TAMBAYOYI DA SUKA SHAFI IMANI DA ALLAH

TAMBAYOYIN DA AKASARI SUKA FI YAWO A ZUCIYAR YARO TUN SUNA KANANA SU NE TAMBAYOYIN DA SUKA SHAFI ALLAH, ANAN ZAMU BIJIRAR DA TAMBAYOYIN DA YARA SUKA SABA YIWA IYAYENSU.

WANENE ALLAH?

DA FARKO DAI, BAI KAMATA MU JIRA YARON BA HAR SAI YA TAMBAYE MU GAME DA ALLAH, AMMA MU FARA MAGANA GAME DA ALLAH KOYAUSHE DA KOWANE LOKACI AMSAR DA TA DACE GA TAMBAYAR YARON GAME DA ALLAH DA HALAYENSA ZA SU TABBATAR DA KOYARWAR TAUHIDI DA IMANI GAME DA ALLAH – MADAUKAKI – A CIKIN TUNANIN YARON DA ZUCIYARSA SABODA HAKA, HANYA MAFI KYAWU ITA CE HANKALIN YARO YA SHAGALA GA BARIN TUNANIN ZATIN ALLAH ZUWA TUNANIN ALAMOMINSA DA KUMA ABUBUWAN AL’AJABIN HALITTARSA DA SUKE NUNA SHI, KAMAR SAMA, GAJIMARE, TAURARI, RANA, WATA, TEKU, BISHIYOYI , DA SAURANSU, DON HAKA MUNA GAYA MASA CEWA WANNAN SAMA ALLAH NE YA HALICCE TA, KUMA WANNAN DUNIYA ALLAH NE YA HALICCE TA, KUMA DUK WADANNAN BISHIYOYIN ALLAH NE YA HALICCE SU, HAKA NAN HAR SAI YA SABA, DA KUMA JAN HANKALINSA DA WADANNAN KALMOMIN, A LOKACIN DA YA TAMBAYE MU CEWA WANENE ALLAH? KAWAI MU BASHI AMSA MAI SAUKI CEWA SHI NE YA HALICCI KOMAI DAKE  KEWAYE DA MU, KUMA MU BA SHI MISALAI DA YAWA GAME DA HAKAN.

KUMA IDAN MUN NUNAWA YARON WAƊANNAN DUNIYOYIN NA SAMA DA DUNIYA, KUMA MUN BAYYANA MASA MURFIN WANNAN TSARIN MAI BAN MAMAKI DA TSARI MAI HIKIMA; MU GAYA MASA: SHIN GA WANNAN TSARIN? WANDA YA TSARA KUMA YA SHIRYA WADANNAN DOKOKIN ALLAH NE – MADAUKAKI -, SANNAN SUNA TASBIHI GA UBANGIJINSU TARE DA ILIMI DA HUJJA, KUMA MU GAYA MASA CEWA ALLAH SHI NE WANDA YA HALICCI KOMAI, KUMA BABU WANI ABU MAKAMANCINSA, KUMA SHI NE MAI RAHAMA, MAI YAWAN KYAUTA, KUMA YANA DA SUNAYE DA SIFFOFI WADANDA DUKKANSU KYAWAWA NE SABODA HAKA, YA CANCANCI A BAUTA MASA SHI KAƊAI, BA TARE DA ABOKIN TARAYYA BA, KUMA CEWA ALLAH MADAUKAKI YANA SON YARA KUMA YANA UMURTAR MANYA DA SU KULA DA SU KUMA SU AMFANAR DA SU DA KUMA KYAUTATA MUSU DA KUMA SAURAN DUKKAN MUTANE, KUMA YANA YI MANA HISABI KAN AYYUKANMU MASU KYAU DA MARASA KYAU KAMAR BADA LADA KO UKUBA, KUMA SHI NE WANDA KE BA DA LADA GA MAI KYAUTATAWA DON KYAUTATAWARSA DA MAI LAIFI KAN LAIFIN DA YA AIKATA, KUMA YANA DA AMFANI: A SANAR DA YARA KANANA BAYANI CIKAKKE; WANDA YA HAƊA DA MAFI KYAWUN AMSOSHI GAME DA ZATIN ALLAH DA SIFOFINSA, GAMA SHI ALLAH NE WANDA: BA A HAIFE SHI BA KUMA BAI HAIFA BA, KUMA BASHI DA SA`A KODAYA.

ZA MU IYA YI MASA TAMBAYA MU CE: WANENE YA SAYA MUKU WAƊANNAN KYAWAWAN TUFAFI? ZAI CE: BABA, KUMA WA ZAI KAI KA MAKARANTA? ZAI CE: BABA, KUMA IDAN KA YI RASHIN LAFIYA WA ZAI KAI KAWAJEN LIKITA? ZAI CE: BABA, KUMA WA ZAI DAUKE KA ZUWA YAWO IDAN AN YI HUTU? ZAI CE: BABA, TO BABANKA NE WANDA YAKE KULA DA DUKKAN LAMURANKA? HAKA NE, TO ALLAH SHI NE WANDA YAKE KULA DA MU DUKA, ALLAH SHI NE MAHALICCIN KOMAI, DUK ABIN DA KA GANI A KUSA DA KAI ALLAH NE YA YI SHI, RANA DA WATA, GIZAGIZAI, TEKUNA DA DUWATSU, HALITTAR MUTUM, DABBOBI DA TSUNTSAYE, HALITTAR MALA’IKU DA ALJANU, ALLAH SHI NE MAHALICCIN DUKKAN HALITTU, KUMA ALLAH MAI KARIMCI NE DA JINKAI.YANA KULA DA MU, YANA SONMU KUMA YANA KAWO MANA ALHERI A KOYAUSHE.

SHIN SURAR ALLAH IRI DAYA CE DA TA MUTANE?

