNAN MATAKIN SUNE IYAYENSA, DON HAKA, SHIRYUWAR YARO TANA DAGA INGANCIN TARBIYYAR IYAYE NE, ALHAKIN KOYAR DA YARAN YANA KAN SU. SHIYASA MANZON ALLAH ((S.A.W)) YA CE: ((DUKKAN KU MASU KIWO NE KUMA DUKKAN KU ABIN TAMBAYA NE AKAN KIWON KU)) [BUKHARY 2558, MUSLIM 1829]. WANNAN NAUYIN DOLE NE A KULA DA SHI KUMA A DAGE WAJEN TARBIYYA DA ILIMANTARWA.

TUNDA MUNA RAYUWA NE A ZAMANIN DA SHA`AWA DA KUMA SHUBUHA TAYI YAWA, YA ZAMA WAJIBI GA IYAYE SU DAGE SUYI TARBIYYAR `YA`YAN SU DA KUMA DAGEWA YA ZAMA MAI CIKE DA GASKIYA DA KWADAYI DA DAGEWA. WANI IRIN DA IYAYE SUKA DASA A ZUKATAN `YA`YAN SU YANA FITAR DA TSURO AIKI NE MAI CI GABA GA IYAYEN BAYAN MUTUWARSU, SAI DAN YA ZAMA SHI NE ABIN DA YA RAGE NA AIKIN KIRKI GA IYAYE WANDA ZAI CI GABA DA YADUWA BAYAN MUTUWA. KAMAR YADDA MANZON ALLAH ((S.A.W)) YA CE: (KO YARO NAGARI DA ZAI YI MAI ADDU`A). [MUSLIM 1631]

`YA`YA A TAKAICE ALLAH YAYI MA IYAYE WASICI AKAN SU INDA YACE:

{ALLAH YANA YI MUKU WASIYYA GAME DA `YA`YAYEN KU} [AL-NISA`I: 11].

MA`ANA:

`YA`YANKU YA KU TARON IYAYE AMANA NE AWAJENKU, ALLAH YA MUKU WASICI AKAN SU DA KU TSAYA KU KARE ABINDA ZAI AMFANE SU A ADDINI DA DUNIYA, KU KARANTAR DA SU KU LADABTAR DA SU KU KIYAYE SU DAGA BARNA KU YI MUSU UMURNI DA YIN BIYAYYA GA ALLAH DA LAZUMTAR TSORON ALLAH A KOYAUSHE. KAMAR YADDA ALLAH ((S.W.T)) YA CE: {YAKU WADANDA SUKA YI IMANI KU KARE  KAWUNAN KU DA NA IYALAN KU DAGA WUTA} [AL-TAHRIM:6]. AN YI MA IYAYE WASICI AKAN `YA`YAN SU, KODAI SU TSAYU AKAN WANNAN WASICIN KO KUMA SU BAR SU SU FADA WUTAMAI RADADIN AZABA DA UKUBA TA TABBATA A KAN SU, WANNAN NA NUNI AKAN CEWA ALLAH ((S.W.T)) YAFI RAHMA SAMA DA BAYINSA, KUMA FIYE DA IYAYE SABODA YAYI WASICI GA IYAYE AKAN `YA`YA DUKDA TAUSAYIN SU AKAN SU.

IDAN TARBIYYAR YARO TA KASANCE TA INGANTA TUN ACIKIN GIDA TO ZAI IYA MU`AMALA DA MUTANEN WAJE TA FUSKA MAI KYAU,SANNAN DUK LOKACIN DA AKA SAMI WATA TAWAYA A  BANGAREN TARBIYYAR YARO TA IMANI WACCE AKA GINA SHI AKANTA  ZA`A SAME SHI DA RASHIN DABI`U NAGARI. TARBIYYA BA ITA CE GYARAN KUSA-KURAI BA, A`A ITA CE KOYAR DA YARO HALAYYAR ADDINI DA HUKUNCE-HUKUNCEN SHARI`A DA YIN AMFANI DA HANYOYI DABAN-DABAN WAJEN ASSASSA MAI YADDA AKE SURANTA ABUBUWA DA TABBATAR DA SU ACIKIN KWAKWALWARSA. YANA DAGA CIKIN TARBIYYA MAI BADA TARBIYYA YA ZAMA MUDUBI YA KUMA RINKA YIN WA`AZI KO NASIHA TARE DA BADA KISSOSHI NA MUTANE NAGARI DA ABUBUWAN DA SUKA FARU A ZAMUNAN BAYA DOMIN A FITAR DA INGANTACCEN MUTUM A RAYUWA.

AN KASA LITTAFIN NAN ZUWA FASALI BIYU:

FASALI NA FARKO:

TARBIYYAR GINA IMANI: KUMA YA KUNSHI ABUBUWA DA YAWA AKAN TUSHE DA GINSHIKI WADANDA ZASU TAIMAKI IYAYE WAJEN TARBIYYAR `YA`YANSU DA YARDAR ALLAH,

AMMA BABI NA BIYU, YANA MAGANA NE AKAN (SAMFURA NA ZAHIRI NA AMSAR IRIN TAMBAYOYIN DA YARA KAN YI GAME DA  IMANI), WANDA A CIKI AKWAI TARIN TAMBAYOYIN DA SUKA FI YADUWA TSAKANIN MATASA NA KOWANE ZAMANI, MUSAMMAN WAƊANDA SUKA SHAFI RUKUNAN IMANI GUDA SHIDA, DA KUMA BAYANI GAME DA YADDA ZA A MAGANCE IRIN WAƊANNAN TAMBAYOYIN.

ALLAH YA DATAR DA MU IZUWA HANYAR SHIRIYA.

ABDULLAH BIN HAMD ARRAKF

'Fel a tetejéhez' gomb