MISALAI NA ILIMI DON AMSA TAMBAYOYIN YARA NA IMANI AMSOSHIN

AMSOSHIN DA KE CIKIN WANNAN BATUN ANA YIN SU NE DA FARKO GA IYAYE DA WAƊANDA SUKE HULƊA DA TAMBAYOYIN YARA DAGA MALAMAI, MASANA, MASU BA DA ILIMI DA MASU KAWO SAUYI, WAƊANDA MUKE ROƘONSU SU DAIDAITA ABIN DA AMSAR TA ƘUNSA GWARGWADON SHEKARUN YARO, MATAKINSA DA IKONSA. SABODA BA ZA MU IYA BA DA AMSA GUDA ƊAYA A MATAKAI DABAN-DABAN NA SHEKARUN YARO, TUNANI DA ƘWAREWA, SABODA HAKA; ABIN DA MUKE BUKATA SHI NE GASKIYAR AMSAR, BA KALLON KALMOMIN BA, KO BAMBANCIN KALMOMIN AMSOSHIN, DA TSAKANIN MAGANA KAI TSAYE DA WACCE BA KAI TSAYE BA DON MU FAHIMTA GA MAI KARATU, WANDA SHI YA KAMATA YA ƊAUKI GABARAR WAƊANNAN AMSOSHIN YA SAKE FASALIN SU TA YADDA YAKE GANIN YA FI DACEWA DA KYAUTATAWA ƊANSA.

DOMIN AMSA TAMBAYOYIN YARON DA SUKA SHAFI KOFOFIN IMANI; IYAYE SU KASANCE SUNA DA MAFI ƘARANCIN WAYEWA WADDA ZATA BASU DAMAR ISAR DA FAHIMTAR ADDINI NA FARKO WANDA KE BAYANIN ABUBUWAN DA BA A GANI A CIKIN TSARIN DA YA DACE DA TUNANINSU DA ƘWAREWAR SU, DA KUMA ƘALUBALEN DA KE GABAN MALAMAI GABA ƊAYA BAI TA’ALLAKA DA SAMUN BAYANAI BA KAWAI, YA TA’ALLAKA NE A SANYA SHI A CIKIN SAMFURI WANDA HANKALIN YARON YA YARDA DA SHI KUMA YA FAHIMTA, KUMA TA HANYAR NUNA DACE DA LOKACI, WURI DA YANAYIN DA YAKE RAYUWA.

BAYANIN NAN MAI ZUWA GABATARWA NE NA MISALAN WASU TAMBAYOYIN DA KE MAIMAITAWA A HARSUNAN YARA, KUMA WAƊANNAN BA DUKA TAMBAYOYI BANE, AMMA MAFI MAHIMMANCI KUMA MAFI YAWA NE DAGA CIKINSU, KUMA MUNA DA SHA’AWAR ZAƁAR MAFI KYAWUN AMSOSHI A RA’AYINMU, WANDA BA MU DA’AWAR AMSOSHI NE NA YAU DA KULLUN, AMMA DAI SAMFURAN DA IYAYE ZA SU IYA FARAWA DA SU NE, KUMA TABBAS SUNA KARBAR GYARE-GYARE, SHAREWA DA ƘARI.

JAN HANKALI:

DUK WANDA YAKE TUNANIN CEWA YANA FAMA DA NAKASA WAJEN TARBIYANTAR DA ‘YA’YANSA TO YA HAIFAR DA WADANNAN TAMBAYOYI NE MASU WUYAR SHA’ANI; BAI YI KUSKURE BA, SABODA WANNAN YANAYIN A CIKIN YARA ANA ƊAUKARSA WANI LAMARI NE NA LAFIYARSU WANDA KE BAYYANA CI GABAN ƊABI’A DA TSARI MAI MA’ANA A CIKIN TUNANIN YARO DA ƘWAREWAR TUNANINSA. YANA DAGA CIKIN GAZAWAR IYAYE WAJEN FAHIMTAR CI GABAN YARO DA BUƊE TUNANINSA DA KUMA KARƁAR ABUBUWAN DA KE TATTARE DA SARARIN SAMANIYA DA HALITTAR DA KE KEWAYE DA SHI, SABILI DA HAKA DOLE NE IYAYE DA WAƊANDA SUKE HULƊA DA YARON SU YI ƘOƘARI DON SAMAR DA GAMSASSUN AMSOSHI GA YARO, HAR ZUWA WANI LOKACI. RUDANI KO GURƁATATTUN HALAYEN DA KE HAIFAR DA ƘARA RIKICEWA DA DAMUWA A TUNANIN YARO, KUMA WANNAN RUDANI DA DAMUWA ZASU HAIFAR DA RIKICI CIKIN ƊABI’A DA RASHIN DAIDAITUWA A CIKIN TUNANI DA MA’AMALA.

BA A HAIFAR DA MANYAN MATSALOLI A LOKACI ƊAYA, KUMA WUTA NA TASHI DAGA ƘANANAN TARTSATSIN WUTA, DON HAKA; DA YAWA DAGA CIKIN HALAYE MARASA KYAU A CIKIN MUTANE SUNA KAMA DA ƘARAMIN IRI WANDA AKA SHAYAR DA SHI A HANKALI DA JINKIRI, KUMA JAHILCI KE SAMAR MAI DA RUWA HAR SAI YA GIRMA YA KUMA HAƁAKA, KUMA YA SAMU GINDIN ZAMA A CIKIN RUHI, SAI TUMBUKE SHI DA KAWAR DA SHI YA WAHALAR.

'Fel a tetejéhez' gomb