A’A, BA KAMAR MU BA NE, DOMIN ALLAH BA ABINDA YA YI KAMA DA SHI, DOMIN SHI NE WANDA YA HALICCE NI, YA HALICCE KA, YA HALICCI DUKKAN MUTANE, YA HALICCI BISHIYOYI, KOGUNA, TEKUNA, DA KOMAI A WANNAN DUNIYAR, SHI NE TUSHEN KARFI, KUMA IDAN YANA SON WANI ABU SAI YA CEWA ABUN YA KASANCE TO SAI YA KASANCE. ALLAH YA BAMBANTA DA MUTUM. MUTUM BA ZAI IYA ƘIRƘIRAR MUTUM BA, AMMA ALLAH YANA IYA YIN HAKAN KUMA YANA IYA YIN DUK ABIN DA YAKE SO, KUMA TUNDA BABU WANDA ZAI IYA GANIN ALLAH A CIKIN RAYUWAR DUNIYA, BA WANDA ZAI IYA BAYYANA KAMANNINSA, BA ZA MU IYA DUBAN ALLAH A CIKIN DUKA ƊAUKAKARSA DA HASKENSA BA, DOMIN IYAWARMU TA NA DA IYAKA. SANNAN SAI MU NEME SHI DA YA JE YA KALLI HASKEN RANA BA TARE DA RUFE IDANUNSA BA, KUMA MU TAMBAYE SHI: SHIN ZA KA IYA CI GABA DA DUBAN RANA? ZAI AMSA DA FADIN A A, DON HAKA SAI MU CE: HAKA

ALLAH  HASKEN DA KE FITOWA DAGA WURIN ALLAH BA ZA MU IYA ƊAUKARSA BA, AMMA IDAN MUKA SHIGA ALJANNA, ZA MU GA ALLAH DA IZININSA.

YARON NA IYA BIJEREWA YA KUMA BAYYANA BAI GAMSU BA, YA CE: TA YAYA BA WANI ABU KAMARSA? ANAN, YA KAMATA A LALLASHE SHI CIKIN NUTSUWA, SAI MU CE: TUNANINMU, KOMAI NUNARSA DA FAHIMTARSA, YA KASANCE TUNANIN MUTANE NE MASU RAUNI, MUNA SANIN ABIN DA ALLAH YAKE SO SU SANI, DA RASHIN SANIN WASU ABUBUWA, BA SHI YIWUWA MU SAN KOMAI. SABODA MUN KASANCE MUTANE NE, KUMA ACE DA SHI: IDAN ALLAH YA KASANCE MUTUM KAMAR MUDA YA YI CUTA KAMAR MU, KUMA YA CI YA SHA KAMAR MU, YA MUTU KAMAR MUTANEN DA SUKA MUTU, AMMA ALLAH BAYA RASHIN LAFIYA BA YA CI, BA YA SHA KO MUTUWA, SHI YANA NAN A KOYAUSHE KUMA SHI NE MAHALICCIN SAMMAI DA ƘASSAI DA KOWANE ABU A CIKIN WANNAN DUNIYAR, SABODA HAKA; ALLAH BA ABINDA YA YI KAMA DASHI, KUMA ZAMU IYA TAMBAYAR YARON: SHIN MU MUTANE ZAMU IYA FAƊIN WANI ABU WANDA YAKE KUMA YA KASANCE? YARON ZAI AMSA: A’A, KUMA TA HAKA NE ZAMU KAMMALAWA YARON DA CEWA ALLAH BA MUTUM BANE KAMARMU, AMMA DAI SHI NE BABBAN MAHALICCI.

KUMA SAI MU CE MASA: JINMU TAKAITACCE NE, BAMA IYA JI SAI ABINDA AKE DAGA WATA TAZARA, IDAN DA ZAMU JI KOMAI, TO DA MUN GAJI, KUMA IDANUNMU SUN TAKAITA, DON HAKA KAWAI MUNA IYA GANI DAGA IYAKANTACCEN NISA, DON HAKA MU BA ZA MU IYA GANIN ABIN DA YAKE BAYAN BANGO BA, KUMA KAMAR YADDA JINMU YAKE IYAKANTACE KUMA IDANUNMU SUKE IYAKANTATTU, TUN DA ALLAH MADAUKAKI YA HALICCI MUTANE KUMA HAR ZUWA YAU ABINDA MUTUM YA SANI SHI NE MAFI KARANCI AKAN ABINDA BAI SANI BA, DON HAKA RUHIN DA KE JIKIN MUTUM – ALAL MISALI – DUK DA CEWA YANA KUSA DA  MU SAI DAI BA ZA MU IYA SURANTA SHI BA, KO KUMA MU SAN HAKIKANINSA BA, DON HAKA IDAN WANNAN YA KASANCE A CIKIN LAMURAN MU NE KUMA TARE DA MU, TO YAYA ABIN YAKE A WAJEN MU?! KUMA BISA GA HAKA, TUNANIN MUTUM MUDDIN YANA DA IYAKA, TO BA ZAI IYA GANE AINIHIN ALLAH BA. SAKAMAKON HAKA, MAGANA GAME DA SURAR ALLAH BA TA HANYAR TUNANI BA CE, KO HANKALI, KO KUMA RUDU, SAI DAI KAWAI DA SHARIA KADAI, KUMA KUR’ANI YA WARWARE WANNAN BATUN DA CEWA: (BABU WANI ABU KAMAR SHI – KUMA SHI NE MAI JI DA GANI NE) ALLAH BA KAMAR MU BANE KO WANI ABU KAMAR MU, KUMA WANNAN YANA NUNA GIRMAN ALLAH WANDA DOLE NE MU ƘAUNACE SHI, MU SA TSORONSA A ZUCIYA, KUMA WANNAN GIRMAN NA BAYYANA CEWA GANIN SA A ALJANNA SHI NE MAFI GIRMAN NI’IMAR ALJAANNA BAKI DAYA.

WANENE YA HALICCI ALLAH?

IDAN DA AKWAI WANDA YA HALICCI ALLAH, DA SAI MU YI TAMBAYA WANE NE YA HALICCI MAHALICCIN, HAKA NE? DON HAKA, DOLE NE MU SANI CEWA DAYA DAGA CIKIN SIFFOFIN MAHALICCI SHI NE CEWA SHI BA ABIN HALITTA BA NE, KUMA SHI NE YA HALICCI DUKKAN HALITTU, KUMA IDAN YA KASANCE ABIN HALITTA NE, DA BA ZA MU BAUTA MASA BA, KUMA DAB A MU BI UMARNINSA BA, TAMBAYA GAME DA WANENE YA HALICCI ALLAH BA DAIDAI BANE, KUMA TAMBAYOYIN DA BASU DACE BA BASU DA MA’ANA, MISALI: IDAN WANI YA TAMBAYE KA GAME DA TSAWON ƁANGARE NA HUƊU NA TRIANGLE? BABU AMSA. SABODA TRIANGLE YANA DA BANGARORI UKU NE KAWAI, KUMA AKWAI KUSKURE A CIKIN TAMBAYA GAME DA WANENE YA HALICCI ALLAH. KALMAR HALITTA DA KALMAR ALLAH BA SA HADUWA; SABODA BA A HALICCI ALLAH BA, KUMA TSARIN HALITTA KAWAI YA HAU KAN HALITTA, KUMA BABU WANDA ZAI IYA HALITTAR ALLAH, IN BA HAKA BA DA AN HALICCE SHI – SHI MA – DON HAKA ALLAH YANA NAN BA TARE DA FARKO BA KUMA BA SHI DA KARSHE.

KUMA IDAN MUKA ƊAUKA CEWA AKWAI MAHALICCIN ALLAH MAƊAUKAKI! TAMBAYA GUDA ZATA KASANCE: WANENE YA HALICCI MAHALICCIN MAHALICCI?! SANNAN WANENE YA HALICCI MAHALICCIN, MAHALICCIN MAHALICCIN??! HAKAN ZAI CI GABA BA IYAKA, KUMA WANNAN BA ZAI YIWU BA, KUMA A KADDARA MU DAUKI MISALIN SOJA DA HARSASHI, SOJAN YANA SON YIN HARBI, AMMA KAFIN YA YI HARBIN DOLE NE SOJAN YA NEMI IZINI DAGA SOJAN DA KE SAMA DA SHI, KUMA WANNAN SOJAN DOLE NE YA NEMI IZINI DAGA SOJAN DA KE SAMA DA SHI KUMA HAKA YAKE HAR ABADA, TAMBAYAR: SHIN SOJAN ZAI YI HARBI? AMSA: A’A; DOMIN HAKAN BA ZAI KAI GA SOJAN DA ZAI BA SHI IZININ HARBI BA, AMMA IDAN SARKAR TA KARE GA MUTUMIN DA BA WANDA ZAI BA SHI IZININ HARBI, TO ZAI HARBA HARSASHI, KUMA BA TARE DA WANNAN MUTUMIN BA, KO MUTANE DA YAWA SUN TARU BA ZASU HARBA HARSASHIN BA, SUNA KAMA DA SIFIRAI IDAN KUN JERA SU KUSA DA JUNA KOMAI YAWANSU KUMA KO SUN KAI MALALA-GASHIN TINKIYA, BA A BAKIN KMAI SUKE BA, SAI DAI IDAN AN SANYA WATA LAMBA 1 A GABANSU KO FIYE.

DAGA INA ALLAH YA ZO? KUMA SHEKARUNSA SHI NAWA?

MUDDIN KA SAN CEWA BA A HALICCI ALLAH BA; HAKANAN KUMA BAI HAIFA BA KUMA BA A HAIFE SHI BA, KUMA BA SHI DA FARKO KO KARSHE, KUMA A KAN HAKA BA SHI DA SHEKARU KAMAR YADDA YAKE GA MU ‘YAN ADAM, DOMIN ALLAH SHI NE BABBAN MAHALICCI, MAI GIRMA, MAI ARZIKI, MAI ƘARFI, MABUWAYI , MAI RAHAMA, WANDA YAKE DA KYAWAWAN SUNAYE DA SIFOFI MAFIYA GIRMA, YANADA SIFFOFI NA KAMALA KUMA BASHI DA SIFFOFIN KASAWA, DOMIN ALLAH, TSARKI YA TABBATA A GARESHI, SHINE WANDA YA HALICCI DUNIYA KAMAR YADDA YA HALICCI DUKKAN ABUBUWA DA DUKKAN HALITTU.

WANENE YA KASANCE KAFIN ALLAH?

WANNAN ITA CE TAMBAYA DAYA GAME DA WANDA YA HALICCI ALLAH, DON HAKA TAMBAYA CE TA KUSKURE, ALLAH MADAUKAKI SHI NE NA FARKO, DON HAKA BABU WANI ABU A GABANSA KUMA SHI NE NA KARSHE, DON HAKA BABU WANI ABU A BAYANSA. ALLAH MADAUKAKIN SARKI YANA CEWA: (SHINE NA FARKO SHI NE NA KARSHE, BAYYANE NA BOYYYAYE – KUMA SHI MASANI NE AKAN KOMAI) (AL-HADID: 3) HAKIKA LOKACI DA GURI BA KOMAI BANE FACE HALITTA DAGA CIKIN SAURAN HALITTUN ALLAH. HALITTU BA ZASU IYA IYAKANCE KO KEWAYE MAHALICCINSU BA, TSARKI YA TABBATA A GARESHI. ALLAH YANA DA DUKKAN SIFOFIN KAMALA DA KYAU, KUMA YA KAMATA ANAN YA FADAKA DA NASIHAR ANNABCI ABU HURAIRA – ALLAH YA YARDA DA SHI YA RAWAITO DAGA ANNABI (S.A.W) YA CE: «SHAIDAN YANA ZOWA DAYANKU YA CE MAI: WANENE YA HALICCI KAZA, WANENE YA HALICCI KAZA, DAGA KARSHE SAI A CE: WANENE YA HALICCI UBANGIJINKA? IDAN YA KAI A HAKA, TO YA BARI YA NEMI TSARIN ALLAH DAGA SHEDAN SAI YA DAINA» (BUKHARI (3276)), NEMAN TSARIN ALLAH DA KUMA KAUTAR DA TUNANIN YARON ZUWA GA WANI BATUN DABAN, DON KADA YA CI GABA DA YIN IRIN WAƊANNAN TAMBAYOYIN. DAGA CIKIN MAHIMMAN AMSOSHI A NAN, KAWAR DA SHI DAGA WANNAN BA SABODA BABU AMSA BA NE, SAI DAI SABODA RUFE HANYOIN WASIWASIN SHEDAN.

SHIN ALLAH NAMIJI NE KO MACE?

YAKAMATA MU HIMMATU WAJAN KIYAYE TUNANIN YARO DAGA YAWAN TUNANI GAME DAZATIN  ALLAH, DA KUMA JAN HANKALINSA ZUWA GA TUNANIN ABUBUWAN DA ZASU AMFANE SHI KUMA SU FA`IDANTAR DA SHI, KUMA ANAN YANA DA KYAU MUYI MA YARO BAYANIN CEWA BATUN NAMIJI DA MATA YANA DAGA CIKIN ABUBUWANDA AKE BUKATA DOMIN BAMBANCEWA TSAKANIN AJI DA JINSI NA HALITTU MASU RAI, KUMA WANNAN NA CIKIN ABIN DA ALLAH YA YI BAIWA DA SHI GA HALITTUNSA, ALLAH MADAUKAKI YA CE: (KUMA SHI NE YA HALICCI AURE BIYU MATA DA MAZA) (AN-NAJM: 45), KUMA ALLAH, TSARKI YA TABBATA A GARE SHI, YA FI KARFIN WANNAN RARRABUWA, AKWAI WASU HALITTUN MA, KAMAR MALA’IKU – HARMA SAMA, GIZAGIZAI, ISKA DA RUWA BA ZA A IYA KWATANTA SU DA MAZA KO MATA BA. DA GASKE NE CEWA AKWAI WASU HALITTU TAUYAYYYU AMMA KUMA BASU CIKIN WANNAN KASON NA MAZA KO MATA, WANDA WANNAN RARRABUWA BATA AIKI AKANSU; ALLAH SHI YAFI DACEWA KAR YA SHIGA WANNAN KASON,: (BABU WANI ABU KAMARSA – KUMA SHI NE MAI JI NE KUMA MAI GANI NE) (ASH-SHURA: 11).

ME YASA MUKA YARDA DA WANZUWAR ALLAH? MENENE HUJJAR SAMUWAR ALLAH?

IMANI DA ALLAH MADAUKAKIN SARKI WATA DABI’A CE TA DAN ADAM DA BABU WANDA ZAI IYA MUSANTAWA, KUMA SHAIDUN SAMUWAR ALLAH SUNA DA YAWA, KUMA HAR YANZU MUTANE SUNA SAMUN HUJJOJI BAYAN HUJJOJI, KOWANE GWARGWADON KWAREWAR SA DA KUMA FANNIN SA. ALLAH (S.W.T) A CE: (FIDIRAR ALLAH CE WACCE YA HALICCI MUTANE A KANTA) (RUM: 30), KOWANE ƊAYANMU YANA DA ƘARFI A CIKIN ZUCIYARSA, WANDA KE MASA MAGANA GAME DA GIRMA, IKO DA KULAWAR ALLAH, DA DALILAN KIMIYYA MASU YAWA SUNA TABBATAR DA KASANCEWAR MADAIDAICIN TSARI A WANNAN DUNIYAR, KUMA WANNAN MADAIDAICIN TSARIN DOLE NE YA KASANCE AN YI SHI NE SABODA WADANNAN HALITTUN KUMA DOLE NE AKWAI WANDA YA HALICCE SU, KO WANENE SHI KO SUN SAMAR  DA KANSU NE BA TARE DA MAHALICCI BA, TO BABU WANDA YA SAN YADDA WAƊANNAN ABUBUWA SUKA FARU, AKWAI WANNAN YIWUWAR, AKWAI KUMA YIWUWAR CEWA WAƊANNAN ABUBUWA SUN SAMAR KANSU KUMA SUNA AIWATAR DA AL’AMURANSU, KUMA AKWAI YUWUWA TA UKU WACCE ITA CE: CEWA SUNA DA MAHALICCIN DA YA HALICCE SU KUMA YA SAMAR DA SU MUN GA CEWA NA FARKO DA NA BIYU BA SU YIWUWA, DON HAKA IDAN NA FARKO DA NA BIYU BA SU YIWU BA; NA UKU DOLE NE YA ZAMA BAYYANANNE KUMA DAIDAI, WANDA SHINE CEWA TANA DA MAHALICCI WANDA YA HALICCE TA – WANDA SHINE ALLAH – KUMA WANNAN SHINE ABIN DA AKA AMBATA A CIKIN ALKUR’ANI MAI GIRMA. (KO KUMA AN HALICCE SU DAGA BABU NE, KO KUMA SUN KASANCE MASU HALITTAWA (35), KO KUMA SUN HALICCI SAMMAI DA KASSAI – AMMA BA SU DA TABBAS) (AD-DUR: 35-36).

DAGA CIKIN HUJJOJI TABBATATTU NA SAMUWAR ALLAH AKWAI AMSAWAR DA ALLAH YAKE YI WA KIRAYE-KIRAYEN BAYI, HAKA NAN: WANNAN CIKAKKIYAR HALITTAR TA SAMMAI DA KASSAI ALLAH MADAUKAKI YA CE: (LALLAI, A CIKIN HALITTAR SAMMAI DA KASA, DA SABANIN DARE DA YINI, AYOYI NE GA MA`ABOTA HANKALI) (ALI-IMRAN: 190), DA KYAUTATA HALITTAR MUTUM ALLAH (S.W.T) Y ACE: (KUMA A CIKINKU BA KU GANI) (AZ- ZARIYAT: 21), HAKA NAN KUMA A CIKIN HALITTAR TAURARI, DUWATSU, DABBOBI DA SAURANSU, DUKKANSU SUNA NUNI DA KIRKIRA GAME DA  MAI YINTA – TSARKI YA TABBATA A GARE SHI. KUMA KASANCEWAR DUKKAN WADANNAN HALITTU DOLE NE SU KASANCE SUNA DA MANUFAR SAMUWARSU, KUMA DUKANSU SUNA BAUTA WA ALLAH SHI KAƊAI BA SHI DA ABOKIN TARAYYA. MUNA IYA GAYA MAI LABARIN ABU HANIFA – ALLAH YA YI MASA RAHAMA – A LOKACIN DA WASU MUTANE SUKA NEMAI YA TABBATAR MUSU DA TAUHIDIN HALITTA. YA CE MUSU: KU GAYA MINI – KAFIN MU YI MAGANA GAME DA WANNAN BATUN – GAME DA JIRGIN RUWA A CIKIN DUHU WANDA ZAI JE A CIKA SHI DA ABINCI, KAYA, DA WASU ABUBUWA SHI KAƊAI, KUMA YA DAWO DA KANSA, SA’ANNAN YA TSAYA DA KANSA, YA SAUKE KUMA YA DAWO, DUK WANNAN BA TARE DA WANI YANA SARRAFA SHI BA, DON HAKA SUKA CE: WANNAN BA ZAI YIWU BA, BA ZAI TABA YIWUWA BA, DON HAKA YA CE MUSU: IDAN AKA DAUKI WANNAN A JIRGIN RUWA; TA YAYA ZAI ZAMA A WANNAN DUNIYAR DUKA, TA SAMA DA ƘASA?!, BA SHI YIWUWA WANNAN CIKAKKIYAR HALITTA TA WANZU BA TARE DA MAHALICCI MAI IKO BA, KUMA MASANI..

HAKANAN ZA’A IYA CE MASA: LOKACIN DA KA JI ZAFI A CIKINKA, SHIN BA KA LURA CEWA KANA JIN YUNWA BA, SAI KA NEMI ABINCI KAI TSAYE DON MAGANCE YUNWARKA? KUMA IDAN KA JI ƘISHIRWA, BA KA NEMAN ABIN DA ZAI SHAYAR DA ƘISHIRWAR KA? KUMA IDAN KAJI KAMSHI MAI DADI, BA KANA JIN FARIN CIKI BA? KUMA AKASIN HAKA IDAN KA JI WARI? YAYIN DA KA KALLI FULAWA, FURANNI, SARARIN SAMA DA YANAYIN DA KE KEWAYE DA MU, SHIN BAKA JIN FARIN CIKI DA ANNASHUWA? HAKANAN KAI TSAYE MUKE JIN CEWA MUNA BUƘATAR ALLAH MAI GIRMA WANDA KOYAUSHE MUKE KOMAWA GARE SHI LOKACIN DA MUKE BUƘATAR SA. DON SAMUN NUTSUWA DA KWANCIYAR HANKALI, LOKACIN DA MUKE JIN HAUSHI DA BAƘIN CIKI; MUNA KOMAWA KAI TSAYE ZUWA GA ALLAH DA YIN ADDU’A GARE SHI, KUMA IDAN MUNA JIN FARIN CIKI, MUNA GODE MASA SABODA SHI.

SHIN ALLAH YANA JI, YANA GANI KUMA YANA MAGANA KAMAR MU?

ALLAH YANA MAGANA, YANA JI, YANA GANI. ALLAH MABUWAYI YA CE: (ALLAH YA JI MAGANAR WADDA TAKE JAYAYYA DA KAI GAME DA MIJINTA) (ALMUJADALA: 1). KUMA YA CE: (YA CE KADA KU JI TSORO INA TARE DA KU INA JI KUMA INA GANI) (DAHA: 46), SAI YA CE: HAKIKA SHI GAME DA ABINDA KUKE AIKATAWA MAI GANI NE) (HUD: 112), AMMA BA KAMAR MAGANARMU BA, KO JIN MU, KO GANINMU; DOMIN ALLAH YA BANBANTA DA HALITTARSA, DON HAKA YANA JIN MURYOYI KOMAI BOYUWARSU, KUMA YANA GANIN ABUBUWA KOMAI NISAN SU, DOMIN ALLAH YANA JIN KOMAI KUMA YANA GANIN KOMAI, AMMA JIN SA DA GANIN SA BA KAMAR JI DA GANI BANE NA HALITTU MASU KASAWA DA RAUNI. (BABU WANI ABU MAKAMANCINSA HAKA KUMA SHI MAI GANI NE KUMA MAI JI NE) (AL-SHURA: 11), KUMA YANA DA KYAU: A DANGANTA WANNAN DA HALAYYAR KAI TSAYE, TA YADDA ZA A CE IDAN ALLAH MAI JI NE KUMA MAI GANI; SHIN YA DACE MUYI MAGANA GAME DA ABIN DA BAYA SO KUMA YA DINGA GANINMU A YANAYIN DA BAI YARDA DASHI BA?!

ALLAH YANA JIN YUNWA DA KISHIRWA?

ALLAH – MADAUKAKI – YANA DA SIFOFIN KAMALA KUMA BAI DACE DA SIFFAR KASAWA BA, YUNWA DA KISHIRWA WASU ABUBUWA NE GUDA BIYU NA RAUNI, KUMA BAYA HALATTA A DANGANTA RAUNI GA ALLAH. DON HAKA ALLAH BAYA BUƘATAR ABINCI DA ABIN SHA; DOMIN ALLAH, MAHALICCIN KOMAI, BAYA BUKATAR KOMAI, KUMA BAYA BUKATAR KOMAI. LOKACIN DA YA KASANCE ABIN BAUTA NA GASKIYA, ALLAH SHI NE TSAYAYYEN DA BAYA CIN ABINCI KUMA BAYA BUKATAR ABINCI KO ABIN SHA, DON HAKA YA WADATU DAGA DUK WANNAN, KAMAR YADDA SHI NE WANDA HALITTU KE FATA. DON CIYAR DA ITA DA SHAYAR DA ITA DA BIYAN BUƘATUNTA.

ANA IYA CE MASA – HAR ILA YAU – CEWA BABU SARARI DON KWATANTAWA TSAKANIN ABIN HALITTA DA MAHALICCI, BA LALLAI BA NE CEWA DUK ABIN DA MUKA ƘIRƘIRA YA ZAMA YANA DA IRIN SIFFOFI IRI ƊAYA DA NAMU, KO? ALLAH BA YA JIN YUNWA KO ƘISHIRWA, BARI IN YI MAKA TAMBAYA: WANENE YA KIRKIRI KEKE? ZAI AMSA DA CEWA SHI NE MAI KIRA, MADALLA, ZO, DAN BARI MUYI TUNANIN TARE DA KEKEN YANA MAGANA YANA TAMBAYAR MAI KIRKIRAR SA: ME KAKE CI? ME KAKE SHA? ME ZAKA CE MAI: WANNAN BA BATUNKA BA NE, KUMA MENENE ZA KA AMFANA DA SHI IDAN KA SANI, KUMA ME ZAKA ƘARU DA SHI AIKINKA NA YAU DA KULLUN, WANDA SHI NE TAFIYA DA SAURI BA TARE DA ƁARNA BA, DA KYAU, KUMA WANNAN SHI NE YADDA MUKE – YA KAI DANA ALLAH YA HALICCE MU NE DON WANI AIKI NA MUSAMMAN: (KUMA BAN HALICCI MUTANE DA ALJANU BA SAI DON SU BAUTA MIN) (AZ-ZHARIYAT: 56) WADANNAN TAMBAYOYIN BA ZA SU TAIMAKA MANA BA KUMA BA ZA SU TAIMAKA MANA BA WAJEN AIWATAR DA AIKIN DA MUKE SO AN HALICCE SU NE DON AKASIN HAKA, ZUKATANMU ZA SU SHAGALTU DA ABUBUWAN DA KE KAWO MANA CIKAS, AMMA YAUSHE KEKE YA TABA TAMBAYARMU MU? LOKACIN DA WANI ABU YA LALACE, SAI YA JUYA GA MAKERINSA DON GYARA SHI, SABODA HAKA, MU KOMA GA ALLAH TARE DA ROKO YAYIN DA MUKA TSINCI KANMU MUN YANKE DAGA BAUTA, KO KUMA LOKACIN DA WATA CUTA TA SAME MU.

YAYA KARFIN ALLAH YAKE?

IDAN MUNA MAGANA GAME DA IYAKANTACCEN IKO KO IYAWA; WANNAN YANA NUFIN MUNA MAGANA NE GAME DA SIFA TA TAWAYA, SABODA ƘARSHEN ƘARFI YANA NUFIN FARKON RAUNI, KUMA RAUNI BA NA ALLAH BA NE, SABODA HAKA; DOMIN IKON ALLAH TABBATACCE NE KUMA BA SHI DA IYAKA, KUMA BABU ABIN DA YA GAGARE SHI, ALLAH, MADAUKAKI YA CE: (LALLAI ALLAH MAI IKO NE A KAN KOMAI) (BAQARAH: 106), KUMA IDAN YANA SON WANI ABU SAI YA CE MASA: KA KASANCE; SANNAN ALLAH MAI IKO AKAN KOMAI. DOMIN SHI NE MAHALICCIN DUKKAN ABUBUWA, DON HAKA BABU ABIN DA YA GAGARE SHI A CIKIN ƘASA KO A SAMA, IYAKANTACCEN ƘARFI SHI NE KARFIN ABIN HALITTA, AMMA GAME DA IKON MAHALICCI: BA SHI DA IYAKA KUMA BABU TAWAYA A CIKI, SABODA HAKA; ALLAH NE KAƊAI YA CANCANCI A BAUTA MASA, ROKO, DA ADDU`A. DOMIN SHI KAƊAI NE MAI IYA BIYAN BUƘATUN HALITTA, YA CIYAR DA SU, YA BIYA MUSU BUKATUNSU, YA KUMA TAFIYAR DA LAMURANSU.

INA ALLAH YAKE? YAYA YANAYINSA YAKE?

BAYAN YARO YA FAHIMTA DA WURI CEWA ALLAH SHINE WANDA YA HALICCE SHI KUMA CEWA ALLAH YANA MATUKAR KAUNAR YARA, KUMA YA BASHI NI’IMOMI MASU YAWA, TO ZAMU IYA BAYYANA MASA CEWA ALLAH YANA SAMA. ALLAH YA CE: (SHIN KUN YI IMANI DA WADANDA KE SAMA) (AL-MALIK: 16), TO, SHI NE MAƊAUKAKI. A CIKIN SAMA, AMMA ILIMINSA YANA KO’INA, ALLAH YA CE: (KUMA YANA TARE DA KU, DUK INDA KUKA KASANCE) (AL-HADID : 4), KUMA BAI KAMATA MU CE: ALLAH YANA KO’INA BA. SABODA WANNAN YANA NUFIN CEWA AKWAI SHI A CIKIN KOMAI, KUMA WANNAN BA GASKIYA BANE. MUN DAUKI  ABIN DA YA TABBATA A CIKIN SUNNAH. HAKIKA ANNABI- AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI – YA TAMBAYI WATA KUYANGA: “INA ALLAH YAKE?” TA CE: A CIKIN SAMA, YA CE: “WANE NE NI?” TA CE: “KAI MANZON ALLAH NE.” YA CE: “KA YANTA TA, DOMIN ITA MUMINA CE” (MUSLIM (537)), KUMA DUK DA CEWA YANA SAMA; SAI DAI KAWAI YANA IYA GANI DA JINMU A KO’INA, DA KUMA TABBATACCEN TABBACIN CEWA ALLAH YANA SANE DA SHI KOYAUSHE. SANNAN A SANYA WANNAN GINSHIKIN A CIKIN RUHIN YARON, AMMA GAME DA YANAYINSA: ALLAH MAƊAUKAKI BA YA KWATANTUWA DA KOMAI DAGA ABIN DA YA HALITTA, DOMIN ALLAH YA FI KOMAI GIRMA, YA FI DUKKAN HALITTU GIRMA, KUMA IDAN WATA HALITTA NA DA GIRMA TO MAHALICCINTA YA FI GIRMA. SHINE WANDA YA TUMBUKE TSAUNIKA, YA MOTSA TEKUNA, KUMA YAYI UMARNI GA RUWA YA NUTSE A CIKIN KASA, BA ABINDA KE FARUWA A DUNIYA NA KOMAI SAI DA UMURNINSA –ALLAH  MADAUKAKI NE – DA NUFINSA, MAHALICCI BAYA BUKATAR HALITTA, DOMIN SAMMAI HALITTU NE DAGA CIKIN HALITTUN ALLAH, KUMA SAMUWAR SA BAI DOGARA DA ITA BA, KUMA BASHI BUKATAR TA; DOMIN ALLAH MAWADACI NE A KOMAI.

TA YAYA ALLAH YAKE GANIN MU ALHALI KUWA MU BAMA GANIN SHI?

IDANUN DA ALLAH YA BAMU A WANNAN DUNIYAR YANA DA RAUNI KUMA BAYA IYA GANIN MAFI YAWAN ABUBUWA, SABODA WANNAN DALILI: ZA KA GA MUTUM YANA AMFANI DA MADUBIN HANGEN NESA DA NA’URAR KARA GIRMA, DON HAKA IDAN MUTUM BA ZAI IYA GANIN ABUBUWAN DA AKA KIRKIRA BA; YA MA FI MUHIMMANCI CEWA SHI BA ZAI IYA GANIN ALLAH MADAUKAKI BA. IKON MUTUM A WANNAN DUNIYA BA YA TAIMAKA MASA WAJEN GANIN ALLAH. BA ZA MU IYA GANIN ALLAH BA, AMMA MUN YI IMANI DA SHI, KUMA MUN YI IMANI CEWA SHI MAI JINKAI NE KUMA YANA KAUNAR MU , KUMA YANA DA KARFI KUMA YANA IYA KOMAI KUMA YA SAN KOMAI, SABODA HAKA YA SAN MUNA MAGANA NE GAME DA SHI.YANZU, ALLAH YA FI MU GIRMA, SABODA HAKA; YANA GANIN MU DUKA A LOKACI GUDA, KAMAR WANDA YA HAU KOLOLUWAR SAMA, KUMA YANA GANIN DUK MUTANEN DA KE KAN TITI ALHALI KUWA BA SA GANIN SA, HAKA ALLAH MADAUKAKIN SARKI YAKE GANIN MU KUMA MU BAMA GANIN SHI, AKWAI ABUBUWA DA YAWA DA BAMU IYA GANI, AMMA SUNA NAN, KUMA MU DINGA GAYAWA YARON: IDANUNMU BASA IYA GANIN KOMAI, BAMA GANIN SAUTI DUK DA CEWA MUNA JIN SA, KUMA BAMU GANIN ISKA DUK DA CEWA MUNA JIN TA, DON HAKA IDANMU BA ZA SU IYA GANIN ALLAH MADAUKAKIN SARKI A WANNAN DUNIYAR BA, AMMA A CIKIN ALJANNA – IN ALLAH YA YARDA – ZA MU SAMI KYAWAWAN IDANUN DA ZA SU IYA GANIN ALLAH – TSARKI YA TABBATA A GARE SHI. SABODA HAKA; ALLAH (GANI BAYA RISKARSA, SHI YAKE RISKAR GANI, SHI MAI KYAUTATAWA NE MASANI) (AL-AN’AM: 103).

TA YAYA ALLAH YAKE GANIN DUKKAN MUTANE ALHALI SUNA DA YAWA?

DOMIN MU AMSA WANNAN TAMBAYAR A AIKACE, SAI MU ƊAUKI YARO MU TSAYA TARE DA SHI A BAKIN TITI, MU CE MASA: BARI MU KALLI MUTANE, KA GAYA MANA YAWAN MUTANEN DA KA GANI, KUMA ZA MU ƘIDAYA MUTANEN TARE DA KAI, SA’ANNAN MU HAU TARE DA YARO ZUWA WANI HAWA, KUMA MU SANYA SHI KALLON MUTANE KUMA YA ƘIDAYA WAƊANDA YA GANI, MU SANYA SHI ƘIDAYA DUK WANDA YA GANI, SANNAN MU KAWO MASA GILASHIN HANGEN NESA DON SANYA SHI GANIN MUTANE DA KYAU KUMA YA KIRGA SU SOSAI, KUMA TA WANNAN MISALIN: MUNA BAYYANA MASA CEWA BA ZA MU IYA AUNA ABUBUWA DA MIZANIN GWARGWADON DAN ADAM BA, KUMA MU BAYYANA MASA CEWA IKON ALLAH YA FI GIRMA DA DAUKAKA FIYE DA NA DUKKAN HALITTU, KUMA MUNA TABBATARWA A CIKIN TUNANINSA KOYAUSHE: (HAKIKA ALLAH MAI IKO NE AKAN KOMAI) (AL-BAQARAH: 106)

ZAMU IYA YI MASA TAMBAYA TAKAMAIMAI MU CE: SHIN KUNA TSAMMANIN TURURUWA TANA GANINMU A CIKIN DUKKAN BAYANANMU, KO KUWA TANA GANIN GIZO NE KAWAI KO INUWA? ZAI AMSA CEWA TURURUWA TANA IYA GANIN KARSHEN KARAMIN YATSANMU, KUMA TANA IYA ƊAUKAR YATSAN A MATSAYIN BABBAN DUTSE GARE TA, DA KYAU; SHIN KUNA GANIN CEWA TURURUWA NA IYA TAMBAYAR KU KUMA TA CE: YAYA KUKE GANIN MU GABA ƊAYA? AMSARKA ZATA KASANCE CEWA WANNAN YANAYIN HALITTA NE; YA DACE DA DAMARKU DA ALLAH YA HALICCE KU DA ITA, SABODA TURURUWA TANA DA IYAKANTACCEN IKO, KUMA TANA IYA ZAMA A CIKIN FIYE DA WURI ƊAYA A CIKIN ƊAKINTA, KUMA YANA DA SAUƘI A GARE KU KU GA WAƊANNAN WURAREN A LOKACI GUDA , AMMA TURURUWA DA KE DA IYAKANTACCIYAR DAMA BA ZA SU IYA GANI KAMAR YADDA KUKE GANI BA, KUMA TUN DA MUN KASANCE MUN YARDA CEWA ALLAH – MAI GIRMA DA DAUKAKA – BA ABINDA KE KAMA DA SHI, KUMA SHI MAI IKO NE A KAN KOMAI, DON HAKA BA HAKA BA NE YA DACE MU ROKI ALLAH TARE DA IYAKANTATTUN IYAWARMU DON WANI ABU WANDA GARESHI ABU NE NA DABI’A, DOMIN IKON ALLAH YA FI GIRMA DA ƘARFI FIYE DA IKON DUKKAN HALITTA. SABODA (ALLAH MAI IKO NE A KAN KOMAI) (BAQARAH: 106)

SHIN ALLAH MAƊAUKAKI YANA GANIN MUTANE A CIKIN DUHU?

ZAMU IYA SANYA YARON KALLON WANI ABU DAGA ƊAYAN FINA-FINAN DA KE NUNA SOJOJIN ƘASA WAƊANDA SUKE GANI DA GILASHIN IDANU YAU DA DADDARE, SAI MU MUNAWA YARON HOTUNAN BIDIYO NA WASU DABBOBI DA TSUNTSAYE WAƊANDA SUKE GANI A CIKIN DUHU, DA KUMA WASU FINA-FINAN DA YAKE KALLO DA WASANNIN DA YAKE YI, AKWAI WANI HASKE – KAMAR SU LASERS, SUNA BAYYANA MANA BOYAYYUN ABUBUWA, KUMA SUNA BA MU DAMAR GANIN ABUBUWA A CIKIN DUHU, SANNAN SAI MU CE MASA: SHIN KA GA YADDA MUTUM MAI RAUNI DA HALITTA MAI SAUKI KE IYA GANI A CIKIN DUHU A WANI LOKACIN? YAYA BATUN UBANGIJINMU WANDA YA HALICCI MUTUM DA DUKKAN WADANNAN HALITTU, KUMA DA ALLAH YA BAMU IKON KIRKIRAR WADANNAN ABUBUWA; SHIN SHI BA ZAI IYA GANI A DUHU BA, ALHALI KUMA SHI NE WANDA YA FI RINJAYE? SHI NE MAFI GIRMA KUMA MAFI IKO, KUMA IKON ALLAH BA ABINDA ZAI IYA RUFE SHI.

TA YAYA ALLAH MADAUKAKIN SARKI YAKE GANINMU YAYIN DA MUKE CIKIN GIDANMU TARE DA ƘOFOFI DA TAGOGI A RUFE?

MUNA  IYA NUNAWA YARON HOTON X-RAY NA LIKITANCI, SAI MU CE MASA: MUTUMIN DA ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA HALITTA YANA IYA GANIN KASHI YAYIN DA YAKE RUFE SOSAI TA HANYAR DAUKAR HOTO, TO YA UBANGIJINMU DA YA HALICCI MUTUM FA? TABBAS ALLAH MADAUKAKIN SARKI YANA GANIN MU YAYIN DA MUKE CIKIN GIDAJEN MU KUMA DUK KOFOFINMU SUNA RUFE, DOMIN KUWA ALLAH BA ABINDA KE KAMA DA SHI. SHI BA KAMAR MUTUM BANE WANDA GINE-GINE KE HANA SHI GANI, DON HAKA MAHALICCI BA ZAI IYA ZAMA KAMAR HALITTA BA. SABODA ALLAH MADAUKAKI NE A KAN KOMAI, KUMA YA DACE: MU KULLA ALAKAR  WANNAN AMSAR DA HALAYYAR YARO, DON MU KARFAFA BANGAREN LURA DA DANDANO NA ADDINI GA YARA.

TA YAYA ZAI SAN DUKAN AYYUKANMU? TA YAYA ZAI IYA SA`IDO AKAN MUTANE BAKI DAYA?

YA KAMATA YARO KOYAUSHE YA KOYI CEWA ALLAH YANA DA DUKKAN SIFOFI KYAWAWA DA KAMALA, KUMA YA SANI CEWA IKON ALLAH MADAUKAKI BA SHI DA IYAKA, DOMIN SHI MAI IKO NE.; ALLAH MADAUKAKI Y ACE: (HAKIKA ALLAH MAI IKO NE AKAN KOMAI) BABU WANI ABU DA YA GAGARE SHI A DUNIYA KO A SAMA, KUMA BA ZA MU IYA AUNA ƘARFINSA DA IKON HALITTU BA, KOMAI GIRMAN ƘARFIN HALITTA; ALLAH YA FI TA GIRMA KUMA YA FI TA KARFI, DOMIN KUSANTO DA ABUN: ZA MU IYA BA SHI MISALI TARE DA RIKODIN DIN KYAMARA, TUN DA TANA IYA YIN RIKODIN DA LURA DA KOWANE ƘARAMI DA BABBA DA YA FITO A YANKIN TABARAU ƊIN TA, DOMIN ALLAH SHI NE MAFI GIRMAN IKO KUMA MAFI KYAN MISALI NASHI NE, DON HAKA YANA IYA KALLON DUKKAN MUTANE A LOKACI GUDA. DOMIN KARFINSA BA SHI DA IYAKA, KUMA ALLAH MADAUKAKI YA SANI KUMA ILIMINSA YA GAME, YA YALWACI KOMAI.

ZA MU IYA BA SHI MISALI, SAI MU CE: A CE AKWAI WANI BABBAN KAMFANI DA YAKE SON SA IDO KAN MA’AIKATANSA, DON HAKA YA SANYA KYAMARORIN SA IDO BA TARE DA SUN SANI BA, SAI TA FARA DAUKAR SU TANA NUNA DUK ABIN DA KE FARUWA A CIKIN DUKKAN SASSAN KAMFANIN A LOKACI GUDA, DON HAKA IDAN BAWAN DA YA KASANCE MAI RAUNI YA IYA YIN HAKAN, TO ALLAH DA YA YI HALITTA BA ZAI IYA YIN HAKAN BA?

ME YASA MUTUM YAKE MUTUWA AMMA ALLAH BAYA MUTUWA?

MUTUWA TANA DAGA CIKIN KADDARAR ALLAH DA YA KADDARA AKAN HALITTUNSA ALLAH MADAUKAKI YA CE: (KOWANE RAI YA DANDANI MUTUWA – SANNAN KUMA ZA KU KOMA GARE MU) (AL-ANKABUT: 57) .MUTUWAR MUTUM ITA CE FARKON LAHIRA. KUMA ITA CE RAYUWA MAFI MUHIMMANCI.

MUTUWA ALAMA CE TA NUNA RAUNI A CIKIN BUKATUN RAYUWAR DA AKA HALICCE TA, KUMA RAUNI BA NA ALLAH BA NE, DOMIN KUWA BA A HALICCI ALLAH BA KUMA BA ZAI MUTU BA, KUMA MUTUM HALITTA NE KUMA YANA MUTUWA. RAYUWAR ALLAH TA’ALA BA KAMAR RAYUWARMU BA CE , DON HAKA RAYUWARMU TANA KAREWA TA HANYAR MUTUWA, KUMA KOWACE HALITTA TANA MUTUWA, BA ABINDA ZAI YI SAURA SAI ALLAH – MADAUKAKI -, CIKAKKIYAR RAYUWAR ALLAH NA BUKATAR DUKKAN SIFOFIN KAMALA, MAFI MUHIMMANCI DAGA CIKINSU ITA CE  SIFAR RAYAYYE WANDA BAYA MUTUWA.

SHIN ALLAH YANA KAUNA TA KAMAR YADDA NAKE KAUNARSA?

ALLAH MADAUKAKI MAI GAFARA NE, MAI JIN KAI, YANA SON MASU KYAUTATAWA, DAIDAIDATTU MASU GASKIYA, ALLAH MADAUKAKI YA CE: (YANA SON SU KUMA SUMA SUNA SON SHI) (MA’IDAH: 54), KUMA DAGA CIKIN ALAMAR SON ALLAH GA BAYINSA: YANA GIRMAMA SU, YANA KULA DA SU, YANA KULA DA LAMURANSU, YANA BASU LADA, KUMA YANA GAFARTA MUSU, KUMA KOWANE DAYA DAGA CIKIN MU YANA JIN TAUSAYIN DA ALLAH YAKE MASA DA KARIMCIN SA A GARE SHI, KUMA ALLAH YANA SON BAWAN SA WANDA YAKE BINSA YAKE KUMA KUSAR SHI, KUMA YANA NUNA ALAMUN KAUNARSA GA ALLAH, TUN DAGA TSARE SALLA, GIRMAMA IYAYE, BA DA SADAKA DA KYAUTATAWA MUTANE, GASKIYA DA KARATUN ALKUR’ANI, KIYAYE ZIKIRI, DA SAURAN AYYUKAN ALHERI, DON HAKA DUK WANDA YA AIKATA WADANNAN ABUBUWA ALLAH MADAUKAKI ZAI ƘAUNACE SHI.

'Fel a tetejéhez' gomb